Sashe 8
Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tana kallon gaban white shirt nata tace “banace anytime kikasa white shirt haka ki dinga sa singlet ba aciki can’t u see yanda bra naki ke showing” dan komawa baya kadan tayi da mahaifiyar tata gabanta na faduwa hankali kaman mai tsoron magana tace “Mom duka sunyi datti ne but yau duk zan wanke” wani kallo Mom ta mata hakan yasa tasake matsawa daga kusa da ita dasauri, girgiza kai na takaici tayi tace “be very very careful Husna or you will not like me kikai provoking din kinsanni very well stand up open that drawer ki dauki sabon singlet” tashi tayi dasauri ta tawuce wajen drawer tajawo sabon singlet taciro tabude shi daga leda black ne mai kyau sai kawai ta cire rolling na gyalen tabude shirt nata tadan kalli Mom ganin bata kallonta yasa tacire rigan ta ijiye kan gado zata dauki singlet tasaka authoritatively Mom tace “zonan Husna” dasauri Asmeey tajuyo takalli Mom dataga ta tsareta da idanu saikuma tadan kara singlet din gaban kirjinta cikeda kunya ta taho ahankali har gaban Mom, muryanta har rawa yake tace “g…gani Mom” Mom irin iyayen nan ne masu lura da yaransu sosai, masu sa ido, ga basu tarbiya, yaranta must do abinda takeso ne dukansu haka ta rainesu har yarage saura biyu gabanta yanzu da Asma’u da Munir, wuyanta Mom takai hannu ta taba tace “yaushe eczema yakamaki?” Zaro idanu Asmeey tayi cus ita bama tasani ba tace “ni Mom an ina”? Wuyanta gabaki daya Mom tashiga dubawa zuwa bayanta saikuma ta juyo da ita hannunta tasa, tashi daya ta karbi singlet datake kare kirjinta dashi ta ijiye a gefe, Asmeey tadan sunnar da kanta kasa, ahankali Mom tabi saman kirjinta da kallo tace “stand up” tashi tayi dasauri agaban Mom, Mom tabi cikinta da kallo sannan da masifa tace “eczema ko’ina a jikinki dame kike wanka? Ina soap naki?” Murya chan kasa gabanta na faduwa tace “yakare” Mom aharzuke tace “tun yaushe”? Gaban Asmeey faduwa yake bana wasaba tace “the 3rd day dakika bani” Mom namata wani kallo tace “mesa baki gayamin ba”? Dasauri tace “Mom ai munada sabulu dayawa a bathroom dinmu anyone nagani sainai wanka dashi” shiru Mom tayi saikuma chan cikin kakkausan murya tace “you’re very stupid, wawiyan yarinya kawai mara wayau, shashasha” sauke kanta kasa Asmeey tayi ahankali hannunta yahau rawa, Mom tace “wani irin stupidity zaisa ki kasa gane cewa you’ve always had a sensitive skin? Waya cemiki u can use just anything kika gani kiyi wanka dashi eh? Why do I waste my money ina saimiki separate abubuwan skincare batare da bari kinyi using sabulan da mayukan da Babanku ke kawo muku ba, If you ever made that kind mistake again saina sabamiki shashasha kawai, bacemin daga gani ki wuce ki maida kayanki kizo kiyi briefing dina on case file dana baki last lemme see idan kinyi wannan” gyadama Mom kai tayi asanyaye duk tayi wani iri tawuce ahankali tasaka singlet din sannan tasaka shirt dinta, bata maida veil dinba tazo wajen tabude jakanta taciro file da Mom tabata jiya tabude tadago kanta takalli Mom kirjinta na dukan uku uku, Mom tace “bani distinction na case din but I prefer persuasive brief, inason statements of facts, then give me substantive issues and procedural issues” gyadama Mom kai tayi hannunta nadan rawa tasake bude jakanta tadauko wani book nata datai jotting komi, tabude zata karanta, Mom tamata wani kallon uku saura kwata tace “kikaje law school haka zaki dingayi? Reading from book? how many days nabaki case din nan nace kiyi reviewing?” Murya chan kasa irin na mara gaskiya tace “7days” Mom tahada fuska tana karkada kafa tace “idan kikamin shirme awajen nan ranki zaiyi masifan baci Asma’u, drop that book I’m listening” gyadama Mom kai tayi saita ijiye book din gently and calmly tafara briefing Mom voice nata narawa, tun tana yi Mom na aikinta harta juyo ta natsu tana kallonta she really tried, saida takai procedural issues ne takakare Mom tamata wani kallo hakan yasa hawaye yafado daga idanunta tace “sorry Mom” Mom tace “okay wat is procedural issues?” Anatse tace “ Procedural issues shine irin wat is the appealing party claiming the lower court did wrong example kaman ruling on evidence, jury instructions, granting of summary judgment, etc” Mom ta gyadakai cikeda gamsuwa tace “okay if you know this then a case file dana baki menene Procedural issues na wajen” shiru tasakeyi cus bata karanta yakai wajen ba, Mom na karkada kafafu tace “7days but bakiyi going through this case file dana baki ba sabida kwana biyu nadan daga miki kafa! This should be the last time you will try this wlh kika kara ranki zaiyi masifan baci! I want you to be the best lawyer in this entire Nigeria, I want you to pass bar exam naki, you’re my daughter no body a Bauchi can mention law ba akira sunana ba Mrs Turaki and kece magajiyata my successor, you just have to work hard you have no option, you must study Asma’u dole ne ba negotiation am I clear?” Ahankali Asmeey tace “yes Mom” Mom zata sake magana aka bude kofan tareda sallama Baba ne ya shigo yana sanye da wata lafiyayyan gizna datasha aiki yabi Asmeey da kallo dake zaune akasa kan carpet gaban mahaifiyarta idanunta sunyi ja kaman ma tai kuka yace “kinyi breakfast Ma’u?” Girgizama Baba kai tayi ahankali tace “a’a” agogon hannunshi ya kalla sannan yazo wajen yasa hannu yadagota yace “wuce kije kiyi kari, je Ammi tabaki abinci Ma’u na” murmushi tayi sosai Baba daban ne kawai he’s very sweet, caring, and very affectionate, ahankali tace “toh Baba” wucewa kofa tayi yabita da kallo tafice shikuma yakaraso wajen ya zauna gefen Mom, cikeda nuna rashin jin dadi yace “why are you so hard on this girl? Jibeta kaman ba Hamda na yar bakutu ba duk ta rame haba! Kin addabeta, finally tagama makarantan at least let her rest, all this damuwa yanzu na menene ita da ko list nasu bai fito ba” rufe iPad nata Mom tayi tadauki Hermes bag nata tanasa iPad din ciki tace “Alhaji I don’t know why you are saying all this now! I’ve always been like this to all yarana and Alhamdulillah kai karan kanka you are proud of my upbringing, Asma’u is my daughter, no one loves her better than I do” anatse Baba yace “of course I know that Barrister and ina alfahari da tarbiyan da kika bama yaranmu Aya is a Nurse, Aisha is a journalist working with BBC, ga Asma’u kice dole saitazama lawyer irinki while Munir na MBBS, my point is all yaran nan baki samusu pressure dakike sama Ma’u ba, kwata kwata baki la’akari da she’s still a small gurl, burin dakikasa akanta yasa I don’t even know wat you did dahar Asma’u tayi WAEC at 14yrs tafara university at 15yrs she’s 21 yanzu wai harta gama LLB, please go easy on her, stop pressuring her, karatu is a gradual process all this things dakike forcing nata takoya yanzu she will learn it gradually a law school, karatun dakike sata da menene menene sukesa idan tayi bacci da kyar take tashi da asuba, batada lokacin kanta, bata da lokacin kula da kanta kowace yarinya a gidan nan da kitso akanta banda Asma’u sabida rashin time, please and please I don’t want this! Kibimin y’a ahankali, boko ba dole bane, ba dole Asma’u saita gajeki ba we have other kids agidan ai, allow this girl to be herself please” Baba yafada calmly yana kallon Mom, Mom takalleshi sai kawai ta dauke kai tace “naji” tamike zata tashi yasa hannu yarikota tadawo takalleshi tace “menene kuma”? Murmushi yamata yace “yau ina side naki baki tambayeni mexanci ba” dan lumshe idanu tayi tabude tace “mezakaci Baban Aya”? Murmushi yayi yasa hannu a aljihu yaciro bandir na yan 1k guda uku yabata yace “make anything, gashi this is for you” takalli kudin he’s mutum da baya kallon kudin matansa he always gives them money, murmushi tayi tace “thank you” manna mata kiss yayi a goshi yace “natafi, kibimin yarinya ahankali a kotu” ahankali tace “to adawo lafiya me y’a.” Dan dariya Baba yayi yafice daga dakin. 💫UWA KO UKUBA? 💫