← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 161

Sashe 25

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Flat dinsu ya shiga zuwa dakinsu da babu kowa, ko ina Hameed yayi oho?Bayi yafada yayi wanka yafito daure da towel yawuce yasa key a kofan sannan yabude akwatinshi kayanshi yaciro komi yasa a wardrobe Hameed yasamai duk abinda yake bukata ya shirya tsaf sannan yaciro laptop dinshi daga bagpack ya kunna yana zama kan gado saikuma yayi jim kafin yakalli wayanshi dake gefenshi sai kawai yadaga wayan……. Gwaggo na zaune anan falo tana surutu duk wani abinda yafaru a Kano yaran nan take bama labarinshi ko gajiya batayi ba, yaran suma sun zagayeta anajin dadin labari harda na takwaran da aka mata wayanta yahau ringing da sauri ta taba wayar dake cikin lalita akasan zanin tace “yooo wa yake kirana ko su Munarin Kauye ne”? Warware zaninta tashiga yi tasa hannu taciro wayan daga lalita takalli screen din kaman ta iya karatu tace “tohh wannan lamba ce batada suna” ta danna dauka takai wayan kunnenta murya ciki ciki akufule Hamad yace “kuma karki kira sunana! Yarinyar chan batai lalleba” yana maganan ya katse wayan Gwaggo tace “wace yarinyar? Ham….” Saikuma tai shiru da sauri tuna yace karta kira sunansa, tashiga bin yaran da kallo daya bayan daya tana sauke wayan daga kunnenta kawai tazare idanun ta mike tace “duk kutashi kuzo ku nunamin kunshin sallan ku daya bayan daya”faduwa gaban Asmeey yayi dake zaune kusa da Ramla cus tasan Gwaggo taga batai lalle ba she will cause trouble tai maza ta mike zata wuce Gwaggo tace “zonan kafin na cimiki mutunci Asama” tsayawa Asmeey tayi tana boye hannunta abaya, Gwaggo tace “mehaka naga kafafunki farare tasss kaman na zabiya! Jibi yara anan ku takwas gasu Hajar hudu ku shabiyu, maza sunsha aski mata sunsha lalli banda ke sai kace yar riko” har lokacin Asmeey taki nuna hannunta ahankali tace “Gwaggo makaranta zani bayan salla saisa an hana lalli a makarantar” dakuwa Gwaggo tamata ta daga murya tace “kinci mai garinku da makaranta yo ko kirista suna zuwa hutun salla balle ke musulma ke baki gajiya da boko sai kace uwarki iyyee? Kinada tabbacin zakiga sallan badi? Babban salla guda hannayenki da kafafu fari sol kaman aljana ina masu lallen wuce ki kiramin su Amina idan basu tafi ba, ke ko sun tafi sai an kirasu” wucewa Amina tayi da gudu ta tafi, Asmeey gabanta na faduwa dumdumdum tace “Gwaggo dan Allah ni bazanyiba ni ki barni” tai stairs da gudu Gwaggo tace “kiramin ubanku Munir” dan shima Munir na falon, tsayawa Asmeey tayi tajuyo da sauri ta kalli Munir daidai yawuce abinshi da sauri Hamda ta sauko tazo wajen zatai magana Baba ya shigo ga Amina da masu lalle da kitso sun shigo falon suma, Gwaggo na daga murya sosai tace “Muhammadu Sani tun kana dan kankani kataba ganin salla tazo da bansa kunshi ba?” Dasauri Baba yace “a’a Gwaggo” cikin fada Gwaggo tace “toh wani dalili zaisa kaf cikin yaran gidan nan Asama ce mara kunshi sai kace wata bare wannan mukai baki ai sai ace mun tsaneta ne ba yar gidan bace” kallon Asmeey Baba yayi da sauri ta sauke kanta kasa zaiyi magana sukaji muryan Mom cikin harshen turenci tace “you know she’s going to Law school bayan salla Alhaji that’s why”kafin Baba yayi magana Gwaggo tace “to yar boko ke duk inda kike saikin nuna mutanen dake wajen basusan komiba kene kikasan komi, ke ba abin kunya bane yarki ta fita daban cikin sauran yara? Komi boki komi boko da boko za’a lahira dazaki hana yarinya yin adon salla? Yin ado da salla sunna ce danko Annabi tsira cewa yayi ranan salla musa kaya mafi kyawu muyi ado mai kyau amman ina zakisan haka sai ilimin yahadu kika sani bana arabi” Mom zatai magana strictly Baba yadaga mata hannu hakan yasa tai shiru, cikeda girmamawa Baba yakalli Gwaggo dake huci yace “Gwaggo kiyikuri yanzu za’a mata” cikeda rigima Gwaggo tace “ai gamasu lallin nan na aika Amina taje ta kirasu anan gabana za’a mata kafin yar boko ta zaga tahanata yi kekuma zauna da shegun idanunta masu kama dana jemage” tanuna Asmeey da atsorace tadan dago kanta ta kallo Mom data mata wani mugun kallo, da sauri ta sauke kanta kasa Mom tajuya daga sama zata koma daki Gwaggo tace “saukowa zakiyi kije kema kisa hannu abayan gida ayi aiki ba daraja kikafi sauran dake wajen ba bakina kima kika fisu ba dan sunfimini ke so dubu” wani kallo Mom tama Gwaggo saikuma ta kalli Baba daya mata kallon baison rigima tayi abinda tace yajuya yafita itama Mom din badan taso ba ta sauko tawuce tafita, Gwaggo tabita da harara, ran Munir fess kaman ya rungume Gwaggo dan dadi aka shiga yima Asmeey lallen dake cikin tsananin tashin hankali duktai zuru zuru sauran yan uwanta harda Munir suka zagayeta suna kallon yanda ake lallen Munir harda matsar da kanninsa baya karsu gwaljema yayarsa lalle, kana ganin Asmeey kasan hankalinta baya jikinta Gwaggo ta buga tsaki tace “Allah yahadaku da jarababbiyan uwa ga yara har yara Allah yabata inba haukan bama yarinya haka kaman Asama wani yahanata yin lalle ba abun tai fada dashi bane amman ita ke hanawa da kanta yarinya kyakkyawa haka son kowa kin wanda yarasa” itadai Asmeey ta saukar da kanta kasa. After magrib aka gama lallen gabaki daya both baki da ja, ta kwanta anan kan doguwan kujera dan ba halin salla suna kallon film tareda sauran yaran, Gwaggo kuma ta fita tsakar gida wajen su Baba tana magana dasu ganin an gama lallen, bude kofa akayi aka shigo Ya Mustapa ne da sauri yaran sukai wajenshi suna gaidashi Ramla ya kalla yace “come here Ramla” dasauri Ramla ta taso taje wajen kofa dayake, jakunkunan ice cream din hannunshi yabata yace “gashi ki raba muku” gyadamai kai tayi dukansu sukai godiya yawuce yafita Ramla tashiga rabon ice cream din na supreme manyan robobi tanaba kowa nasa, tazo gaban Asmeey hakan yasa Asmeey tace “kibani strawberry” Ramla tarike last strawberry tace “nawane shi vanilla zan baki” dasauri Asmeey tace “ai kafin ki dauki strawberry nace miki ni shinakeso” Ramla tace “to baza’a bayar ba” kallon Ramla Asmeey tayi cikin ido sai kawai ta dauke kai tace “ki hada duka ki shanye banso” ran Ramla baci yayi jin abinda Asmeey tace, cikeda masifa tace “ohh kullum akaina ne kikeda bakin rashin kunya ko”? Dasauri Nana tace “Ya Ramla kiyakuri” tashi zaune Asmeey tayi daga kwancen ta harari Nana tace “wayace kisa baki? Da ke akayi?” Akufule Ramla tace “wai ba Baba yace kidenamin rashin kunya ba? Dani kike magana kaman kinyi da sa’an ki? You’re a rude stubborn girl wawiya kawai” ran Asmeey yabaci jin zagin da Ramla tamata tace “ni dai ba wawiya bace” hannu Ramla tasa ta dungure mata kai saida Asmeey takoma baya tsabagen yanda Ramla ta dunguruta tace “okay nine wawiyan kenan? Ki kara magana kiga wlh sai kinsha mari akan kumatun nan naki daya saba shan mari”dasauri Yusra tai wajen kofa tabude tafice ganin Ya Ramla da Ya Asmeey na chachan baki akan ice cream…. Ganin bataga su Baba ba yasa tai wajen motoci inda taga Ya Mustapa tsaye tareda Ya Hamad tai wajensu tana haki tace “Yaya ga Ya Ramla chan da Ya Asmeey suna fada a falo sabida ice cream” “because of ice cream”? Ya Mustapa ya maimaita, gyadamai kai tayi tana zaro idanun gulma tace “she prefers strawberry itakuma Ramla tace vanilla zata bata tace bataso shine Ya Ramla tashiga dungure mata kai tace mata wawiya wai zata mareta akan kumatunta da suka saba shan mari” Ya Mustapa yace “wuce muje” binta yayi zai wuce daidai nan sai ga Mom data zagayo daga backyard tashiga flat din hakan yasa Ya Mustapa yace “ga Mom chan tafi kawai bari basai naje ba” wucewa yayi yakoma inda Hamad yake tsaye dan shi baiyi motsi ba daman. Mom na shiga dakin tagansu suna chachan baki hade giran sama da kasa tayi yaran kowa yayi tsit kaman anga dodanniya gaban kowa na faduwa harda ita Ramlan ganin Mom, maida kofan Mom tayi tarufe takaraso falon yaran kowa na komawa baya, Ramla ta kalla strictly tace “what is going on here”? Ice cream na hannunta Ramla ta nuna mata tace “Mom Ya Mustapah ne yazo yabani ice cream yace narabamana, kingani nabama koya shine nazo naba Asmeey this Vanillah agaban kowa agaban yaran nan tahaumin rashin kunya harda cemin wawiya wai kawai dan ban bata strawberry b……” Kafin takarasa maganan Asmesy ta tari numfashinta muryanta na rawa tace “wlh Mom karya takemin itane tafara cemin wawiy……..” tassssssss! Mom ta dauke Asmeey da lafiyayyen mari da saida ta ijiye kafafunta na lallen kunshi akasa saman tiles hands nata suka kwalbe ajikin chair, ita kanta Ramla saida kirjinta yabuga bata taba kawowa Mom zata daki Asmeey over this silly ice cream issue ba, idanun Asmeey harwani baki sukayi gashi a left side Mom tamata marin inda tamata dazu da safe, Mom namata wani mugun kallo cikin kakkusan murya tace “is this tarbiyan dana baki? Are you stupid kike kiran yayarki dake gaba dake makaryaciya! Are you stupid Asmeey!” Mom ta daka mata tsawa da saida falon ya amsa idanun Asmeey sukai jaaa ga duka kannenta awajen, she felt embarrassed, baki tabude zatai magana amman kuka yasa ta kasa magana cus tana bude baki zata fashe da kuka ga kanninta awajen, Mom dake huci sosai tana kallonta tace “okay I’m talking to you kin sauke kanki kasa ni ga shashasha eh?” Dago kanta tayi ta kalli Mom sai kawai jikinta yahau rawa ganin idanun Mom tace “so….s……” saikuma sorry yakasa fitowa sabida kuka, ran Mom yayi masifar baci tawani fizgo gaban rigan Asmeey haka yarinyar ta taso fuuuu kafafuwanta sukai daba daba akasa skirt nata ya sauka kan black lallin Ramla naso tabata hakuri cus she’s regretting telling Mom amman tsoro take ahada da ita, Mom tashiga daga murya tana jijjiga Asmeey yace “don’t you know how to apologize Asmeey ko saina daddakaki zaki bada hakuri” rawa bakinta yashiga yi idanunta sunyi fiki fiki sun kankance daidai lokacin Gwaggo tabude falon ta shigo tundaga lallin da taga ya kwalbe akasa ta shiga kallo da yanda Mom tarike yarinyar tana kallon yanda hannayen Asmeey da jikinta ke kyarma kawai Gwaggo ta kurma mahaukacin ihu
Chapter 25 · 0% Book details