← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 161

Sashe 45

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Flat dinsu Baba yashiga yara duka an musu wanka sunsa kayan salla an basu breakfast tea da bread sunasha harda yaran su Su Ya Mustapa, dasu Ya Abdallah duka, suna ganin Baba falon kaman makaranta. “Good morning Baba” murmushi Baba yamusu yace “anashan shayi to asha ina zuwa nima abani nawa nasha” wucewa yayi sama ya kalli agogon bango ganin 9 something ya kalli dakin Mom saiyaji ransa na baci yawuce wajen kofa yabude kai tsaye ya shiga ciki, Mom yagani zaune tayi wanka taci gayu tasa wata shadda dayasha aiki ga Mama gefenta dake kada musu shayi, Mama na ganinsa tace “ahh Baban Aya kaine, mun tashi lpy ina kwana” haushi rufe Baba yayi baima amsata ba yace “bamu wuri Maman Nana” tashi Mama tayi takalli Mom tace “bari naje Maman Aya kuka gama kirani awaya” gyadamata kai Mom tayi cikeda isa tana gyara farin glasses na idanunta, Mama tazo tabi ta gefen Baba tawuce tafita ta maida musu da kofan tarufe, Mom ta kallesa ba yabo ba fallasa tace “ina kwana” Baba bai amsata ba rai abace yace “wat are you still doing agidana? I thought I made it clear cewa ki barmin gida this morning”? Tea da Mama tahada mata tasa hannu tadauka takai baki ta kurba, Baba na kallonta wondering tayaya ma ya auri mace mai girman kai haka harya iya zama da ita na all this years suka hayayyafa, kurban tea tayi ta ijiye cup din sannan tasa hannu tadauki wani file dake nan kan table ta mikamai da hannu tana kallonshi ido cikin ido tace “ka sakeni yes naji ka sakeni, but korana daga gidan nan Baban Aya baka isa ba saidai ni na koraka idan naso” kallonta Baba yakeyi sosai ba rahama kan fuskansa yace “gidan mahaifina daya baro kauye yashigo nan birni yagina mana all i did was nakara kudi nasai land nayi renovating gidan nan na maidasa haka na zamani shine zakice ni zaki kora”? “Kwarai! Kajini da kyau Baban Aya, gidan nan is mine ka duba takardun nan kagani da signature ka akai, gida nawa ne!” Abba na tsaye wajen kawai yasa hannu a aljihu zuciyansa na tafarfasa yashiga kiran Faisal yana dagawa yace “Son kazo ina sama” ya katse wayan Mom ta ijiye file din kan table tacigaba da shan tea tana kallon TV abinta, juyawa Baba yayi yabude kofa daidai Faisal na hayowa saman zai wuce side din Baba, Baba yace “gani nan Son” tahowa Faisal yayi suka shigo dakin tare yakarasa wajen table yadauki file yamikama Faisal daya tsaya yana jiran Baba batare daya kalli inda Mom take ballema ya gaida matan ba dan wlh he hates her sosai, Baba yace “takardun gidan nan ne wai gida ta ne tayaya akayi suka dawo nata Faisal”? Faisal is lawyer he knows all this hakan yasa yashiga reviewing komi sannan yakalli Baba yace “Baba ya akayi kayi signing takardun nan?” Baba yayi shiru saiya kalli Mom datamai wani murmushin keta ya dauke kai yakalli Faisal yace “tana bani takardu da dama ina signing na makarantun yaran gidan, kasan kap yaran gidan nan ita ke handling school nasu, sune kawai abinda nake signing saidai tahaka ne tabani na signing ban sani ba” dan ijiyan zuciya Faisal ya sauke yace “gidan nata ne yanzu Baba kayi signing” kurban tea Mom tayi tasauke kasa tadanyi murmushi tace “ilimi nada dadi yau kaga rananta ko Baban Aya? Nasan with this kind of people dakakedasu as yan uwa watarana za’a saka ka sakeni, ka koreni, nasan ba cikakken ilimi gareka ba haka naje dakinka na dauko takardun nayi komi na hada ciki takardun makaranta su Yusra kayi signing yanzu inga ubanda ya isa ya koreni daga gidan nan wlh saidai ni na koreka da yaranka da matarka da mutanen nan daga gidan” Faisal jiyayi kirjinshi na tafarfasa ya cigaba da tsayuwa anan he can insult this bitch of a woman hakan yasa yace “Baba can I go?” Gyadamai kai Baba yayi Faisal yajuya zai wuce Mom tace “kaikuma uwarka kagani ka watsar ba ni Salima ba” juyowa Faisal yayi yamata wani kallo sannan kawai yabude kofa yafice.

Baba yakalli Mom yanuna mata files na hannunshi yace “Salima ni zaki kwacema gida? Gidan mahaifina? Shi zaki maida naki sabida kinga banda sani kan harkan makaranta kaman ke? Salima tunda na aureki nataba cutar da ke? Makarantan nan da abinda kika zama yau is all thanks to me nina saki kikai karatun da kudina? Gidan nan banawa bane eh nasan ninasai filaye kusan uku na hada na karama gidan girma nayi renovation saisa yan uwana suka bar gidan yadauki sunana a paper da komi ba nasu sunayen amman hakan baya nufin nine mai gidan nan gabaki dayansa Yaya na ciki, Kawu na ciki, mahifiyarmu Gwaggo na ciki, this house is gidan gado da mahaifinmu yabari, Salima kin maida gidan da babu zufanki ko daya ciki naki sabida makarantan da karatun da kikayi na ilimin mallakan abinda babu zufanka aciki ko shi karatun lawyer?” Baki Mom ta tabe tace “kanka akeji Baban Aya! Shekarun mu talatin da aure munada diyar 27yrs shine zaka sakeni yanzu? Ni zaka saka? Maisa baka sakeni tun ina yar yarinyataba sai yanzu zakamın sakin rashin mutunci kace na tattara na barmaka gidanka, is something wrong with u?Akwai wani level da ake kaiwa a aure da wlh miji bai isa yasaki matarsa ba, Baban Aya baka isa kasakeni ba wlh! Zama daram babu inda zanje! Gidanku bawai na kwace to sell it kowani abu bane no it’s just lave-rage, idan kanason gidan ku na gadon nan u want to protect it at all cost to ka zauna dani zama daram inba hakaba get ready kahakura kaima da gidan gadonku” Ijiyan zuciya Baba yasauke yana girgiza kai yace “fine gidan nan ba kirike, Alhamdulilah ni da yan uwana ba dukiya ko wani abun duniya ne agabanmu ba kirike gidan bazan taba kaiki kotu kona tsaya yakanki sabida gidan nan ba, but just know this dagayau ke ba matata bace! Me and you are complete strangers! Babu any hakki naki akaina u are on your own, I don’t know you dagayau Salima, gidankuma gashi duk yanda kikeso kiyi dashi gado ne kici, kin nunamin kalanki ba yarmu kadai kika tsana ba yau kin nunamin nima you’ve always hated me, baki sona ko daya Salima inhar kin iya kin amfani da ilimi da wayau kika yaudareni nayi signing takardun gidan nan only shows me baki taba sona ba, kaman yanda bakison mahaifiyata da yan uwana kije bakomi, take” ya ijiye mata files din akan table yawuce yafita Mom tabishi da kallo kirjinta na bugawa feeling very bad a zuciya, she thought Baba would beg her yace ya maidata just to save gidan, itafa she cares so much about that name tag na marraige Mrs Salima Muhammad S Turaki, her name, her status is her identity! Marraige is power! But karfin hali da taurin kai yasa taki magana tasan laslas he will come back to her ta cigaba da shan shayin zuciyanta na tafarfasa kasa daurewa tayi ta tashi tabude kofa tafito dakinsu Asmeey tawuce tabude kofan babu kowa ciki kirjinta ya shiga tafartafasa yana suya kaman an zuba kwalbati.
Chapter 45 · 0% Book details