← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 146

Sashe 84

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kad'a kansa ya ce "Babu laifi". Ni ban kawo komai ba. Na tashi na yi kicin da nufin dora girki. Sai na tarar da ya girka ya juye a flask. Ga shi ya mayar da ruwan wanka kan gawayin. Na bu'de na ga ya yi zafi ainun. Na dauko babban flask din da nake zuba ruwan zafi na cika shi. Na ajiye sannan na juye ragowar na shiga wankan. Sai da na shirya na ha'da Mana abincin na kai ina cewa "Yau dai ka zama Yabi, na dawo na tarar ka yi komai sannu da kokari". Ya sake yi mini wani irin kallon da ban gane ma'anarsa ba. Duk da dai yanzu ya canja amma ba musguna mini yake ba, kawai walwala da sukuninsa ne suka ragu, sannan yana yawan yi mini abubuwan da suke kona mini rai ta hanyar shata layi da abin hannuna. Na kalle shi na ce "Sauko mu ci to". Ya girgiza kai ya ce"ci, ni ba yanzu zan ci ba". Na marairaice na ce"To zo ka dinga bani a baki na gaji sosai Wallahi". Ya sake kafe ni da kallon da yafi wadanda ya yi mini. Bai kuma ce komai ba. Na rasa gane manufar hakan sai kawai na fashe masa da kuka mai tsananin gaske. Ya taso ya zauna kusa da ni ya ce "Me na yi miki zaki yi mini irin wannan kukan?" Da kuka sosai na ce "To akan me zaka dinga yi mini kallon tuhuma? Akan me ba zaka zo mu ci abinci tare ba? Na riga da na gane ka tunda ka fahimci na fara sonka shikenan ka nade kafar wando fara yi mini wula'kanci kala kala". Ya matso jikina sosai ya kwantar da ni a kirjinsa ya ce "Da gaske kina sona Asiya?" Na ture shi na zum'bura baki na juyar da fuska gefe. Na kasa bu'de baki na ce uffan. Ya saki gauron numfashi ya ce "Shikenan na daina yi miki wula'kanci, duk da nasan ba na yi din". Da kansa ya zuba mana abincin. Lokaci zuwa lokaci kuma zai debo ya bani a baki. Ko ruwa da ya bula ledar bai sha ba, bakina ya nufa da shi. Na zuke tas na bar masa leda a hannu. Sai wani ya bu'de. Da yake ina siyar da pure water, saboda masu zuwa lalle kawia na tsiri siyar wa kuma sai nake yin ciniki sosai. Na yi gyatsa "Na yi hamdala. Gaba'daya sai jikina ya mutu murus gajiya ta taso mini, ba abin da nake so irin na kwanta na yi barci. Ga shi maghariba ta kawo kai. Na kalli agogo na ga za'a kai minitina arba'in da biyar kafin a kira sallah. Na mik'e na kwashe kwanukan, na hau zaga tsakar gida dan abincin da na ci ya dai-daita. Na koma falon na kwanta a kujera na yi daidai iskar fanka na kad'a ni. Ya taso ya fara bin gabbobina yana dannawa sannu a hankali nake jin da'di a jikina. Ban ankara ba sai kawai ya sure ni yana cewa "mu je daki na wartsake miki gajiyar gaba'daya. Na fara shure shure shi kuma ya ri'ke ni gam. Fadi nake yi "No bazan yarda ka dora mini wata gajiyar ba gaskiya". A kunne ya ce "Amma kinsan na ce idan kina yin gardama komin kankantar ta cikin ba shiga zai yi ba". Nan da nan kuwa na yi muk'us domin har zuciyata so nake na ganni da ciki, so nake na ganni da baby a hannuna kamar yadda nake ganin su Ubaida. Har aka fara kiran sallar Bai samu nutsuwa ba. Kan dole ya tsallake ya bar ni. A gurguje ya yi wanka ya nufi masallaci. Ni kaina a dole na sake wanka na sauke farali. Yau da wuri muka kwanta domin ana idar da sallar isha da ya shigo ya rufe gidan, ni dama a kwance ya tarar da ni. Sai da ya karasa abin da bai ida ba sannan muka yi wanka, muka kwanta wajen tara da rabi. Washagari lafiya muka rabu, da zai fita na ce "Idan fita ta kama ni zan fita. Bai ce komai ba, ni kuma ban yi zaton bai amince ba. Da yake na dora cewar na fara Home service akan status dina. Sai kuwa na dinga samun k'ira akan ana bu'kata ta a wuri kaza. Na za'bi gida biyu, na bawa guda biyu hakuri akan wasu sun rigasu. Na kammala gyaran gidan tsab. Na fice. Wannan ranar har dare sannan na koma gida. A k'ofar gidan na tarar da shi, cikin wani irin yanayi. Yana ganina ya zabura ya mik'e. Ni kuma ganin a waje muke yasa na zarta shi na shige. Sai kawai na tarar da k'ofar tamu da sabon kwad'o. Na jinkirta amma bai shigo ba. Na gaji da tsayuwar jiransa. Na fara hassala ya gan ni amma ya kasa shigowa, yasan kuma ya canja kwad'o. Na gaji na fita na tarar da shi yana zaune tamkar dutse ko motsi ba ya yi. Na ce "K'ofar a rufe take fa". Ko kala bai ce ba. Na sake fusata. Na ce "Ka zo ka bu'de mini". Nan ma tamkar da Dutse nake magana. Allah yasa ma babu kowa a wajen. Zuciyata ta hauro matu'ka da gaske. Duk fa'din tashin da nake yi dan asirinsa ya rufu shi bai ga hakan ba. Murya na rawa na ce "Ni kake yiwa wula'kanci haka?" A fusace ya ce "Wace ce ke? Gida ne bana bu'katar ki a cikinsa ba, ba sai ki koma inda kika fito ba, kin ga kin yi maganin wula'kancina, nima na huta da rainin da kike yi mini". Jikina ya yi matu'kar sanyi, hawaye ya b'alle mini. Murya na rawa na ce yanzu a daren kake so na tafi gida?" Shima murya na rawa ya ce "Ai ni a daren kika dawo mini gida. Dan haka ki koma inda kika fito ko ki je inda zaki, ai dai babu sisin ki wajen kama gidan har yanzu, bare ki yi mini sabon isgilanci". Na fara kuka na ce "Na rantse da Allah Tijjani kai bahago ne na k'arshe. Duk tunanina mu ha'du mu rufawa kanmu asiri wani bai ji ko ba'a gane halin da muke ciki ba, amma gaba'daya ka murde ka canja, ka ki da'din azanci. Dan Allah ka fahimce ni, nifa ba jin da'din yadda kake yi nake ji ba". A tunzure ya ce "Yo dama ni ina da abin da zan jiyar da ke da'di ne?" Na yi sakare ina kallonsa gaba'daya ya juye ya koma wani azababben mutum. A hankali na ce "To zo ka bu'de mini, tunda dare ya yi." Ya girgiza kai ya ce "bana son ganin ki a cikinsa." Na juya na ce "Shike nan na gode". Na fara tafiya ni kad'ai ga shi wajen ba kowa, tsoro ya kama ni, da na ji kamar ana bina. Sai da muka iso wajen hasken solar na juya sai na ga shi ne yake bin bayana. Na tsaya na ce "To mene ne kuma, ba dai ka kore ni ba?" Da sanyin murya ya ce "Bakin titi zan raka ki, kada karnu ka su biki". A tunzure na ce "Allah yasa ma kuraye su kama ni, su cinye ni! Bai ce komai ba, har muka isa inda zan bi na yi gida. Na kalle shi na ce "Yanzu me kake so na fa'dawa Baban Marina?" Kai tsaye ya ce "ki fa'da masa gaskiyar abin da ya faru kawai". Na marairaice na ce "Tunda har ka rako ni nan, nasan ka huce, mu koma gida ka fa'da mini abin da na yi, ba sai ka ce na baka hakuri ba, zan nemi afuwarka". Ya girgiza kai ya ce "A a bana bu'katar ki a gidan ne, ki je gida, ko ki je ki kwana a wajen neman ku'din ki". Ganin zai sake tunzura da yawa yasa na tafi din. Amma tafiya kawai nake yi, bana ko sanin inda zan jefa k'afata. Tashin hankalina ace na je gidan Marina da sunan bacin rai. Na sani masu murnar ganina sai sun fi masu yin jajjabi yawa. Kuka nake yi sosai. Me zan cewa Baba da Gwaggo ni Yabi? Ko Ubaida k'aramarmu ba'a taba tura ta gida da sunan ta yi laifi ba sai ni? Ni kuwa dama akuyata ta yi shura. Ina ganin hanyar da zan bi na isa gidan, amma sai na bi wanda zata kai ni gidan Yaya Ummi. K'arfe tara da rabi na shiga d'akinta tamkar jifa. Cikin sa'a mijinta ya je Jos d'aurin auren yar kaninsa sai gobe litinin zai dawo. Ganina a wannan daren ga kuka ina yi, duk sai ta diriri ce ta dinga fa'din mene ne, daga ina kike?" Ina kuka, na fa'da mata Tijjani ne ya ce "Bazan shigar masa gida ba." Ta dauki salati ta ce "To ke da ina kika je?" Na fa'da mata gaskiya. Ta yi shiru ta ce "Tsakani da Àllah laifinki ne Yabi. Tunda bai amsa miki ba, ai kinsan ba wai yana so ba ne. Sannan me yasa kika yi dare har wajen tara?" Na yi shiru sai kuka kawai nake yi. Domin tskani da Allah ban san ina son Tijjani sosai ba sai yanzu da ya yi min irin wannan hukuncin. Ji nake kamar na yi ta zunduma ihu har kowa ya fahimci rad'ad'in da nake ji. Baya ga haka kuma fishin da na ga ni shinfide a kan fuskarsa ya sake dagula mini lissafi. Cikin kuka na ce "Ni bana son na je gida Yaya Ummi. Baba fishi zai yi da ni, haka ma Gwaggo. Ga magauta su tasa mu gaba da dariya da zunde". Ta nisa ta dauki k'aramar wayarta ta ce "ku'din ciki babu yawa, amma bari na gwada na ga ni. Bugun farko ya dauka tamkar me jira a k'ira shi. Ta gaishe shi da walwala. Sai kuma ta ce "Yaya Bulkachuwa sai ga Yabi ta zo mini a wannan daren, kuma abin mamaki ta ce wai kai ne da kanka ka koreta, ai da sai ka yi hakuri da safe ka tura ta gidan." Dake a sifika ta saka sai na ji ya ce "Na kasa yin wannan tsinkayen Ummilolo. Amma yanzu taimake ni ta kwana a gidan ki, gobe sai ta wuce gida". Da sauri ta
Chapter 84 · 0% Book details