← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 146

Sashe 59

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

miki kwanaki a zauren gida baki ji ba? Wallahi ki mutunta ta kan ki, ki kame bakinki daga zagina. Ni zaki ce wa a gidan uban wa? Ubana zaki zaga? Baki isa ba, rashin kunyar ki ya tsaya a kaina. Ni da kike ganina nasan mutuncin iyayena da gaske, ba wai yaudarar ina sonsu a baki ba, amma na kasa kare musu martabarsu a bayan idonsu ba." Ya mike tsaye ya ri'ke kunnensa alamun gargadi. Da kumfar baki ya ce "Billahillazi kika kuma yi mini lalle a daki sai na wula'kanta ki, ke da gayyar ta ki. Sannan yau ne rana ta karshe da zaki yi gigin zagin iyayena. Ki bari, bana so! Idan kuma kin ki ji, lah shakka ba zaki k'i ga ni ba". Ya tafi ya bar ni ina kuka mai tsananin gaske, domin ba k'aramin shigata marin ya yi ba. Tunda ga wannan lokacin gaba ta k'ullu a tsakaninmu mai tsananin gaske. Ya fita daga al'amarina gaba'daya. Baya bin ta kaina, yana dawowa daga sallar asuba zai fice tun gari bai yi haske ba. Ba zai dawo ba sai wajen Tara. Nan ma yana gama uzzirinsa zai sa kai ya fice. Ba zai dawo ba sai dare. A hakan na fuskanci wajen gini yake zuwa. Fitar asubar ne bansan me yake yi ba. Zuciyata har kissima mini take yi lalata yake fita yi. Dan haka na sake wasarsa, na sake jin haushinsa. Bana girki sai dai na saka almajiri ya siyo mini, abincin siyar wa tunda ana yi a makwabta. Ina samun lalle da kitso. Ban kuma fasa yi a dakin nasa ba. Sai dai kafin ya dawo sun tafi, ni kuma zan gyara masa dakin, sai dai k'amshin muhallabiya ya kama dakin. Bai ta'ba magana ba. Ban sani ba, ko dan bai dawo ya tarar da mu a ciki ba. Ko kuwa ya hakura ne?. Cikin wannan yanayin da muke ciki na yi matu'kar rame wa. Na yi baki. Kullum cikin kuka da b'acin rai na ke. A ranar da na cika wata guda a ranar Dada ta zo ganin dakina. Bulkachuwa da kansa ya dauko ta a mashin ya kawo ta. Ta dinga yaba tsarin dakunan. Amma ta kasa gamsuwa da yanayinmu. A sanyaye ta ce "Mai sunan manya Yabi ta sake kankace wa, ta yi duhu, duk da ita fara ce kal. Kai ma dube ka, babu wani annurin angwanci tare da kai." Ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce "Kowa da yadda yake fuskantar kalubalen duniyar nan ai. Me nake da shi da zan jiyar da Asiya da'di bare na samu nutsuwa da ita. Na barwa Allah komai. Idan na mutu Dada na yafe miki wannan ha'din da kika jagoranci aka yi. Cike nake da fargabar kada auren namu ya sake d'aid'aita zumuncin gidan Marina." Dada ta dauki salati tana fa'din "Ashe har yau baku shirya ba? Ashe ba kalau kuke zaune ba, shi yasa ka dinga zille wa idan na ce ka kawo ni gidan ka?". A hankali ya ce "k'alau muke Dada." Ta kalle shi ta ce "Tashi ka bamu wuri." Bai yi musu ba, ya fita din. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajja Yabi. Me yasa ba zaki kwantar da hankalin ki ba? Mai sunan manya son ki yake irin son nan mai tsananin gaske. Ban ta'ba ganin abin da ya sanyaya shi irin lamarin ki ba. Tun wanccan satin na je gidan Ubaida tana zaune k'alau da mijinta. Sai ke ce zaki kunyatamu?" Na rushe da kuka sosai na ce "Ita mijinta ai baya wula'kanta ta, baya yi mata sanadin da zata kwana ta yini da yunwa. Mijinta mai kamun kai ne. Amma ni kuwa fa?" Kuka ya ci k'arfina sosai. Duk son kan da Dada ta wanzu tana yi a tsakaninmu da su Bulkachuwa a wannan ranar na ga damuwa mai yawa akan fuskarta. Na ga alhinin halin da ta gan ni a ciki a jikinta Ta bu'de baki ta kira shi. Ya amsa ya shigo. Ta ce "Me ka ke yiwa yarinyar nan haka? Ai farkon zaman bata birkice ba, tunda kowa ya zo sai ya ce Yabi tana zaune cikin walwala kamar ba ita ba. Me ya jefa ta cikin wannan tashin hankalin?" Da rashin kuzari ya ce "Zagi irin na tsamar nama ta yi mini. Hakurina ya k'wace na mare ta. Shike nan fa! kuma yau zancen nan an kai sati biyu. Amma ta taurare ta k'i barin abin ya wuce." Ya fa'da cikin damuwa mai yawa. Dada ta ce "Ai baka rarrashe ta ba. Baka ha'diye fishin ka dan ka kawo masalaha ba." Da sauri ya ce "To na yarda, na yi kuskure, taya ni bata hakuri. Bazan sake dukan ta ba, amma ita ma kada ta sake zagi na". Tausayinsa ya cika Dada domin ta sake fahimtar ya fa'da matsanancin soyayyar Yabi. Ta nisa ta ce "kin ji abin da ya ce Yabi. Ki yi ha'kuri, komai ya wuce ba zai sake ba. Na cigaba da kuka sosai. Ina son na fa'da mata ni girkin da ya sanya aka aka yi masa ne, yafi nukurkusa ta fiye da marin. Amma bansan dalilin da ya sanya na kasa fadar wannan maganar ba. Ta dinga rarrashina tamkar ba Dada da bata yi mini sassauci ba. Sai da na yi shiru. Sannan ta kalle shi a zafafe take yi masa magana. "Idan har ka kuma dukanta, to ka tabbatar zan aikawa uwarka ta zo, tunda ka nuna ban isa ba. Ai ba'a baka ita dan ka dinga gwada mata k'arfi ba. Duka duka ma nawa take ne Yabin? Ba zaka yi hakuri da kuruciyar ta ba?" Ya yi shiru ya kasa bu'de baki ya fa'di abubuwan da nake yi masa. Karshe ya buge da bata hakuri da al'kawarin zai canja.
Chapter 59 · 0% Book details