← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 161

Sashe 112

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rabon da Asmeey datayi baccin daya mata dadi harta manta sai yau ko harda huran data sha ne haka ta lapke Gwaggo tai juyin duniya Asmeey ta tashi da asuba tai salla takasa wuraren 5:30 arude Mamie tazo dakin Gwaggo ijiyan zuciya ta sauke ganin Asmeey na bacci a dakin Gwaggo ta sallame salla tace “kaman yarnan irin laulayinki ta dauko mai fitina jiya datazo ta tasani agaba harna fara bacci fa saida natashi nabata hura” dan murmushi Gwaggo tayi tace “tafi abinki zan tada ita anjima kadan tai salla, masu ciki nada uzuri dan Allah” juyawa Mamie tayi tafitoo around 6 Asmeey ta tashi mikewa tayi tashiga bayin Gwaggo tayo alwala tazo tasaka hijabi tai salla tana idarwa tai azkar tasake komawa gado sai wajajen goma Gwaggo ta daka mata duka tace “wai bazaki tashi mutafi biki diyar Hajiyayye ba” tashi Asmeey tayi ahankali tana shafa inda Gwaggo ta daketa tace “bari naje nai wanka” tawuce tafito saita wuce kitchen Mamie na magana da mai aiki she woke up good yau kawai saita rungume Mamie tace “Mamie ina kwana, Mamie zanbi Gwaggo muje biki” layinsu ne bikin just 2house tsakaninsu ko itama zata shiga bikin sai zuwa anjima amman hakan yasa Mamie tace “tom kije amman jeki wanka sai kizo kiyi kari” gyadama Mamie kai tayi tasaketa tawuce tafita Mamie tabita da kallo shes not happy with yanda take raman nan sai duwawu datake karayi da nono shikenan da hasken fata, sama Asmeey taje tafada bayi brush tayi wanda saida tai yellow amai ta lallaba tai wanka tafito daga bayin wayanta data bari dakin na ringing wucewa tayi wajen gado ta tsaya tana kallon wayan Hamad ne hararan wayan tayi tawani juya dudda zuciyanta namata tadauka but tayi alkawari zata daure.

Wani lace mai bala’in kyau sky blue taciro ta zaro sky blue gyale ta shirya tsaf tayi makeup sosai tasa dan kunne ta fesa turare tadauki handbag tazo tadauki wayan datake harara ta jefa ciki tadauki car key kuma da motanta zataje tafito Gwaggo da Mamie kallo suka bita da shi Gwaggo tace “yau naga abu Asama bikinki sai ashirin ga watan gobe wannan gayun ai saikifi Fiduh kyau” Mamie tayi dan murmushi tace “zoki kari” zuwa tayi ta zauna Mamie tabata tea sai waina da pepper soup tea tasha tasha pepper soup ko waina daya bata tababa tana gamaci ta mike tace “muje Gwaggo” tashi Gwaggo tayi tace “saikin shigo Hamida” Asmeey tace “Mamie bye bye”dan zuwa is wajen Mamie tayi saita karbi gyalen Asmeey ta yafamata daga saman kai tace “saikin dawo”
Suka wuce suka fita Mamie takoma kitchen ga mamakin Gwaggo wajen motanta Asmeey tayi tace “Gwaggo da mota zani nagaji ban iya tafiya” Gwaggo tace “nan da nan Asama ni zaki kashe bari kiji banda motar Doctor babu motar wanda nake shiga agidan nan hakanan ku kasheni” bude mota Asmeey tayi tace “nidai natafi” Asmeey ta tada motan tana murmushi tai reverse ta juya Gwaggo tasaki baki Asmeey tai gate abinta mai gadi yabude Gwaggo tabita da kafa tana fita waje tamaga gidan bikin danga mutane awajen saita wuce wajen tayi parking a layin motocin wajen tana jiran Gwaggo takaraso ga maza sosai awajen sai bin motanta ake da kallo thank God tinted ne, Gwaggo na zuwa wajen ta tsaya Asmeey tabude kofan ahankali tafito tanama Gwaggo dake hararanta murmushi sunyi wani irin kyau tace “bakene kikaki shiga ba” rufe motan tayi Gwaggo tasa hannu tawani kama hannunta tace “muje ina rike da ke kafin ki bata” sukai gate din ana kallonsu ahankali sukaji ance Gwaggo. Dasauri Gwaggo tajuyo ganin wani matashi sanye da manyan kaya farare masu kyau da zaiyi tsaran Hamad yasa Gwaggo tace “Aliyuuuuuuu! Aliyuuu gizo idanunta ke mini” dan murmushi yayi yace “nine Gwaggo” Asmeey kuma tajuya abinta tana kallo cikin gidan inda yanmata ke rawa DJ nasaka kida, murmushi yayi yana satan kallon Asmeey yace “ina kwana Gwaggo” daidai nan Asmeey ta fizge hannunta daga na Gwaggo tai cikin gidan, Gwaggo tace “kika bace baruwana” Aliyu yabi Asmeey da kallo yace “wacece ita Gwaggo yaushe Mamie ta haifi mace”? Dariya Gwaggo tayi tace “yar wajen Muhammadu Sani ce, yarona na biyu dake Bauchi” Aliyu ya gyadakai yana kallon Asmeey dahar taje ta zauna akan kujera tana kallon Amarya sa masu rawa, Gwaggo tace “kaga bari naje” Gwaggo ta wuce cikin gida tace “ga Gwaggo gaGwaggo” dagudu Fidduh tawani rungume Gwaggo suna rawa zokaga yanda aka zagaye Gwaggo Asmeey tai shiru tana kallonsu tana murmushi dole Gwaggo tadinga gantali sonta ake sosaitazama Gwaggon kowa da kowa, ringing wayanta yashiga yi ba kakkautawa dasauri tabude jakanta taciro wayan Ya Hamad ne ke kiranta, amman taki dauka harya katse yana sake kira taki dagawa harya katse yasake kira na uku saitai wani murmushi dadi na lullubeta ashe yadamu ta duba from jiya zuwa yanzu yamata 23missws calls, ganin he’s still calling and zuciyanta na gayamata bazai hakura ba saita amsa yasa tamike tai waje tana tafiya ahankali tafito tabude motanta tashiga daidai yana sake kiranta this time video call hade fuska tayi tasa hannu ta dauka taki kallon screen dinma dan bataso ta kallesa zuciyanta ya karaya, ijiyan zuciya Hamad ya sauke ahankali yana zaune kan gado dagashi sai wasu fararen pajama masu kyau da farin hulan sanyi akansa, duk yayi wani iri kaman ma baida lafiya, binta yayi da kallo da motan datake ciki da gayun datayi calmly cikin voice dinsa mai bala’in dadi yace “kina ina!”? Ya Allah! Wani irin faduwa gaban Asmeey yayi jin calm sweet voice nasa datai missing for days har lokacin taki kallon screen din wayan kai tsaye cikeda jin haushi da fushi tace “biki!” Saikuma cikeda jin haushi yanda dai mata keyi idan sunaso sukai maza bango tace “biki nazo” shiru Hamad yayi yana kallonta ranshi ya bala’in sosu cus bikin nan ba’a tambayesa ba, baisan da bikin ba, baimasan nawaye ba but takama ta fice and look at yanda taci gayu da gyale on her shoulders ana ganin gashinta ta keya sosai data gaban kan ga kirjinta a bude dan bata rufe chest nata da mayafi ba, danne zuciyarsa yayi yace “kin sanar dani about bikin nan? Bikin waye? Wa kika sani? Waya baki izinin fita Asma’u?” Juyowa Asmeey tayi ta kallesa cikin ido cikeda masifa zatai magana akai knocking motanta dasauri ta juya ganin mutumin dazu yasa aranta tace “ko Gwaggo ta aika anemota ne” da sauri ta birkito hakan yasa wayan hannunta ya karkace shima Hamad was able to see d glass ya hango wani a tsaye Asmeey ta sauke glass kasa da sauri ta kallesa Aliyu dabai lurada wayan ba at all yace “wat are u doing a mota ke kadai Pretty?” Wani iri Asmeey taji kafin tace “wani abu yana mata wani kallo bayama iya boye yakamı yace “Gwaggo ke nemanki but tunda kina mota bari naje nagaya mata ko” gyadamai kai tayi ya juya Asmeey taja glass din sama hakanan kawai saitaji gabanta yafadi tana addu’a Allah sa Ya Hamadi baiji ba tajuyo ta kalli wayan wlh yanda taga fuskansa saida gabanta yayi mummunan faduwa but ta dake takuma ki magana saima sauke kai tayi daga kallonsa, da kyar Hamad dayakeji kaman zai mutu yace “na barki agida baki tambayeni ba kifito kizo wani biki God knows where har maza na miki magana calling u pretty Asma’u!”
Itama Asmeey cikin fushi tace “na mutu acikin gida kakeso? Ka kamani ka kulle banda saloon bana zuwa ko’ina kiran mutum bakayi how many times nake kiranka baya zuwa? The ones that I’m lucky wayan ya shiga kuma dauka kakeyi? Ai kaima u are there Allah kadai yasan how many women surround you tunda kazama crush din kowa why would you complain dan wani yamin magana kai mijin nawa kamin ne!”?
EPISODE 8️⃣0️⃣

Asmeey tai maganan cikeda tsiwa zuciyanta na tafarfasa tace “kuma duk wanda yamin magana saina amsa dan kaji, ai kaima kana amsawa har shaking hannun mata kanayi yanzu! Kuma nima I will shake duk wanda yabani hannuns……” “Asma’u!” Hamad ya daka mata tsawan da saida ta firgita yace “nabaki one minutes kiwuce ki koma gida ko ranki yabaci!” Dudda ta firgita da yanayin data gansa amman ta daure tace “ni biki nazo ba yanzu zan koma ba” wani iri sosai Hamadi yaji yace “shikenan ki koma ki cigaba da hira dashi a wajen bikin” cikeda tsiwa tace “eh zan koma mucigaba at least yafi wanda baya kirana tunda yaje wani gari, kuma karka kara kirana” ta katse wayan jikinta har rawa yake sabida masifa da bacin rai ta kifa kanta akan kujera sai kuma taji ranta yabaci kawai tafashe da kuka ta tada motan tana reverse tajuya tawuce gida tai horn aka budemata, shiga gidan tayi tai parking takashe motan ta kifa kanta a sitari tafashe da kuka sosai kaman zata kama da wuta takeji.
Chapter 112 · 0% Book details