← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 161

Sashe 38

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Kama Fawaz police sukayi suka samai ankwa, Hameed yakaimai nushi aciki, Baba yabude bayi ahankali saiyawani irin tsayuwan ban tausayi yahade hannayensa biyu akan cikinsa yana kallon Asmeey Abba yazo wajen yana kiran sunayen Allah yaduka yakama Asmeey Munir da idanunshi sukai ja yazo zai kama hannunta ihu tayi na azaba, Baba yaduka dasauri yakalli hannun ahankali yace “ta karye” fashewa da kuka Munir yayi kawai ya rungume Asmeey, Hameed yaduka yadauki gyalenta da dankwalinta dake wajen yazo wajen ahankali ya warware yasake rufa mata ya lullube harda fuskanta murya chan kasa yace “I will carry her kira Ya Mustapa Abba” chak yadaga Asmeey data kasa kallonshi yawuce yafita da ita Munir yabisu abaya da Kawu, Motan su Baba Hameed yasaka ta yana kallon fuskanta yanda take kuka har lokacin ta bala’in galabaita yadan koma baya ahankali, Baba ya shiga bayan Kawu yashiga gaban motan Abba dake bin wajen da kallo yakalli Hameed yace “ina Hamad? Banganshi ba call him” wayansa Hameed yaciro yakira Hamad but baidagaba ahankali yace “Abba let’s go I’m sure yatafiyansa ne kasan shi” dan jimm Abba yayi sannan yashiga gaban motan kusa da Kawu Hameed yawuce yashiga mota shida Munir suka tada motan akabar wajen.
Sosai Baba ya rungume Asmeey baya iya magana but kana ganin fuskanshi kasan kukan zuci yake sosai ahaka sukakai private clinic dinsu, suna zuwa aka karbeta akai ciki da ita Baba yabi doctors dinsu akace ya dakata tukunna dawowa yayi sai kawai yasami waje yadaura hannuwansa aka duka biyun Munir kuma yana tsaye sabida kawai dauriya ne da cijewa yasa baiyi ta kurma ihu yana kuka ba, zama Abba yayi kusada shi hakama Kawu duk suka dafashi kanshi ahaka ayanda yake cikin wani irin murya mai rauni yace “Yaya mezan gayama Allah? Mezan cema Allah? Y’ay’ayan mu amana ne garemu, nakasa killace amanan da Allah yabani dubi abinda wani d’a namiji yama y’ata Yaya” Yayi maganan yana dago kansa idanun Baba kaman zai fashe da kuka ahankali Hameed yakalli Munir dake goge fuskanshi yamai alama yazo suka wuce sukabar wajen, murya chan kasa yace “ko bai mata fyade ba wanda nake gani da kyar ma in baiyiba yariga yabatama diyata rayuwa ya barka suturan danama diyata ya yaye lullubin dana mata domin killace al’auranta” Baba yawani fuzar da iska, yana girgiza kai gwanin ban tausayi yace “Yaya Salima tasan waye yaron nan, wannan yaron yayi suna anan garin Bauchi, ansan yan gidan ko diyata Aya lokacin saida nahanata zuwa daman sabida mahaifiyarta take kawance da yar gidan Maryam kowa ya sansu m…..mesa Salima zata aikamin diya tareda su? Mesa Salima ta tsani y’ata yar cikinta yarda muka haifa tare ta sunna da soyayya”?Murya chan kasa yace “Yaya kunsani banyi makaranta ba da kyar na lallaba nagama sakandire shima bazanyi karyaba bawai nasan wani abu bane hakan yasa duk wani harkan karatu makarantan boko dai kap a hannun Salima yake duka yaran gidan ita ke sakasu a makaranta tayi komi ni nawa tafadamin adaddin kudin da ake bukata na bata tabiya shikenan bani cikin lamarim ta daura buri kan Asma’u saita zama lawyer irinta saita gajeta daganan duk tsanan yafara”Yayi shiru chan yace “dasafe nake fita naje kasuwa sai mangariba nake dawowa bana sanin meke faruwa amman Yaya namaka alkawari duk wanda nagani agabana ina shiga na dauki mataki, Salima tacika fushi da fada da sauri hannu masifaffiya ce duk nai hakuri sabida mun zama daya shekarunmu talatin da aure, akan wani dalili zata hada yarinyar nan da mutanen nan suje gidansu?Meyake faruwa ban sani ba” daidai lokacin Ya Mustapa yashigo asibitin yazo wajen shima Dr su Baba na fitowa duk sukai wajenshi Baba yanuna Mustapa yace “ga dana shima Dr ne dan Allah yimai bayanin komi” gyadamai kai yayi Dr yawuce tareda Ya Mustapa suka shiga dakin su Baba duk suna tsaye su Hameed ma sun fito, kusan 15min sukayi sannan Ya Mustapa yazo wajensu Baba, ahankali yace “yaron baici nasaran bata mata rayuwan ta ba” dasauri Abba da Baba da Kawu duk sukace Alhamdulillah, ahankali Mustapa yace “but ya karya mata hannu sannan akwai lot of ciwo ajikinta signs na she was physically abuse ya daddaketa gaskiya” duk kallon Ya Mustapa suke ahankali yace “an daure mata hannun nace dazaran tagama shan drip a sallameta sabida muje gida zan cigaba da mata treatment agida” atare kowa yace “Alhamdulillah” dan shiru Ya Mustapa yayi saikuma ya matso dab da Baba hakan yasa Baba yace “yi maganar ka Doctor” dan ijiyan zuciya yayi yace “Baba ba hurumina bane ince this, nasan awasu wajen dan mahaifiya na dukan yaransu it’s fine is okay, Baba banda dukan da yaron nan yamata yau akwai ciwuka da tabo da dama ajikin Asmeey abin yayi yawa” yadanyi shiru yanajin nauyin maganan dazaiyi but hakan yasa yace “Baba please ka duba lamarin nan kayi binciken abinda ke faruwa a rayuwan Asmeey da wanda bata fadamaka kar watarana mu wayi gari babu Asmeey cus ciwukan jikinta sunyi yawa kaje dakin kagani da kanka, she’s a girl what will her future husband think of us? Haba ciwukan yayi yawa” Ijiyan zuciya Baba ya sauke ahankali yashiga tafiya wlh he’s feeling so down and unhappy dakin yabude ya shiga, rigan asibiti yasani cus an ciremata riganta daya yaga hannayenta yafara kallo duk tabon ciwo baijin yataba ganin Asmeey da riga mai karamin hannu ba ashe saisa takesawa ga gefen wuyanta ma duk ciwo da kanshi yadaga riganta yana kallon bayan jikinshi na mutuwa da sanyi yadawo tagaba yana dubawa yaga cikinta haka ya lumshe idanu sai kawai ya kifa kansa jikin gadon yakai 10min ahaka sannan yadago kansa yana kallon fuskan yarinyar sannan yatashi yafita yasami waje ya zauna Ya Mustapa yadawo dawani t-shirt sabiwa yabama nurse tasa mata duk suka zauna, Ya Mustapa yayi clearing bill din. Within 30min ruwan yakare Nurse ta tayata sa rigan bata iya amfani da hannunta daya sannan aka sata a wheelchair nurse tafito da ita Asmeey takasa kallon any of them sabida kunya da jin nauyi, She was even wishing inama tamutu agadon asibitin ganin yanda takeyi yasa babu wani wanda yacemata wani abu banda Munir daya kasa daurewa yayi wajen bai damu da duk mutanen wajen ba dukawa yayi agabanta hakan yasa nurse din ta tsaya shiru yayi yana kallon fuskanta duk ja da bruises na ciwo gefen lips dinta har bandage an saka ga hannunta adaure an lullubeta da bargo dakuma gyalenta taki kallon Munir din tayi wani iriiii rawa bakinshi yakeyi ahankali yace “As…..s….m….Asmeeey” gangarowa hawaye sukayi daga idanunta hakan yasa Baba yace “tashi muje gida Munir” dagasa Baba yayi yamike da kyar yana kallon Asmeey da just around two dazu na rana she was fine but yanzu dukta chanza, sukai mota da ita Baba da kanshi yadagata da Munir tashiga mota ya zaunar da ita Munir yashiga yazauna kusa da ita kawai saiya kama hannunta me lafiya yarike Asmeey tai shiru she looks lifeless, Hameed yaja motan suka baro asibitin shima bini bini yana kallonta ta madubin gaba zuciyanshi namai zafi.
Wuraren 5:30 suka isa gida yanda sukabar matan a tsakar gida haka suka shigo gidan, daga Gwaggo, Mamie, Ammi, Ya Aya, matan su Mustapa da yaran dukansu şuna waje banda Mom, motocinsu na shigowa duk suka mike Aya tafara tafiya Gwaggo da sauran duk suka biya abaya.
Baba na bude kofan yafito Aya ta tsaya turus ganin kanwarta ta chanza gabaki daya kana ganinta kasan taci duka hannuwanta biyu tadaura abaki takasa motsi Gwaggo tai wajen hankalinta atashe. “Abubukar meya saman mini jiki? Muhammadu Sani meya sami Asama? Eh ku sanar dani” Mamie da Ammi suka tsaya duka babu wanda ya iya motsi da kyar Abba yace “yanzu ba lokacin magana bane bari mu kaita ciki” ahaukace Gwaggo tace “nace ku gayamin abinda akama jikata tadawo haka? Lafiya kalau tabar gidan nan me aka mata?” Ijiyan zuciya Baba yasauke ahankali yace “Gwaggo bata mata rayuwa yaron yaso yayi amman cikin ikon irin na ubangiji bai cimma burinsa ba yanzu haka yana hannun yan sanda”
“Fawaz ka mikama ga yan sanda”? Dukansu sukaji magannan Mom wani irin kankame Munir Asmeey tayi jikinta yashiga kyarma sabida muryan Mom dataji Hameed dake gaban motan zaune yabita da kallo ta mirror hakama Munir dukansu speechless, dukansu juyawa sukayi suka kalli Mom dataci gayu cikin abaya tafito ga wannan farin glasses din a idanunta tarike handbag idanunta kur kan Baba tace “client dina ka mikama yan sanda Baban Aya”? Baba na kallonta yace “har kotu saina shiga dashi I will get justice for y’ata can you see abinda yama Asmeey look at your daughter Salima! Look at her” yanuna Asmeey dake cikin mota tarike Munir gam ta manna fuskanta awuyan Munir hannayenta na rawa, Baba da ranshi ke tafarfasa yana ihu yace “bakiji komi azuciyanki ba? Waye baisan Fawaz dan gidan Taurari agarin nan ba? Yaro Mara tarbiya da da’a zaki aikamin diya wani waje dashi and ko ajikinki infact fita ma zakiyi daya lalata mata rayuwa fa”? Mom na kallonshi babu ko dar cikeda girman kai da isa tace “ita taso ai! Kaga ba wannan bane agabana I need to get my client out of cell” tawuce, azuciye Baba yace “Salima” tsayawa chak Mom tayi batare data juyoba, Baba yace “wlh kika kuskura kikai bailing yaron nan abakin aurenki!Dasauri kowa ya kalli Baba, Abba zaiyi magana rai abace Baba yace “wlh Yaya bazan saurareka ba ta kuskura ta fiddo yaron nan abakin aurenta saki daya wlh! Bantaba ganin mahaifiya mara kaunar yarta irin Salima ba, Yaya kasan yanda nakejin ciwo wani dan iska yama y’ata wannan abu? Kamata yayi duk ciwon danakeji ita taji sama da nawa tunda itane mahaifiyarta amman kaga ciro yaron zatayi wai toh wlh wlh taje abakin aurenta” shiru Mom tayi na kusan one good minute saita daga kafanta zatai tafiya dasauri Aya tace “Mommm” juyowa Mom tayi ta kalleta dawasu kalan idanu tace “wallahi kikace tak Aya sai ranki yayi masifan baci yau!” Tana maganan tajuya tawuce wajen jeep dinta ran Baba nawani irin suya yanda Mom ta dizgasa agaban duka yaransa da yan uwansa da masu aikinsa yan gadi na gate ta kunna mota taja aka bude mata gate tafice, da kyar Abba ganin Baba bazai iya magana ba yace “Aya dake dasu Ammi da Mamie ku taimaka mata tayi wanka” yakalli Ya Mustapa dashima yayi mutuwan tsaye yace “kabasu maganin dazata sha doctor” saiya kama hannun Baba yawuce dashi flat dinsa zuwa dakinsa asama Kawu yabisu.
Gwaggo tace “ni yar gidansu Tasiu wace kalan annoba Muhammadu Sani ya auro, Hameed!” Takira Hameed daya fito daga mota tana sallallami tace “kodai sato yar nan tayi ba tata bace lokacin cikinta cikin roba take sawa? Ku kunduba”? Wucewa abinsa Hameed yayi boys quarters ganin duka mata ana flat dinsu dan nan aka wuce da Asmeey, Ya Abdullahi dasu Faisal ma duk suka bisa abaya.
Chapter 38 · 0% Book details