← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 161

Sashe 97

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan sallan magrib duk kowa yadawo gidan harda Hamad, Mamie da Asmeey suka shiga kawo abinci falo suka ijiye kuloli da plates, Hamad sai kallonta yake duk inda tayi nan idanunsa zaiyi har saida Faisal ya dakamai duka acinya akunyace Hamad ya sauke kai kasa Faisal yamai whispering yace “for God sake Babanta is here sai kallon diyarsa kake kaman zaka hadiyeta” tashi daga wajen Faisal yayi sai kawai yakoma dayan kujeran ya zauna kusada Ya Mustapa, da Faisal da Hameed suka cigaba da kuskus Ya Mustapa yakallesu ya daukekai, daidai Asmeey tazo bama Ya Mustapa abinci, zata wuce a sace Hamad yakama gefen hijabinta sarai Ya Mustapa yagani but yayi kaman bai ganiba yafara cin abincinsa, itama Asmeey tsayawa tayi tana gyara plates na hannunta cike da munafunci kaman ba hijabinta aka rikeba, murya chan kasa wanda ko Ya Mustapa bai isa yaji ba yace “serve me what u cook” saiya saki hijabin nata gently, shi bai sani ba amman babu wanda bai gansu a falon ba har Baba, har Munir, har Abba, har Mamie but kowa yayi kaman bai gani ba, Asmeey ta wuce kitchen batare data koma wajen kulolin dake wajen ba nan tsakiyan faloba, spaghetti ta debo a plate mai bala’in kyau tasaka a tray mai kyau, spaghetti yaji naman da akai meat balls dashi da chicken and it’s looks so yummy and appealing a ido, shi taji tanaso taci yasa ta dafa dan tuwon shinkafa akayi da miyan taushe sai jellof rice kuma batason any, zuwa gabansa tayi tasa hannu daya ta dauki coffee table ta ijiye gabansa batare data kallesa ba tadaura tray spaghetti akai, yarinyar dako Ya Mustapa bayan ta debamai abinci anan kulolin dake falon zuwa tayi tabasa a hannu ya karba but ta ijiye na mijinta a kyakkywan coffee table, ga abincin looks delicious sai kawai ta koma kitchen instead of zobo dake falon da other drinks saita kawomai fresh cucumber drink mai sanyi a cup mai kyau, kaman wasa fa dazun da tace bari tama kanta cucumber juice, har wani styling cucumber slice tayi gefen cup dinsa, tazo ta ijiye dan kallonta Hamad yayi asaye yace “thanks! Allah miki Albarka!” Asmeey tawuce tana sunnar dakai, Gwaggo data kasa hakuri tace “bura’uba mu za’a nunama bamu kaiba, kibani tuwo ki bama mijinki taliya mai uban kajin nan? Abani bakin zobo abama miji wani farı da koriya koriyan ruwan lemu” kowa na dakin wani mugun kallo akama Gwaggo dayasa ta hadiye maganan tace “to nai shiru”Hamad ya sunnar da kansa kasa yayi shiruu yakasa ci, Ya Mustapa yace “eat your food ko sai yayi sanyi?” Girgiza kai yayi yadauki fork yadan kalli kowa na dakin ganin duk ba shi ake kallo ba Abba ma hiransa yake da Baba, su Ya Faisal waya suke tabawa ma sunacin abinci, Munir nama Gwaggo da Mamie magana yasa yadan sauke ijiyan zuciya ya kallo Asmeey dake gefen Mamie itama rike da plate na spaghetti dan hada ido sukayi da sauri ta dauke kai tai murmushi kasa kasa, ahankali yadeba spag din yakai bakinsa today is the first time yakecin abincin Asmeey and it taste good for him, bayason cin abinci and anytime dazaici yanason abinci that is stress free, bayason yaji, yanaso abinci ya nuna lusss not half done, meat or chicken he wants it super soft, baison abinci too greasy, and saiyaji abincin Asmeey is exactly abinda yakeso saici yakeyi, rabon dayayi clearing a whole plate of food ya manta kodan yanason Asmeey ne saisa yake ta ci batare dayaji yayi loosing apatite ba oho, kowa kallonsa yake a sace har Mamie, tass ya cinye komi yaci meat balls yaci nama yadauki cucumber drink din ya kora yana ijiye cup, kawai Hameed yace “wlh, wlh Abba ni dai kumin aure wlh nagaji! Haba dan Allah!”Saiga idanunsa na tartaro hawaye haba sai dariya, Baba da Abba saida suka murmusa dan sunsan sabida Hamad da Asmeey yayi maganan, Hameed yace “kaga lafiyayyen taliyan da akama dan uwana kuwa? Dayake mu ba mutane bane aka babbamu tuwo aka bama miji stir fried taliya da juice daban ba zobon mu ba, aka bamu a hannu aka basa a tray harda daurawa a table” yanuna cup din zobonsa na hannu yana nuna na Hamad, kunya yakama Asmeey sosai ta tashi da gudu tai kitchen, Hamadi ma kunya yakamasa, Gwaggo tace “nafara magana an hanani, kofin ma har ado tamasa fa da wanchan abun” tanuna cucumber, tace “haka shima yake kawo kayan dadi ya tsallakeni anan kasa yakaima matarsa sama, jajayen robobin nascrem (icecream) kuke cemasa ko saidai nagani a kwandon bola ni baza’a kawomin ba” mikewa Hamadi yayi a kunyace zai wuce Baba yace “Hamadi abinda akema mahaifiyar mu kenan dama” haba Gwaggo saita fashe da kuka, tace “yauwa Muhammadu Sani ai nasan kai zakayi magana bakason rashin adalci, dana kaiwa Abubakari kara kwabata yayi wai nacire idanuna daga kan yaran nan” dasauri Hamadi yayi kofa yawuce yafita Hameed ya harareta yace “ke kincika sa ido Gwaggon nan” tafi tayi tace “eh nagadai halinmu daya” zatai magana sauran yayyin suka tashi sukai waje dan salla aiko suna fitowa Faisal yace “kunji yanda yake samata albarka kuwa? Harda wani rikemata hijabi yana mata magana kasa kasa tana shafa kwanuka so a dole suyi confusing dinmu, wlh da Asmeey da Hamadi munafukai ne na bugawa jarida” dasauri Ya Abdallahi yace “ni gani nake ma kaman an buga coitus” wani kallo Ya Mustapa yamusu, Ya Faisal yasa dariya yace “ashe ba kai kadai ka lura ba cus they’re very close kaga yanda yake binta da kallo kuwa, Hameed anyi coitus ne? Kaine dan gida” hakanan Hameed saiyaji yana kunyan fadi saiyasa dariya yace “munafukin nan ko yayi zai bari musani ne” Faisal yayi kwafa yace “Allah ya nuna mana randa zamuga Asmeey da ciki that day I will roast Hamadi Billahillazi sai yayi kuka” suka kwashe da dariya Ya Mustapa yace “Allah ya shiryaku” yawucewansa abunsa, yana jiyosu suna cewa zai mana bayani filla filla ta yanda tai ciki idan aruwa tasha muma muje mu nemo ruwan, Ya Mustapa ya girgiza kai aransa yace “brother ku dayariga ya wuce wajen nan”.
EPISODE 6️⃣4️⃣
Chapter 97 · 0% Book details