← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 161

Sashe 51

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣3️⃣

Tashi tayi tawuce wajen window tadaga labule taga Baba yafito tareda Munir sun wuce masallaci chan saigasu Mustapa sun wuce chan kuma Kawu da Baba da Hameed, chan dan har anje ruku’u saiga Hamad shima yafito, Mom ta tsare Hamad da idanu tana gyara glasses nata tana kara karemai kallo, he walks one step at a time da bala’in natsuwa sai wani sheki yake kaman ma wanka yayi, hulan kwankwasa kaji hadisi ke kansa da faran jallabiya, yayi wani irin kyau yana tafiya, tsayawa taga yayi chak duk Mom na kallonsa to her biggest suprise saitaga Hamad yadago kansa sama ya kallo exactly directly window ta chan saman bene sun hada ido, sauke kansa kasa yayi anatse yacigaba da tafiya, Mom tace “mahaukacin psycho, I said it, yaron nan yanada mental disorder normal people sun wuce no body notice me but he did, this are signs na masu mental kolo kolo brain yawan lura ina chan sama tsaye wajen window but jikinsa ya gaya masa ina nan, my daughter will never join blood with you”.
Saida Hamad ya shiga masallaci Mom tabar window tafada bayi tayi wanka tafito tabude wardobe, wani shadda gzinar taciro royal blue dayaji aiki da duwatsu sannan tayi salla tazo ta shirya tsaf takafa wani dauri mai kama da mafici sabida fadi ta kafa glass din nan tafesa turare takoma tazauna tana kada kafa karyansu tasha karya.

Gabaki daya half half tayi baccin jiya she’s trying to wrap kanta around kalman aure da Baba yace yamata, ga damuwa batasan ko Mom ta yarda ko bata yardaba dan tasan Mom basa shiri da this people gashi tun ranan yawon sallan bata sake ganin Mom ba, then ga Ya Hamad, tunaninshi ya addabi zuciyanta kawai fado mata yake arai nonstop, he’s living rent free in her head, her mind, and her heart so duka duka sai asuban nan tasami bacci. Shigowa dakin Mamie tayi dahar tayi wanka ta shirya dan so suke by 8 zasu wuce wajen gadon tayi tana kallon fuskanta she looks so beautiful while sleeping dudda bata gama warkewa ba har yanzu fuskanta da ragiwan ja Mamie tayi murmushi aranta tace “Hamadi na ya auri kyakkyawan yarinya” azahiri kuma tace “Asmeey Asmeey” bude idanunta Asmeey tayi ahankali Mamie tasa hannu tadagota akunyace Asmeey ta sunnar da kanta kasa kawai yausai taji tanajin kunyan Mamie ita kanta Mamie saida ta lura abin yaso bata dariya tace “ni zaki fara wani jin kunya aiko zan mangareki awajen nan” adan kunyace tai murmushi still taki kallon Mamie, ahankali Mamie ta matso saikuma gently ta rungume Asmeey, Asmeey tawani boye kanta jikin Mamie, patting bayanta Mamie tayi tace “Assalamu Alaykum Daughter na!” Runtse idanunta Asmeey tayi da sauri, Mamie tace “I am so lucky d’ana ya auro mini the most amazing and special yarinya kap duniyan nan Asma’u!” Kaman Asmeey zata nutse akasa Mamie tace “Allah ya sanya albarka a aurenku Asmeey, Hamadi yarone na kwarai dana tabbata wata rana zakiyi alfahari kasancewanki matarsa, tashi kiyi wanka kiyi salla Asmeey yau zakije gidan mijinki”kankame Mamie Asmeey tayi kirjinta na bugawa kawai taji she’s having goosebumps, is she happy she’s married to Ya Hamad? Ta tambayi kanta cus bamata san ko farin ciki takeji ba wlh, but one thing she can say for a fact is ko bakinciki daya bataji na an auramata shi, ko jin haushi not at all, batajin hakan but kuma batasan ko she’s happy bane but then she doesn’t feel sad so she finds the whole of abinda takeji wired and creepy feeling da bata taba experiencing in her life ba”
Ganin taki sakinta yasa Mamie tace “ko muje bayi na miki wankan ne?” Dasauri ta girgizama Mamie kai, Mamie tace “to sakeni” ahankali tana kirjin Mamie cikin whispering tace “kunyanki nakeji Mamie” kwashewa da dariya Mamie tayi sosai and she’s so suprise dabataga any sadness regarding aurenba sai kawai taji alakanta abin da yarinyar tagaji da azaban mahaifiyarta saisa take farin ciki da auren, Mamie tayi murmushi tace “cikani naje bayi nasamiki macleen a brush sai kiyi wanka nakawo miki kari kiyi nasan yanzun nan Gwaggo ma zatazo” ahankali tasaki Mamie tana wani juyar da kanta Mamie ta kadakai tawuce tabude drawer dakin inda Aya ta ijiye ma Asmeey kayan dazata saka yau tabi hanya tace “zan kiramiki Ramla ta tayaki” Mamie ta shiga bayi tasamata toothpaste tafito tace “tashi kije” saukowa daga gadon tayi ahankali Mamie tajuya zata fita ahankali tace “thank you Mamie” tawuce bayi da sauri” da kyar ta iya cire rigan jikinta da kanta da hannu dayan tayi komi da komi tafito Ramla tagani zaune kan gado tana mata murmushi sosai tace “Amaryan Ya Hamadi” cus Munir saida yagaya mata jiya but amana dan he couldn’t contain her joy kaman zatai kuka taturo ma Ramla baki tace “ni ba amaryan kowa bace nidai” Ramla ta tashi tana daukan cream tana zuba mata a hannu itama tana sawa tashiga tayata shiryawa ita ta tayata saka hook na bra abaya sannan tasaka gown na atampa mai kyau free dinki ne bubu sabo a atampa Ami kyau dauke kai tayi da sauri saikuma batace bataso ba ganin haka sai kawai Ramla tafice da sauri taje dakinsu tana mamaki chan tadawo da jakan makeup nata ta zauna kan dadduman taciro kwalli tace “bari mufara sashi” tsaf Asmeey ta tsaya tasamata sannan ta shafamata lip gloss bakinta sai kyalli yake Mamie tashigo da tray na tea da chips dasauri Ramla ta tashi ta amsa tace “Mamie kawo” Mamie takalli Asmeey da taga Ramla na mata kwalliya sai kawai Asmeey ta chanza a idanunta, she looks big and matured bubun atampan data sane ko auren da aka mata ne oho but saita chanza, fita Mamie tayi tabasu wuri bayan tace “tadaure taci” Ramla tace “ci sai mu cigaba” chips tasa hannu ta dauka taci saikuma ta kalli Ramla tace “tayani ci muka gama ki shafamin hoda Ya Ramla” ahankali Ramla tace “Asmeey kinason Ya Hamad ne dama?” Dasauri Asmeey ta kalli Ramla sai tafara kokarin magana takasa batasan mezatace ba lips dinta suka shiga rawa da kyar tace “a….a’a” baki Ramla ta tabe tace “munafuka! Wlh kina sonsa cus u look happy today zakibar gidanmu” tass suka cinye Ramla ko ta shafamata hota da abubuwa da dama Asmeey bata hanata ba harda shafa mata eye shadow, tashafa mata janbaki pink tunda taga tanason amata makeup din, tadauki dankwalin atampan tamata dauri mai bala’in kyau sannan tadauki gyalen ta gold tayafa mata bayan tasaka mata da kunne masu kyau takawo mata takalmi flat shoe ta feffesa mata turare sai kawai ta tsaya Tana kallon Asmeey tace “wlh lalle da karayan hannun nan yayi hindering having that full Amarya look but kinga yanda kikai kyau Asmeey zoki kalli madubi” ahankali Asmeey takalli kanta amadubin kaman ba itaba tama kanta kyau kwalliyan da Ya Ramla tamata kaman wata professional makeup artist faduwa gabanta yayi dasauri tace “Ya Ramla mu gog…” shigowa dakin Munir yayi yana washe baki ganin Asmeey saiya tsaya chak kaman ba Asmeey ba she looks exactly like Matar aure, like Amarya, tayi wani irin kyau looking very very matured, da kyar yarufe kofan yataho wajen baiyi wata wata ba kawai ya rungume Asmeey sai kawai ya fashe da kuka Ya Ramla tace “yasin zanje nakira Nana taganka kana kuka” dasauri yadago kansa daga jikin Asmeey idanunsa sunyi jazur duk ruwa ya harari Ya Ramla datai dariya ta kwanta kan gado tana kallonsu sannan yakalli Asmeey da duk saitai wani iri for the first time tunda ta farka saitaji kuka yazo mata amman tadaure, ahankali takai hannunta saman fuskanshi tana gogemai idanunta na tara hawaye tace “na yafemaka duka kudadena dakaci bashi da wanda na baka ijiya” haba Ramla da Munir sai dariya kyakyakya kaman mahaukata, Asmeey tai kwabe kwabe da fuska tana kallonsu tace “to biyani kudina”.
💫UWA KO UKUBA?💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣4️⃣

LAST FREE PAGE🥳
Munir na tsayar da dariyansa ganin tana shirin kuka yace “Ya Ramla Asmeey tafara hankali tayi aure wai ta yafemin bashi harda sababbin 5k da kika bani rannan” suka sake dariya sai kawai ta tsaya tana kallonsu tanajin wani iri sai taji kawai tana kewansu sai kawai tafashe da kuka, Munir dasauri yace “Ya Asmeey menen….” Rungumeshi Asmeey tayi ahankali tace “you are the best brother in this entire world Munir I don’t want to go kano alone, kadingajin maganan Mom please karka bata mata rai kaji” shiru yayi Asmeey tadago kanta tamikama Ya Ramla hannu ta taso itama idanunta sunyi ja tace “Ya Ramla ki gayama Baba zaki bini banso naje ni kadai kinga bantaba zuwa kano ba ke kinji, Ammi duk taje dake bikinsu Ya Mustapa har Ya Faisal ni kadaice bantaba tafiya ba, please kibini tunda ke Kingama school Munir can not travel sabida school follow me” zaro idanu Ramla tayi tace “zan dai zo nan gaba but not now dena kuka toh kinga makeup dinki duk ya baci” dasauri Munir yace “sake mata gaskiya cus Ya Hamadi ya auri fine Babe see my sister naaa who deyy”
Ramla itama tace “fine girl no pimples, Matar Yaya Hamadi agidan Ya Hamadi” kawai Asmeey tasake fashewa da kuka bude kofan akayi Mamie ce ganin yanda Asmeey ke kuka tace “ohhh kuke sata kuka haka”? Shigowa dakin Abba yayi yace “kuzo kuwuce tunda kuka kuke sata” gyalenta Mamie tayafa mata akai tace “muje” kawai sai Asmeey taji kukan yazo mata da gaske Mamie takamata Munir yakama hannunta mai lafiya yana daurewa but he’s feeling very emotional suka fito.
Chapter 51 · 0% Book details