Sashe 23
Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
daya tun tana yarinya amman shi kadai ne cikin yayyinta magana bai taba hadata dashi ba, shine ma wanda ba’a ganinshi, shi kowa ne bayama magana, kullum yana daki saidai ranan da za’a kauye, hartakai gaban flat dinsu gabanta faduwa yake hannu tasa tabude kofan falon babu kowa ciki banda akwati nan su dake nan falon da masu gadi suka kawo. Gently tace “Assalamu Alaykum” but shiru sai eco na muryanta da flat din yadauka staircase tafara hawa tana wucewa sama daidai nan falon sama ta tsaya ahankali tace “Ya Hamad!” Shiruu kaman babu kowa a side din, dan tafiya tayi zuwa gaban first room dakenan falon saman ahankali tace “Ya Hamad!” Jin shiru yasa ta wuce second door din saitadan taba tareda knocking tace “Ya Hamad!” Shiru babu amsa hakan yasa tace kodai ba nan ya shigo ba wani flat yaje ko boys quarters, maybe tafita taje boy quarters taduba tana tunanin ta juyo Ya Hamad tagani tsaye abayanta awajen mummunan faduwa gabanta yayi sosai har tana neman kurma ihu tahana kanta da kyar ta daura hannuwanta duka biyun akan kirjinta ta saman gyale tana wani kalan mummunan numfashi sabida tsorata datayi ta jingina da bangon wajen da sauri tana numfashi sosai kaman kirjinta zai fita tana kallonshi fuskanshi da ruwa gashin giranshi yawani kwanta sabida lema, dogayen gashin idanunsa sun tattare sabida ruwa pink lips dinshi sunyi wani pink sosai jikinsu duk lema hakama sajenshi a jike ga hannayenshi daya nannade hannun rigan dake jikinsa zuwa sama tafukan hannayensa ajike da alamu dai he was in the bathroom yana wani irin kallonta, hakanan kasa jure kallonshi tayi sabida yanda taga yanada wani irin kyau barinma yanda kwallin idanunsa yamai kyau, tunda take bata taba tsayawa this close to Ya Hamad ba, idanunshi namata wani iri dasauri ta dauke kanta, kawai bakinta yahau rawa, cikin wata yar kamkanuwan murya da bamatasan tanada kalanta ba dayake so scattered sabida tsoro tace “ahhhmmm…..uhmmm dama daman…..” saikuma ta dafa bango kaman zata suma sabida yanda taji yacika mata gaba and he smells damn good raspberry dawani oud da lavender da sandal wood da vanilla takeji yake mata, softly murya ciki ciki yar karama mai wani irin taushi yace “who slapped you?” Dawani irin sauri tadago idanuwanta ta kalleshi today is the first ever time tunda dai tai girma tayi kuma hankali da Ya Hamad ke mata magana, cus he doesn’t talk to them, yaune rana na farko datakejin muryansa agabanta, kallonsa take kaman yanda yake tsaye shima yana kallonta bazaka iya tantance ya yanayinsa yake ba his eyes looks warm calm serious harsh sexy kai komiba, bala’in kwarjini taji yamata idanu lips dinta rawa suka shigayi sai ta shiga wasa da yatsunta tana kallon yatsun murya chan kasa tace “faduwa nayi akasa” to her biggest suprise saitaga Ya Hamad ya matso gabanta dab da ita da sauri tadago idanunta ta kalleshi bai kalli kwayar idanunta ba duko da kanshi yayi daidai tsayinta yashiga sauko da fuskanshi wajajen fuskanta da mahaukacin sauri Asmeey ta kulle idanunta daidai saitin fuskanta Hamad ya sauke fuskanshi yana kallon wajen dayayi sauka idanunshi sukayi kan kwantaccen gashin sajenta mai kyau zare idanunshi yayi daga wajen ya maida idanunshi kan fuskanta yana kallon yanda ta kulle idanunta lips dinta na rawa tana fidgeting fingers nata sosai hakan yasa yadan koma baya ya tsaya getly yace “who slapped you?” “Mom” ta amsa kai tsaye dawani kalan sauri tabude idanunta cikeda mahaukacin mamaki jin yanda tafadi gaskiya what did he do to her? Dago idanunta tayi suka hada idanu again yai mata wani kallo sai kawai yajuya zai koma first room na wajen data fara zuwa dataga kofan abude dasauri tace “Baba yace nakiraka!” Kaman bada shi tai magana ba dakin ya shiga ya maida kofan yarufe batare daya juyoba tabi kofan da kallo tasake kai hannayenta tadaura kan kirjinta dake bugawa none stop saikuma tasake kallon kofan dakin daya shiga sai kawai tawuce harda dan gudu gudunta tashiga sauka daga staircase din har lokacin kirjinta bai dawo daidai ba tayi kofa daidai zata bude aka rigata budewa Ya Hameed ne chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yace “kin gayamai Baba na kiransa?” Gyadamai kai tayi, Hameed yace “meyace?” Kallonshi tayi tace “baice komiba” sama ya kalla saikuma ya kalleta yace “did u put anything a face dinki?” Girgizamai kai tayi alamun a’a, cikeda kulawa yace “put ice okay” gyadamai kai tayi tace “toh” wucewa abinshi yayi yawuce stairs itakuma takama kofan tafice da sauri tayi wajen mai kitso tazauna aka cigaba da mata kitso har lokacin takasa dawowa daidai she’s just feeling somehow sai taba kirjinta take tana feeling heartbeat nata da har lokacin bai dawo daidai ba tanajin muryanshi a kunnuwanta da bata tabaji ba, for as long as tasan kanta Mom bata taba wani abu ta gayama kowa ba hatta Baba, but wat happened data gayamai Mom ce ta mareta yanzu idan ya sanar da wani akasan Mom ce ta mareta yazatayi? Mom ai saita kusan kasheta, baya magana so ba lallai yafada ba but idan yafada fa? Sai lissafi daban daban take aranta ana mata kitson, kusan 10mins da zamanta awajen hakanan kawai ta dago kai ta kallo gaban flat nasu karaf suka hada idanu yabude kofa yafito daga flat dinsu Ya Hameed biyedashi dasauri ta dauke kanta kasa shima haka baimasan mesa ya kallo wajen bishiyan da baida wani nisa da gaban flat dinsu ba yawuce abinshi, hakanan Asmeey taji takasa daurewa samin kanta tayi da sake juyowa tabishi da kallo tundaga yanda yake tafiya anatse kanshi akasa Ya Hameed kuma na danna waya yana magana dashi, “he’s o quiet” tafadi aranta, saida ya shige flat dinsu sannan tadauke kanta tayi shiruu bamatasan mesa taki dawowa daidai ba in something daya faru within just 1min a flat dinsu, hancinta takai wajen kafadanta sai taji kaman tana kamshin dataji a jikinshi, dasauri tace “Mairo dan Allah kunji ina wani kamshi?” Mai kitson tace “kamshin mene Asmeey?” Tsare mai kitson tayi da idanu dan sun dakatar da kitson saitai shiru wondering why is she even asking this kind of question sai kawai ta dauke kai dasauri tace “uhm ni banmasan mesa nai tambayan ba barshi kinji” dan dariya mai kitson tayi tace “ai ke koda yaushe kina kamshi bantaba zama namiki kitso naji kina wari ha Asmeey kin tuna nataba rokonki turare har kika bani” dan murmushi kadan tayi hakanan sai ta manta she’s sad ma sai tunane tunane kawai take.