Sashe 76
Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Mom ta daurama Mamie mugayen idanunta tace “y’ata nazo gani, koko diyar dana haifa ban isa nazo na ganta ba saina tambayeku”? Kallo Mamie tamata sannan takalli Asmeey da jikinta ke rawa tarakube jikin kujera akasa Mamie na mamakin wannan kalan tsoro da yaran nan keji na uwarsu tace “tashi ki daukowa mahaifiyarki lemu da ruwa Asmeey” hannun Mom tadagama Mamie tace “wani lemu? Fanta, coke ko 7up koko Popcola”? Mom tayi wani dariyan keta tace “banashan cheap drinks kuma sune agidan nan” Mamie tawani kalleta Mom ta dauke kai cikeda iko sannan tama Asmeey wani kallo dayasa yarinyar kawai ta dimauce tareda fashewa da kuka murya kasa kasa harwani haki take sabida yanda zuciyanta ya hargitse tace “Mom i…ina kwana! Sannu da zuwa Ya ji…..ki Mom”? Falon Mamie tashigabi da kallo tana neman wayanta da bata ganiba wayanta na sama adakinta, Mom takalli Asmeey tace “tashi muje dakinki I want to talk to you privately!” Mikewa Asmeey tayi tsaye da kyar tana goge kwalla takalli Mamie, cikin tsawa Mom tace “ohh ganin diyata sai kin bani izini Hamidah? Naga kallonki ake”? Dasauri Asmeey tasauke kanta tashiga tafiya, wani kallo Mamie tamata tace “gaki ga ita Salima” wucewa Asmeey tayi sama kafafunta har hardewa suke Mom na biye da ita tana kara kallon yanda yarinyar takara kyau, Asmeey ta chanza mata gabaki daya a idanunta, ahankali Asmeey tabude dakinsu dayake a gyare tsaf yana kamshi turaren wuta Mom tabiyota ciki tanabin dakin da kallo tana tabe baki da yatsine fuska kaman taga kashi tace “look at kurkukun dakike ciki da sunan dakin matan aure wat is this?! This room looks like wani prison room a kuje prison” tanuna dakin da hannu tana daga murya tace “wat kind of cheap paint and curtains ne adakin nan? See gado kaman na almajira, ko Gambo yar aiki na nasiyama yarta dazatai aure gadon dayafi wannan kyau balle ke diyata, carpet din nan ko sadaka aka bani banaso! Wannan dakin shine dakin da aka iyama shi jobless yaron karo karo aka saki ciki? Wait anama baki abinci kuwa? Jibi yanda kika rame kikai duhu? Is that jobless boy feeding you? Are you eating proper balance diet? When was the last time kikaci salad? Good protein kaza ko naman rago? I know it that jobless mahaukacin yaron nan can not feed my daughter? Look at diyata ahaka aka dauketa daga kano? An bawa mahaukaci y’ata da baya ciyar da ita jibi yanda yarinyar ta duk tabi ta lalace” Mamie duk tana jiyo Mom, tasan kuma da ita take sarai, kasa natsuwa tayi ta hayo sama tashiga dakinta taxauna bakin gado tadauki wayanta tai shiru, auren nan means alot to Hameed anything dazaisa takira Abba kowani cikinsu bazasu tsaya inda sukaje ayi komi ba zasu dawo, Hameed can cry for them he will be hurt, hakan yasa takira Hameed ringing na biyu yadaga yace “Mamie na kewana kikeyi ne?” Anatse tace “zaka iya barin abinda kakeyi a bank kazo gida yanzu?” Faduwa gabansa yayi yace “meya faru Mamie? Bakida lafiya ne?” Murmushi tayi tace “lafiya lau just come home now now dan Allah Hameed” kawai tashi hankalinsa yayi yace “okay Mamie, but fadamin menene? Karnaje nai hatsari i am very worried” cikeda damuwa tace “that woman is here” “wace woman Mamie”? “Mahaifiyar Asmeey” cikeda bakin ciki yace “fuck my marriage I am calling Hamad right now I am calling Abba” dasauri Mamie tace “Hameed kabari suyi concentrating wajen neman aurenka” baima tsaya daukan permission ba fitowa yayi wayan na kunnensa yace “Mamie she will hurt our sister again that is idanma bata dauketa tagudu da ita wani waje ba that woman is evil, Mamie gamunan zuwa becareful with her Mamie” ya katse wayan Mamie tafito daga daki falon sama ta zauna.