← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 161

Sashe 13

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

BAUCHI
Mom na saukowa kasa daidai Munir na shigowa falon ta tsareshi da ido, tahowa yayi inda take kanshi akasa ahankali yace “Mom ina wuni” babu wasa kan fuskanta tace “professor ka called me about performance naka lately” iya maganan datayi kenan tana kallonshi sai bakinshi yahau rawa yace “ahhm Mom d….da…dam” tasss! Mom ta dauramai mari daidai Ammi na shigowa falon takalli Mom hakama yara kowa yajuyo dan duk suna falon, Hamad kawai yaduka da sauri jikinshi na rawa yace “Mom I missed class dinshi couple of time ne sabida late coming kuma bai sanar zai mana test ba” azafafe Mom tace “and so wat? Is that an escuse kafadi a course nashi? Wat happened to daily reading danai mandating akanka with your sister na kai revising anything da aka koya muku and learn it kafin kai bacci? Sabida nadan daga maka kafa kwana biyu is that the reason why you’re misbehaving? Do you want me to trash you?” Dasauri yace “Mom kiyakuri I will not fail again” azafafe Mom tace “good!” Tawuce ko kallon mutanen falon batayiba saida Munir yaji bude kofan side nata tashiga sannan yatashi tsaye ahankali, Ammi duk zuciyanta yamata ba dadi yayi wani corridor anan kasa yabude kofa yashiga cus anan dakinshi yake Ammi tawuce sama dakinta, ahankali Asmeey tashiga saukowa kasa tawuce dakin Munir tabude kofan, daga ita sai Munir, sune the only yara da Mom tai gwaranni akansu, Munir is 20 ita 21, Munir na zauna kan gadonshi yadauki paper test din yabude yana kallo 12 over 20 yaci ga hawaye na gangarowa daga idanunshi jin an bude kofan yasa yadago yana ganin Asmeey ne cikeda masifa yace “leave my room” kaman bada ita yake magana ba tazo gaban gadon ta zauna saikuma ta matso dab dashi tasa hannu ta karbi paper test din tana kallo kafin ahankali tasa hannunta tadaura kan kafadanshi ta rungumoshi ta side daura kanshi yayi kan kafadanta kawai saiya fashe da kuka mai ciwo cikin kuka yace “Wlh I will tell Baba ni hostel zan koma I don’t want to leave here, idan Mom na dukanki ke anyhow gaban kowa kaman jaka ni I am a Man bai kamata tana marina agaban kannina ba, i deserve some respect” saida Asmeey tadan dago kanta takalli Munir jin maganan dayayi gabanta har faduwa yayi, cikin whispering na bala’in tsoro tace “Munir stop talking like that akan Mom is not good, I know Mom can be annoying but she loves us so much, she did alot of things for us batare datama jira Baba ba, kaga she bought that power bike for you rannan u were so happy, akan zancen school take takura mana ai but if you look at it very well is still for our own good nan gaba mune zamu ci moriyan karatun mu not her” cikeda rigima irin na yaron da ranshi yabaci yace “tell me menene point na takuramana akan school can’t she just let us be? Look at Ammi bata takurama Ya Ramla ba and still Ya Ramla graduated with a good grade second class upper, I hate wat Mom is doing to us kinsan how many times kike bani tausayi? Kinsan how many times nake shigowa this room and cry because of you? Allah sa kisami mijima that will take you far away from her ni wlh sometimes I wish Ammi ne ma Mamana not Mom!” Daidai lokacin aka bugo kofan dakinsu Mom suka gani atsorace dukansu biyun suka mike tsaye Mom tashigo dakin tareda maida kofan tarufe tasaka key takalli Munir dake kallonta dudda jikinshi na rawa but yaturo baki sosai yadauke kai yaki magana itakuma Asmeey kawai saita boye abayan Munir, Mom ta kalli Munir dake kallonta tace “you feel ka girma you can talk back at me ko Munir? Okay I’m here repeat everything daka fadi just now inba hakaba yau saidai ubanka ya haifi wani wallahi tallahi”.
💫UWA KO UKUBA 💫

✍🏻M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
Chapter 13 · 0% Book details