Sashe 37
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tun suna yara k'ananu, amma shi da kansa ya datse soyayyar kuma yanzu Allah ya turo mata wani sai ya ce bai cancanci a ba shi aurenta ba. Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?" Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa? Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa? Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka yi daidai da zaginsa kake yi." Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma? Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri. Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun mutane ba'a karba ba. Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure, bare ya ce zan wani damu." Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?" A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke kitsa ta. A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi mata ba? Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi mini alfarma da kawaici." Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka." Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa. Rannan na ji wani malami yana fa'din ainihin manufar ma'anar kuyanga ta haifi uwargijiyarta. Sak fatawar da ya bayar tamkar ke ya siffanta haka na dinga ji". Na zuba ido. Ina jiran ta rushe da kukan da zata tara masa jama'a tamkar yadda take yi mana. Amma sai ta share ta yi mirsisi ta fanshe da cewa "Shi ubanta ai ya yarda na isa da shi, shi yasa ya katse al'amarin babu tashin hankali. Allah ya shirye ka mai sunan Shehu.". Ya shareta ya kalle ni ya ce "Yanzu kina son wannan ba'kin yaron ko kuwa dole aka yi miki?" A hankali na ce "ko bana sonsa tunda Baban Marina ya amince ai maganar ta kare". Ya girgiza kai ya ce "Baban Marina mutum ne Wlh amma ban son ha'kurinsa, any way Allah ya sanya albarka all the best Asiya Toro". Daga haka ya mike ya fice yana fa'din da kin ce ba kya so. Wallahi da tsaya miki zan yi, komin sharrin mai sharri ba za'a baki wanda ba kya so ba, domin kema y'a ce ba baiwa ba. Kina da hakkin ki so a kuma so ki". Wannan abin da ya yi mini sai ya rage tsanar sa a raina. Dada ta dinga fa'din "Sha sha kamar ba saboda shi aka yi komai ba." Na rasa gane manufar wannan maganar ta Dada. Tsawon sati da kulla alakarmu da Nura wanda ya yi zuwa uku kenan. Mamakin kaina nake ta yadda ya shiga raina sosai. Ko dan sau'kin kansa da yadda ya iya kwalliya da shirya zan ce ne? Ga shi ma'abocin kyauta duk zuwa sai yasan me ya ru'ko mini wala na ci, ko na amfani, gwargwadon k'arfinsa. Mahaifiyarsa da ake kira Yaya itama ba karamin son al'amarin take yi ba. Domin da kanta ta zo da kuma ledarta mai shak'e da kayan kwalliya. Kusan yini ta yi lamarin da ya takura ni, kunyarta sosai na ji. Wanda ko kusan ban ta'ba jin irin hakan akan mahaifiyar Yaya J ba. Karba ta samu daga ahalin gidanmu, dan kuwa ko Mama bata yi abin kaico ba, har ta tafi. Dada ce dai bata wani karbe ta da fuska mai yakanah ba, hatta shi da kansa da ya je gaisheta bai ji da'din karbar da ta yi masa ba. Hankalina ya fara tashi domin kuwa ba hannu Rabbana ya je mata ba, sai da ya siyo mata lafiyyayun lemo da kankana da ayaba tika tika. Na dinga fargaba da tunanin wata'kila wannan d'in ma, ta yi mini sanadinsa tunda su Baban Tsakiya kullum cikin fadin Alh Tanimu munafiki ne wai yana nuna wa ya fisu kusanci a wajen Dan-uwansu". Kuma gaskiyar magana a yanzu da muka shafe satika kusan uku ba k'aramar shakuwa muka yi da shi ba. Ina matu'kar kad'uwa a duk sadda zuciyata ta ayyana mini muna iya rabuwa. Ban ta'ba kuma shiga irin wannan yanayin a baya ba. Duk kishin Yaya J a kaina ya ha'kura ya bar ni da Nuru domin da kansa ya ce ba zai hana ni kula shi ba, amma shima kada na ce na sallama shi, ya yarda ni din allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka. Dan haka zai cigaba da lalube cikin ruwa har Ubangiji ya taimake shi ya damk'e abin da yake nasa ne