Sashe 127
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kada ya gasgata ni Asiya! Nasan mahaifuyata zata shaide ni, duk fitina ta bana harkar maye bare kuma a yanzu da na girma. Ba zan shiga safarar abin da nasan illah ce ga al'umma ba. Ina miki ranstuwa da girman Allah ban san mugun abu aka bani ba. Waya kawai aka mini akwai sakon kaya da zan karba a Dutsen tanshi, idan na kai Kano za'a karba a biya ni. Kinsan kuwa ina harkar sakonni(Delivery). Ban tab'a zaton za'a mini kutse a cikin sana'a ta ba. Ni yanzu babban tashin hankalina ke ce. Ban san hukuncin da za'a yanke mini ba little. Kinsan k'asar nan waka sani ne waya sanka." Idona taf da hawaye na ce "Nasan baka aika ta wannan BAK'AR TA'ADAR ba. Da ikon Allah ina tare da kai, komin tsanani". Ya murmusa ya ce "Alhamdulillah! Na samu amincin firgicin da nake ciki. Dan Allah Asiya kada ki canja, kada ki juya mini baya a cikin wannan halin canka cakare da nake ciki." Idonsa ya kad'a sosai ya kasa cigaba da magana alamun ya shiga rudani. Hanif ya ce "Baban 2 kada yi kuka zamu zauna mu taya ka zama. Ammo ta tafi ta barmu tare da kai". Hamim ya ce "No zamu je mu koyo yadda zamu kwace shi daga hannun yan sandan kawai". Na yi k'asa da kaina kawai ina hawaye domin tausayin da suka ba ni ba kad'an ba ne. Ban iya ce musu komai ba. Shine ya yi jarumtar sake rungume su tunda a akan cinyoyinsa suke. Murya na rawa ya ce "Baban 2 baya karya domin wanda ya yi karya ya zagi Allah, Wanda ya zagi Allah kuwa dan wuta ne. Dan haka am innocent, ban yi laifi ba. Sharri aka yi mini. Kowa ya yi sallah ya yi wa Baban 2 addu'ar ya zama free". Suka had'a baki wurin ce wa zamu yi sosai ". A sanyaye muka rabu domin gobe za'a dawo da shi BAUCHI dan shiga kotu. A hanya Nasiba ta sake rasa kuzarin ta, dama kuwa bata iya sake wa a gabana na dade da fahimtar a takure take da ni. Abin da Bulkachuwa ya yi mata kuwa ya sake sanyaya mata jiki. Ina hankalce da ita, ina ganin yadda take son yi mini magana amma ta kasa. Cikin kundubala ta ce "Yabi!. Na amsa da "Na'am" murya babu amo. Ta kalli twins da suke barci a jikina. Ta ce "Idan na ce miki bana son Yaya Bulkachuwa na yi karya domin na girma da son sa, ke ma kin sani. Idan na ce miki a yanzu dole aka mini a kan aurensa zaki yarda?" Ban ce komai ba. Illah ido da na zuba mata. Ta numfasa ta zarce da ce wa "Ni da kaina bani da yadda zan yi ne. Domin kuwa mutane da yawa suna haduwa da kalubalen a hadasu da iyaye karkatattu. Sai dai duk da hakan ba zamu ki sonsu ko janye wa daga gare su ba. Na sani tun farko soyayyar sa gare ni ba mai yawa ba ce, bare yanzu da yake auren ki. Dan Allah ki yi hakuri kada ki datse mu'amala da ni Yabi. Al'amarin zumuncin yau ya shiga rudani mai yawa, amma idan aka yi hak'uri aka danne, aka yi sassauci sai a samu masalaha a duniya, a kuma samu rabauta a duniya. Zan yi iyakar kokarina na fita a harkar mijinki, na yarda Yaya Bulkachuwa ba mijina ba ne, ba kuma zai zama ba. Kada ki ce maganganun da ya yi cin fuska ya yi mini, zahirin gaskiya ya amayar". Na rik'e hannunta murya na rawa na ce "Ban kullece ki ba. Amma idan na ce ban ji ciwon abin da ya faru ba na yi karya. Har abada ba zan iya auren mijin ki ba Nasiba. Amma na hak'ura na barwa Allah ya yi mini zabi akan lamarinku. Tunda ai ba haramun ba ne. Shi yasa na hak'ura na barwa Allah komai". Dukkanmu kowa zuciya ta narke, muka dinga kuka. Ubaid da yake gaban motar ya yi tsaki ya ce "Sai ku yi ai. Amma ai mu kam mun kudire matukar ya aure ta sai ya sako mana ke ko da kuwa a gaban alkali ne". Na daskare da maganar sa. Na tuna na ba shi watanni shida. Gabadaya ma shekarunsa ashirin da uku ne. Amma ya yi magana kamar wani babban wanmu. Sai kuma hawayena ya sake zuba a dalilin yadda maganar auren Nasiba da Bulkachuwa ta zama silar samar da soyayya a tsakanin ahalin Baban Marina. Yan ubancin da manyanmu suke gwada mana ya yi matukar zangwanye wa. Na yarda mafi yawan kalubale ya kan zo da wata nasarar komin kankatarta sai dai idan ba a kula ba, ko an bari hankali ya kwace an yi fishin da ya shallake hankali.