← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 161

Sashe 47

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masallaci suka shiga aka tada salla sukayi ana sallamewa da 2mins Hameed yatashi zai fice Abba yace “koma ka zauna” zama yayi kusa da Munir dake gefensa, Abba yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa dake azkar sannan Ustaz yacire Mic daga wuyanshi yakashe duka, babban aminin Baba yafara bude wajen da addu’a kowa ya kallesa yace “tom babban aminina ya gayyace ni dan nazo nan nabada auren diyarsa Asma’u” atare gaban Hamad da Hameed da Munir da sauran yayinsu suka buga, rawa hannun Hamad yafara gently yaji saukan hannun Ya Mustapa akan hannunsa dasauri Hamad yadago kansa yakali Ya Mustapa hawaye harsun taru aciki yasauke kansa da sauri kasa, Baba ya kalli Ustaz yace “Bismillah Akaramakallahu” gyaran murya Ustaz yayi yace “Masha Allah ayau mun taru anan domin muzama shaida akan auren daza’a daura tsakanin Hussain Abubakar wato Hamad” dawani irin sauri Hamad yadago kansa kirjinsa ya buga shima Hameed dudda he felt relieved but he was shocked dayaji sunan Hamad, Munir yawani irin jin dadi harda wani motsi kaman zai kwaso shoki Hameed yamai wani annoying look ya natsu yana murmushi, Ustaz yace “da yarmu Asma’u Muhammad Sani, anyi duban jini da sauransu?” Ya Mustapa yace “Hamad AA ne, blood group O negative zai iya auren kowa” Ustaz yace “Masha Allah” nan yacigaba da daurin aure tsakanin Hamad da Asmeey akan sadaki dubu dari Baba ya fiddo da kudin yabiya duk su Abdullahi da Faisal dasu Hameed are in shock cus basu san da maganan ba kawai aka shafe, Abba yace “kawo goron da sweet Doctor” tashi Ya Mustapa yayi sai alokacin ya saki hannun Hamad da kawai ya sauke kansa kasa kirjinsa sai bugawa yake, baimasan wat he is feeling ba, Ya Mustapa yashigo da goro one bag da sweet aka bude aka rarraba Aminnan Baba suka amsa suka sa albarka sukai sallama suka tafi, Yayan Mom Alhaji Mahmood yace “toh ni ku nunamin sirikin nawa ba gane yan biyun nake ba wanne ne Hussein wannene Hassan?” Baba yayi dariya yanuna Hamad yace “gasa nan” sai kawai Hamad yaboye fuskansa a guiwa gwanin kunya sai kace wata Amarya mace, zokaji dariya a masallaci hatta Ustaz saida yayi dariya da su Ya Faisal ma haka shima Hameed saida abin yabasa dariya dudda he’s in shock, Munir harda rike ciki dan wlh Ya Hamad kaman wata mace abinda yayi sosai fa ya kife fuska a knees.
Baba yakame tasa dariyan yace “surukinka akwai kunya Alhaji Mahmood” Yayan Mom yace “ahh ai nagani to Masha Allah, Allah yasa albarka, ga Asma’u dai mun baka amana, mun yarda dakai cus nasan waye mahaifinka tun muna yan samari kafin ya koma kano” Baba yace “kwarai” Abba ya jinjina kai, Alhaji Mahmood yace “zama da mata sai hakuri saikuma anakai zuciya nesa dan haka ina maka fatan alkhairi bari naje Alhaji ma’assalam” yamika musu hannu yana gaisawa da kowa Baba ya bisa dan yanaso yayi magana dashi yajuyo yakalli Munir dake dariya yana washe baki uwa Aj’ı aka daurama aure yace “kai zonan” tashi Munir yayi yabisa da sauri.
Ustaz yamike yayi sallama da Abba yafice, Abba yatashi yadan kalli Hameed daya sunnar da kansa yana sosakai na rashin gaskiya Abba yace “muna komawa gida za’akai kudin aurenka gidansu ita wacce kakeso din tijararre” yawuce yafita, Ya Abdullahi yatashi yana kallon Hamad dahar lokacin yakifa kansa kan guiwansa yace “ango, ango, ango Hamad” Faisal yace “wuhuhuuuu sai amarci ina gayamaka Ya Abdallah” zokaga dariya harshi Ya Mustapa saida yadan kyakyata amman a fuske, Hameed yataso shima yace “ku tsaya kuje Yaya” duk suka tsaya suna kallosa yace “yanzu kowannenmu zai dauki topic ne dazai koyamai kan zaman aure, ni Hameed his twin brother i will take him kiss and hug” zokaga dariya, Ya Faisal dan sune sako dagashi sai su yace “as yayan ango I will teach him tarayya” wani kalan tashi Hamad yayi tsaye da duka hannunsa a fuska zai fice suka rikeshi suna ihu. “Angooo Angooo” kaman zai fashe da kuka Ya Hamad har lokacin hannayensa nakan fuska yace “Yayaaaaa” Ya Mustapa na dan dariya ciki ciki yazo ya karbesa yace “dalla ku cikasa wai mehaka kuna abu kaman yara”Hameed yace “damafa yadan kyasa harda siyamata ice cream” kaman Hamad zaiyi kuka yace “ni banso” yajuya yafita daga masallaci zasu bisa Ya Mustapa yataresu yace “wai sai kun sakashi kuka zaku huta? He’s in shock let him be” Ya Abdullahi yace “Ya Doctor wai ya akayi Abba ya chanza”? Ya Mustapa ya harari Hameed yace “wannan mara kunyan yanada babe so karya wahalan da Asmeey that is already going through alot shine aka hada da Hamad, once we get to kano zamu mai gini a compound a flat da zasu zauna” Ya Faisal yace “but Ya Doctor tayaya Hamad zai fara rayuwa da mace ku baku gansa ba? I’m still worried for Asmeey fa, cus can heeeeeee?” Suka wani bushe da dariya, Ya Mustapa yayi shiru but duk sun gane maganan sa, Ya Mustapa yace “well all I know is he’s a man, komujima komu dade zamuga yaransa” Hameed yayi wani ihun iskanci yace “Yaya kaga dan Allah nima muna komawa kano washe garin rannan kuje gidansu Zee wlh Yaya nakai 2more months banyi aure ba zaku iya rasani washhh” kunnensa Ya Mustapa yakama yace “kaiko naughty boy” ihu Hameed yayi yana dariya yace “sorry Yaya Sorry” Ya Mustapa yace “lemme warn you tundaga yanzu naga ka takurama Hamad koka samai ido ranka sai ya baci and that goes for dukanku” yasaki kunen Hameed yanuna Faisal da Abdallah da duk ke gimtse dariya, yace “allow him to get close to matarsa, banda sa’ido you know yanda Hamad yake wlh na kamaku in anyway ranku zai baci” Faisal yace “Yaya bazan samai ido ba but wlh Yaya curiosity wan kee me I just want to see yanda Hamad zaiyi coitus” Zokaga dariya Hameed harda faduwa akan dadduma cus ya dauka shi kadaine dan iskan ashe Ya Faisal ma dan iska ne, infact yama fishi iya iskanci is the way he said coitus that killed him finish, duk kawai yanda Hamad zaiyi abu akeso agani, Ya Mustapa yakallesu da Faisal da Hameed sai kuma ya kalli Abdullahi dayaga shima rike dariya yake da kyar hannuwansa har zabura suke sabida yanaso ya tuntsure da dariya yace “ohhh hardakai Yayansu akeso aga coitus”? Ya Abdallah yawani bushe da dariya yana kama cikinsa yace “Ya Musty sorry, sorry, is not my fault, to Hamad din namune wlh ko mace bata isa tanuna mai kunya ba, ni I can’t wait to see his wife with belly maybe aruwa zatasha, yaron da a bayi yake chanza kaya yayi wanka how he go do the thing now? With clothes on or off”? Zokaga dariya su ukun kaman mahaukata, ganin suna nema susa shima yayi dariyan babba dashi 40 something years kawai Ya Mustapa yajuya yafice daga masallacin yace “yan iskan yara” sunma manta duk a masallaci suke zama sukayi ciki suna gulma suna bude babin Hamadi.
💫UWA KO UKUBA💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣1️⃣
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈

CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461

EPISODE 2️⃣1️⃣

Tsaf Baba ya sanar da Yayan Mom Alhaji Mahmood abinda ke faruwa tundaga kan zancen fyade, wanda already tun jiya ya sanar dashi awaya dakuma zancen karbe gidan gadonsu datayi, ran Alhaji Mahmood yabaci yanaso yaje yasameta Baba ya hanasa yace “yabarta tayi yanda taga dama da gidan” sundanyi magana kafin yawuce shima, Baba yawuce yatafi.

Baba na zaune dakin Gwaggo, Ammi ta shigo, Aya ta shigo, Gwaggo na zaune daketa washe baki, Mamie ma haka, Baba yace “Aya na aurar da Asmeey!” Dasauri Aya ta kalli Baba tace “Baba Asmeey”? Gyadamata kai yayi yace “ba’a dade da daura aurenta ba anan masallaci sabida inaso jibi su Yaya da Gwaggo suka tashi wucewa su tafi da ita” ahankali Aya da gabanta ke fadi tace “waye mijin Baba”? Murmushi Baba yayi yace “Hamadi!” Murmushi Aya tayi saikuma tayi wata cute dariya sanin Hamadi sarkin kunya takalli Mamie tasake murmushi Mamie ma haka, Baba yakalli Gwaggo yace “Gwaggo bance ki fitar da zancen nan ba Asmeey y’ata ne nakuma aurar da ita na sanar da Baffan ku Aya Alhaji Mahmood hardashi wajen daurin aure, zuwa gobe idan Asmeey tadan sami karfi da kyau zan sanar da ita, kafin kitafi inaso keda su Ramla ku hadamin kayanta tsaf da credentials nata da komi nata zaku iya ciremata kaya kala biyu da zata saka gobe da shi jibin tayi tafiya, sauran zansa akai mota yau din nan dasauri Aya tace “toh Baba” Ammi tayi murmushi tace “Allah sanya alheri Mamie” Mamie tace “Ameen Ameen nagode” dan hira sukayi Aya sai wani dadi takeji.

Ranan sai yamma Ya Aya tatafi sai alokacin Asmeey tafara jin damuwa bataga Mom ba tana nan saita fara tunane tunane Ya Hamad ma tadanyi shiru saita kalli kofa shima bata gansa ba duk saita farajin ba dadin Munir ya shigo yana wani murmushi yahayo gadon yace “Asmeeeyyyyy” dan hararansa tayi tana turo baki tace “sunana kake kira kai tsaye” dariya yasake yi yace “I am just happy sabida ke” “ni?” Asmeey tadan tambayashi dasauri yace “wai Nana” dan murmushi Asmeey tayi bata kara magana ba tadaura kanta kan pillow tana kallon yanda yake taba wayansa yana Instagram sai kawai Mom tasake fadomata arai tace “Munir Mom na side dinta?” Yana jinta Munir yayi banza da ita hannunta mai lafiya tamika ta taba Munir tace “Munir Mom fa”? Batare daya kalleta ba yace “kije takarasa karya dayan hannunki duka kinga saiki huta” shiru tayi bata sake cewa komiba kanta na kan pillow tana kallon wayansa tashiga lumshe idanu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Chapter 47 · 0% Book details