← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 161

Sashe 150

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wallahi tallahi batason takara yin rayuwa without Ya Hamadi, shi karan kansa Baba bai yarda da maganan ba hakan yasa yace “Mamie abarsu dai zata warke anan” Mamie tace “tayaya? Naga zuwa aiki yake daga safe har 4 na yamma, yanzu gobe muntafi naija, shima zaije office wazai zauna da Asmeey da bata gamajin sauki ba”? Har cikin ran Mamie she’s saying this sabida yanda taga Hamad yama yarinyar hartai zuru zuru ne, Hamad wani kalan yaro ne da sai ahankali kaman yanda yayi choosing rayuwan alone abaya da rashin magana, yanda yanzu yayi choosing Asmeey nan saiya kusan halaka yarinyar nan da yawan bukata, yara irinsu Hamadi idan suka kama abu daya sun kama kenan sai wani ikon Allah, haba Fisabilillahi jibi Asmeey daga farkawanta baya tunanin komi sai biyan bukatansa, yarinya bata iya tafiya da kyau, kana ganin idanunta kasan ba bacci akai sai hamma take akan wani dalili? Asmeey is mentally not okay kalli dai kalan maganganun data dinga yi rannan da daddare yanzu kuma yaro yasata agaba da jaraba da wanne zataji idan tai shiru Asmeey will break down completely kwana biyu ana abu, ita daman tunda taga Mustapa yahana azo gidan tasan yayi hakane kaninsa ya more bayan yasan sarai Hamadi baisan ya isa ba akan abu, Mamie zata sake magana politely Ya Mustapa yace “Mamie bama gidan nan kafafunta sukaji sauki and it’s all thanks to Hamad! Karmu shiga hakkinsa Mamie sabida mun gansa shiru shiru baida magana” Hameed yace “wlh dan idan nine bazan yarda ba, 8 zuwa 4 she can manage, she’s a big gurl Mamie ai” dan ijiyan zuciya Munir ya sauke cus baison lamarin shima baiso sister sa takoma naija for now, Mamie zatai magana Abba yamata alamu da idanu tai shiru saita hakura ita kawai tanason Asmeey tana tausayinta, Hamad baisan hakuri da sararawa mace ba, he knows nothing akan irin abubuwan nan, mikewa Mamie tayi tawuce dakinsu tace “taho Asmeey inaso nai magana dake” gaban Hamadi faduwa yashigayi why is Mamie calling her? Tanaso ta tambayi Asmeey in private ko tanaso takoma Nigeria ne? Dago kansa ahankali yayi yakalli Ya Mustapa kallon da shi kadai yasan meaning kawai yadauke kansa, ahankali Asmeey tadanyi yunkurin mikewa tsaye gabanta sai bugawa yake duk yanda taso karta kalli Ya Hamadi kasawa tayi dan kallonsa tayi but kansa na wayan daba dannawa yakeba kowa na dakin na lurada ita but kowa yayi kaman baiga komiba, gently tajuya ta daure ta gyara tafiyanta tawuce dakin bude kofan tayi ahankali zaune taga Mamie kan kujeran gaban laptop table din Hamad tana kallon Asmeey da kawai saita kasa kallonta tayi sauke kanta kasa ta maida kofan tarufe Mamie tace “zonan” zuwa Asmeey tayi ta zauna kan gadon da Mamie ke nunamata tazauna ahankali kanta akasa ahankali tace “Mamie gani” dan shiru Mamie tayi chan tace “Asma’u nasan nice mahaifiyar Hamad, but at dsame time Asmeey nasan kalan relationship din dake tsakaninki da taki mahaifiyar, babu wata uwa ko mahaifiya arayuwanki that can stand and speak for you sai ni, you are my daughter Asmeey har zuciyana!” Mamie tadan sauke ijiyan zuciya chan tace “ina shigowa gidan nan kallo daya namiki nasan fitinan Hamad bai barki kin huta ba keda ke fama da rashin lafiya you just got back from dead” sosai Asmeey taji tana kunyan Mamie dudda kanta na kasa sake kama bakın gyalenta tayi tadaura kan fuskanta Mamie tanuna kanta tace “Asmeey kalleni nan ki gayamin gaskiya, natafi dake Nigeria ki kara hutawa ki warke gabaki daya namiki gyaran jiki tunda daman lokacin da za’ayi bikinku bamu samu mun miki sabida ciki, yanzu sai amiki gyara mai kyau sosai ki kara warkewa saiki dawo?” Wani irin kunyan Mamie Asmeey taji, for Mamie takirata daki dudda a falo kowa was against it but she still insisted tamata maganan idan tace no ai kaman tabama Mamie kunya ne ko, next time bazata kara tsayamata hakaba zataji tsoron tai standing up for Asmeey, Asmeey tabata kunya another thing is forget duk yanda Ya Hamadi yabata wahala she loves her husband yanzu arayuwanta babu wanda takeso kaman Ya Hamadi, daman Mom was number 1 mutum datakeso arayuwanta yanzu is Ya Hamadi followed by Munir saisu Aya batason anything dazaisa takara rabuwa da Ya Hamadi, banda haka wanchan yar office din datake ta shige masa she’s not a child to some extend tagane Ya Hamadi nason sex idan bai sameta ba fa yaje ya auri yar office din nasu? Yazatayi da rayuwanta? And her one final reason is Mom! Batason wani abu dazaisa idanuwan nan nata sukara ganin Mom arayuwanta cus zata iya daukan wuka ta chakamata kokuma ta shaketa and she don’t wanna ever raise hand nata on her mother cus Annabi yace kamatudini tudan duk abinda kayi sai anyi maka so batason yaranta su mata hak wata rana the best thing for her is not to ever set eyes on Mom but kuma how can she watsama Mamie that loves her this much har tana kirawota daki kasa a idanu? Saita kasa magana, Mamie dake kallonta tace “Asma’u me kikace? Bani amsa?” Cikeda jin nauyin Mamie da girmamata tace “Mamie ke mahaifiyata ce! Kome kika fadi akaina kin isa ne kuma yayi daidai!” Murmushi Mamie tayi tace “don’t worry kinada papers already zaki iya zuwa nan anytime kawai shiryaki nakeso nayi tsaf ki warke kuma completely ko?” Gyadama Mamie kai tayi, Mamie tace “Allah miki albarka ina zuwa bari naje na gansu” tashi Mamie tayi tafice bata wani dade da fita ba saiga Aya da Munir duk sun shigo dakin suka maida kofa suka rufe Ya Aya tace “me Mamie tace miki”? Ahankali Asmeey tace “tanaso nabita nakoma Nigeria sabida na idasa warkewa!.”
EPISODE 1️⃣3️⃣3️⃣

Atare Munir da Ya Aya sukace “and me kika fada”? Dan shiru Asmeey tayi ta kallesu saikuma tace “nace kome tace is okay by me” mtswww! Dan tsaki Munir yayi yace “common Ya Asmeey akanme bazaki ce no ba? U just woke up after watanni biyar spend time with your husband that has been by your side through this tough time akanme zakibi Mamie ki koma Nigeria? Wat is in the Nigeria for u anyways? When mijin ki na nan eh?” Murya chan kasa Asmeey da itama jikinta yayi sanyi tace “bazan iya gardama da Mamie ba” hararanta Aya tayi tace “Mamie ne mijinki ko Hamadi? Are you a fool Asmeey? Are you telling us Mamie ce keda iko akanki not Hamadi?” Dan shiru Asmeey tayi looking confuse, Ya Aya taja kujera ta zauna tace “Asmeey did u have any idea what Hamadi went through rannan da Mom ta saceki?” Zama shima Munir yayi suka shiga bama Asmeey labarin komi jikin Asmeey yayi sanyi tayi kuka ta gode Allah ko ita taga raman dayayi bayan yatashi saita karajin wani damuwa aranta takai bayan hannunta kan fuskanta ta goge hawaye tace “har cikin raina I don’t wanna go cus banmason something that will make me see Mom but then Mamie spoke to me in a way danaji it will be so rude nace mata no! Ai kaman na zama butulu mara kunya, Ya Hamadi ai is her Son too but bata kalli wannan ba she just want wats best for me kungani saisa” somehow duk sunyi understanding Asmeey kawai Mamie needs to understand cewa Hamadi ba yaro bane, she needs to stop looking at him like her last born mara wayau mai yawan shirme and just trust the boy with Asmeey, she’s feeling kaman he will make mistake da Asmeey duba da yanda yake babu kowa kuma agabansu to correct them and again yarinyar just got out of trauma so she just have to trust Hamadi and believe in him, knocking dakin akayi Baba yashigo cus he noticed Mamie wants to speak to her family and baison ganin yana wurin takasa maganan datake so tayi, bayaso Asmeey taje Nigeria but if Mamie insist zai yarda cus he trust Mamie, she’s a good woman wlh, kawai sai yazo wajen yaransa but harga Allah shima baya wani son Asmeey taje Nigeria .
Chapter 150 · 0% Book details