← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 161

Sashe 135

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gently babu karfi jikin Mamie tazo gaban gadon tadan zauna ta kalli Asmeey cikeda tsantsan so dan yanzu morethan ever tama kanta alkawari Asmeey tadawo yarta, irin yar cikinta yarda taduka ta haifo, saita daura hannunta saman cikinta sannan takalli Ya Mustapa tace “taci abinci Doctor?” Girgixama Mamie kai Ya Mustapa yayi ahankali yace “tube za’a samata kokuma asamata nutritional drip cus the way she’s now she can’t eat da kanta or take any magana da kanta saidai ta IV or tube” Shiru Mamie tayi tajuyo takalli Asmeey ahankali tace “azo asamata yarinyana najin yunwa Mustapa, ba abinci a cikin nan nata” tajuyo ta shafa fuskan Asmeey cikeda so tace “kikaji sauki only abincin dakikeso za’a dinga dafawa kinji? Just get well soon Ma’u na kinji? N….na….na…..yi……” muryan Mamie yafara rawa itama takasa daurewa Ya Mustapa ya girgiza mata kai alamun no, da kyar Mamie ta saita kanta tace “nayi alkawari bazanyi kuka ba, amman idan bakiji sauki ba zantayi, get well soon Asmeey natafi dake na kula dake dakaina kinji”? Tayi shiru tana kallonta Abba yadan dafa kafadan Baba dake kallon Asmeey jikinsa babu kwari yakasa komi, motsi hannayen Asmeey sukayi dasauri Hamad ya matso kusa da Mamie yace “Husnahhh Yaya her hand just move” wani irin mikewa hannayen Asmeey sukayi saikuma tashiga dunkule yatsunta kaman wacce zata dawo gurguwa tafara wani irin motsi tana jiniya irin na mahaukata marasa magana yawu na fitowa bakinta tana wani irin nishi tana fotoda harshe tana runtse idanunta tana wani kalan complex ihu. “Uhnnnnnnn……unnnnnnnn…..”Mamie ta tashi daga gadon da sauri tarude, Mustapa ya danna alerm na kiran doctors Hamad yarude yace “Asmeey! Asmeey! Husnah menene!” Kai Asmeey batasan ma metakeyi ba Baba yayi baya zai fadi Abba yarikesa daidai doctors guda biyu na zuwa, daya psychiatrist dayan gynecologist dinta tsoho, da nurses biyu sukace afita afita har Hamad suka kora aka taru akan Asmeey kai Mamie tayi kuka ta gode Allah sukai charko charko agaban dakin.

Saida suka bata 30min dakin sannan suka fito suka wuce while Ya Mustapa yazo wajen jikinsa ba kwari yakallesu, Hamad yace “Yaya what happened to matana?” Dan ijiyan zuciya yasauke yamikama Hamad wata paper yace “her doctor yayi referring nata to psychiatric hospital, wat happened to her now is experiencing na pains datayi she’s feeling kaman yanzu ake mata komi, and she will be having the episodes every here and there, she needs to be transferred to psychiatric hospital” Baba daya rude yace “menene shi psychiatric hospital? Shi asibitin nan fa”? Anatse Munir yace “asibitin mahaukata ne psychiatric hospital, Baba Yaya baiso yafadi mukune but ciwon hauka yadan kama Asmeey! Naga file nata an rubuta type 2 depression dakuma wani abu da bangani da kyau ba! This hospital basu da capacity kula da patient dakeda matsalan kwakwalwa saisa akaece akaita asibitin mahaukata inda zataga physician da nurses dasuka kware akan abinda ke damunta!” Kowa kallon Munir yake har Ya Mustapa cus he just explained abinda he couldn’t bring kansa to explain to his family, wani abu Hamad ya hadiye awuya anatse yace “matana bata haukace ba! She’s just sick!” Kowa ya kallesa gwanin ban tausayi, Baba duk karfin halinsa ya fashe da kuka yana shafa kirji yace “Asma’u hauka? Innalillahi! y’ata bata haukace ba wlh! Za’a mata sauka zataji sauki, wlh bata haukace ba, Munir kada ka kara kirama yar uwarka hauka!” Ijiyan zuciya Hamad ya sauke idanunsa sunyi jajir yakalli Ya Mustapa yace “how many days will it take me nasamanwa Mamie visa?” Kallonsa Mustapa yayi baice komiba, dasauri Ya Aya tace “I have Ya Hamad na garinku!” Shiru Hamad yayi ya fuzar da iska yace “Ya Mustapa I will fly my wife to Washington DC, Aya talk to your husband idan zai yarda kibimu, Hameed contact those your people muji yanda Mamie zata sami express visa na raka mara lafiya, I have medical insurance for me and my family a DC, ko babu ma I will put my last kobo na samawa matana lafiya, I won’t stay still and do nothing! I am her husband and I will call the shot! Asmeey bazataje asibitin mahaukatan Nigeria ba! We are going to DC!” Yakalli Hameed yace “go home bring my system to me we are traveling this week at max!” Baba kallon Hamad kawai yake yanajin wani natsuwa aransa, Asmeey tasami miji dayake tsaye akanta wlh! Alhamdulillah he made the right choice for Asmeey, wato kap rayuwan yarinyar nan d only Allah datasamu mai kyau cikinsa is Hamadi!.

EPISODE 1️⃣1️⃣0️⃣

Cikin 5days aka samawa Mamie Visa kudi ke magana alaji! And Hamad spend it, Aya mijinta ya yarda cus Mamie tadan tsufa ita kadai the work will be too much for her, Ya Aysha tadauki yar Aya ta wuce da ita Abuja.
Business class Hamad yamusu booking da special care na patient shiyakema Asmeey komi ambulance yakaisu airport, special care services daya biya handle check in nasu da kaisu jirgi aka kwantar da Asmeey agado, aka mata fixing duk wani medical abu datake bukata onboard, Hamad na kusada ita while Mamie da Aya na seat nasu jirginsu ya daga, for those 14hrs runtse idanu Hamad baiyiba yanakan Asmeey pampers ake samata, ya chanza mata pampers yana share mata yawu yakama hannunta yarike yana kallonta, wlh yanzu ne ma yakeson Asmeey dan soyayyan dayake mata yanzu yafi nada yawa, like wani irin mugun kaunarta Allah ke dauramai this days kaman zai cinyeta. Daga baya ya kwantar da kansa jikin gadonta yana rikeda hannunta bacci yakamasa koda Mamie tazo dubasu taga yayi bacci yabata tausayi tadauki bargo tarufa masa cus Asmeey arufe take ta tsaya tana kallon Asmeey she’s sleeping tana addu’a kar Allah yabar yarinyar nan ahaka Allah ya warkar ita
Da asuba jirginsu ya sauka akwai sanyi sosai sweater yasama Asmeey kafin kowa yafita special services dinsu akazo aka fitarda su aka sakasu a ambulance direct sai asibitin da Hamad yayi komi dasu a online sunada progress report da medical history na Asmeey da komi sharp sharp akasa Asmeey on admission akai komi da komi suna bari a kwana but just one person dakin Asmeey ita kadai, komi akwai, hospital ne babban gaske they have psychiatric care and support unit a ward din kuma Asmeey take, nan da nan akai plugging nata to so many things, ga name tag nata a hannu an samata uniform farare masu bala’in yau, Aya tace “yaje gida da Mamie tahuta” baiyi musu ba yariga yakira driver sa yana hospital din sukaje suka shiga mota shida Mamie suka tafi gida, hannun Mamie yarike suka shiga elevator har zuwa floor nasa suka wuce gaban dakinsa yabude ko’ina a gyare Mamie tabi gidan da kallo tace “nanne gidanka?” Gyadama Mamie kai yayi Mamie tai murmushi tace “Alhamdulillah” wucewa sukayi two bedroom ne yakaita duka dakunan kafin cikeda girmamawa da bawa mahaifiya daraja yace “wani daki kikeso Mamie”? Dan murmushi Mamie tayi tanuna laptop room nasa tace “nan nakeso kai ka zauna anaku Asmeey zataji sauki soon tare zakuyi zamanku” sunnar dakai yayi yashiga dakin dudda agyare yake tsaf but saiya shiga kakkabe kakkabe Mamie tace “laaaaa me kakeyi Hamadi common jeka huta ruwa zan watsa namana girki shigo da akwatunan mu” Gyadama Mamie kai yayi yafice itakuma tashiga bayi ta tsaya tana kallon komi dantane yasami daukaka haka saida ya shigo taleko tace “zoka nunamin Hamadi” shigowa bayin yayi yanuna mata komi yafice ya kwantar da akwayinta yabude mata komi yaciro kayanta ta jeramata wardrobe kayan abincin ya ijiye akasa yadaga akatin yasa a Sam sannan yafice yaje dakin yayi salla a jirgi saiya zauna yayi shiru, yabar Ya Aya da wayansa dakeda line dinsa na garin nan hakan yasa yakira wayan da landline na dakinsa da sauri tadaga tace “Ya Hamadi!” Murya chan kasa yace “how is she?” Murmushi kadan tayi she just loves yanda Ya Hamadi ke son kanwarsu he’s not even hiding it anymore yanzu oo baya iya boyewa, tace “she’s fine asibitin nada kyau doctors daban daban keta zuwa dubata yanzu bakinta ake dubawa, in sha Allah sauki yakusan samuwa” ijiyan zuciya yasauke kadan yace “I will be back soon please don’t leave her site, there’s Qur’an awayana ki kunna mata, it makes her sleep easily” ahankali Ya Aya tace “tom zan kunna yanzu” ya katse wayan.

Nan da nan Mamie tahada simple porridge na dankalin turawa ta debo a plate tazo dakin knocking tayi shiru hakan yasa tadan bude dakin kadan yana zaune gaban gado but bacci ya kwashesa Hamad is exhausted baya bacci kullum yana cikin browsing condition na Asmeey online, koda yaushe yanakan kula da ita he’s not letting kowa do something for her wucewa gaban gadon tayi ta zauna ahankali firgigit yabude idanu, kallonta yayi saiyadan saukar da kansa kasa yace “sannu da aiki Mamie” abincin Mamie ta debo a spoon anatse tace “yaushe ne zaka koma aiki?” Ahankali yace “next week Monday” spoon din takai bakinsa ahankali yabude baki ya karba yasauke kansa kasa anatse Mamie tace “while Asmeey is recovering kaima u need to take care of yourself kaga yanda karame, kwata kwata bakacin abinci, baka bacci, Hamadi Asmeey zataji sauki trust me! Kallan addu’o’i da rokon Allah da sauka da akasa anayi kan yarinyar nan gakuma namu addu’an she will get better soon kawai ta azabtu ne, but zata warke and she will be stronger than ever trust me, but you have to be strong, haihuwa kuma Allah ke bayarwa daman, zai kara baku, put yourself together kafara shirin komawa aiki kaji”? Gyadama Mamie kai yayi idanunsa na taruwa da hawaye kafin yakai bayan hannu da sauri ya goge yacigaba da basa tass ya cinye sukai waya da yan gida sannan tawuce tai parking abincin dazata kaima Aya tadawo dakin saitaga wani wahalallen bacci ya kwashesa a zaune yake baccin wlh, ahankali tazo tadan gyara masa kwanciya gently ya kwanta taja bargo ta rufamasa tazauna bakin gadon tana kallonsa saita daga hannu sama tace “Ya Allah ka tausayama this children Asma’u da Hamadi don rahamar ka kabasu ikon cin jarabawan nan! Ya Allah lafiya na hannunka, kabawa yarinyar nan dabama asan meke mata ciwo ba lafiya Asmeey ba uhm ba uhm’um, Ya Allah help this girl please!” .

EPISODE 1️⃣1️⃣1️⃣
Chapter 135 · 0% Book details