Sashe 20
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata. Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan". Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?" Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi? To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba." Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan. Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi". Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa". Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku. Ba komai Ubangiji ya sanya alheri". Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina. Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai". Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye. Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga bayi ya fito. Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba. Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur. Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai tsabar yadda na washe shi. Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda maganar bata shige shi ba. A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba. Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi ta yi mini a gida. Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige daki. Idan ta gama abinci zata mini zubin auki. Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta, ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta. Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima. Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje. Ba musu Iki ta fita. Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa a gida?" Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?" Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu". Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana, gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne". Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin tausayi sosai tsabar ba'kin ciki." Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba. Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu." Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a tafiyar". Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an fa'da masa inda kike ba." *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.