Sashe 18
Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
see you okay Wifey” shiru tayi jin batayi magana ba yasa yace “are you there” rasa abinda zatace yasa tace “wayana zai mutu my battery is low zansa charge” dasauri tacire wayan daga kunnenta ta katse ta yarda wayan tareda kifa kanta agado tana sauke ijiyan zuciya. Kusan 3mins tayi ahaka sannan ta tashi tawuce wajen wardrobe nasu tabude wani atampa taciro gown tasaka green yamata so simple a jiki tasaka hijab sai kawai tahau kan dadduma. Around 3 Mom ta shigo gidan kashe motanta tayi ta shigo falo Ramla tace “Mom sannu da zuwa” ko kallonta Mom batayiba tawuce daki abinta Ammi tafito daga dakinta takalli Asmeey datagani gaban dakinsu tana kallon bangaren Mom sai kawai tazo tawuceta ta tafi dakin Mom kai tsaye tasa hannu tabude kofan da sallama Mom na zaune tana kokarin ciro iPad mata daga cikin jakanta ganin Ammi saita tsaya tana kallonta Ammi ta maida kofan tarufe tazo ta zauna kan kujeran dake facing na Mom anatse tace “Maman Aya nasan maganan dazan miki ba lallai ta miki dadi ba, sannan ba hurumina bane but all I know shine d’a na kowa ne! Asmeey da Ramla da Munir duk daya suke awajena” Ammi ta danyi shiru sannan ta kalleta ido cikin ido tace “Salima yaran nan mune muka haifosu amman kisani amana ne su agaremu wanda Allah yabamu rannan gobe kiyama Allah zai tambayemugame dasu, hakkinsu na kanmu, idan muka cutar dasu Allah zai saka musu sannan zai hukuntamu! Kene mahaifiyar yaran nan kinsan me kike musu kinsan ya fushinki yake aransu, nasan sun miki laifi but yanda kika sharesu is torchuring them, tun jiya they couldn’t eat sabida ke! They couldn’t sleep sabida ke, Asmeey tun jiya takasa saka lafiyayyen abinci abakinta same with Munir dudda Babansu yatasashi agaba yatafi school tun safe, I’m sure ba lallai yama gane abinda ake koyarda su a makaranta ba! Gabaki daya yaran kin barsu agantale duk sun zama wani iri, idan ciwon zuciya ya samesu ko hawan jini I’m sure you will not forgive yourself Salima! It’s okay for us mothers to be angry but kinfi kowa sanin mai fushinki yakema yaran nan I don’t even know wat I’m doing her but seeing them is breaking my heart, what is so big dazakima Asma’u kalan tabon da hala yaran dazata haifa nan gaba zasu gani a jikinta? Aganina me wacce zatai fada ne da duk wanda zaiyi inflicting such pain ajikin yarki mace ba ke kimata dakanki ba, wallahi Allah zai tsayar dake akan yaran nan, amman kiyakuri idan na shiga huruminki” Ammi na maganan ta tashi tawuce kofa tabude tafita, Mom tabita da kallo ranta ya dagule, yau Aya da Aisha duk saida suka kirata kuma tasan Babansu ne yakira ya sanar da su, kafafu ta kada tai dan ijiyan zuciya ta sauke anatse tace “Lami” da sauri yar aikinsu Lami tashigo dakin anatse tace “gani Hajiya” “kiramin Asmeey” Mom tafadi atakaice hakan yasa Lami tafice. Asmeey na zaune kan gado idanunta sunyi jazur Lami tabude kofansu tace “kizo Maman ki na kiranki Asmeey” dasauri Asmeey ta mike tsaye ta gyadamata kai gabanta faduwa yake, tafito tana tafiya ahankali tawuce side na Mom ahankali tabude kofa, babu kowa a falo hakan yasa tawuce bedroom din tai knocking da sallama daga ciki Mom tace “come inside and lock the door” kofan tabude ahankali babu kowa a dakin gadai kofan bayi a bude maida kofan tayi tarufe tasa lock ta tsaya awajen, daga bathroom Mom tace “zonan” wajen bayin Asmeey tayi gabanta na faduwa sosai taje gaban bayin ta tsaya, Mom na tsaye wajen tap ga bucket tana tara ruwa tama Asmeey wani kallo tace “zonan” wani irin nishi Asmeey tafara tana kallon Mom, yanda kirjinta ke motsi zaka dauka fashewa zaiyi sai kawai hannayenta suka fara rawa jikinta ma haka takasa magana, tadan shigo ta gaba gaban bayin sai kuma taji knees nata sun kasa daukanta tadafa bango zatai kneeling bakinta na kokarin furta magana. “M…..Mo….Mom….” Taku daya Mom tayi tazo wajen tasa hannu tawani fizgota cikin bayin Asmeey zata tsala ihu Mom ta bugata da bangon bayin takai hannayenta kan wuyanta ta shaketa da bala’in kyau idanunta na kadawa tace “because of you mutanen da basu kai komi ba, in educational level i think NCE gareta but tanada audacity da zatazo tana gayamin maganan banza ana cewa Allah zai tambayeni sabida ke, kedin banza da wofi, Babanki bai kwana anan ba dudda yana bangarena and still yabiyoni yacimin mutunci akanki this morning, are you showing people ina making naki sad eh? Are you showing mutane I’m hurting you”? Girgixamata kai Asmeey tayi tana tari idanunta sunyi ja kaman zasu fito, Mom nawani irin kallonta tace “nina haifoki and I can kill you babu abinda zai faru, Shegiya wulakantacciya sabida ke anata kirana, wani daraja gareki Asma’u dan Maman ubanki” wani Irin kyarma tafara idanunta na juyawa kaman zata mutu ganin haka yasa Mom tasaketa Asmeey ta zube awajen tana wani irin tari tana bankarewa tana dukan wuyanta, Mom ta tsaya tana kallonta zuciyanta na tafarfasa sai kwai ta juya ta sunkuci bucket na ruwan datake tarawa ta daga ta juye akan Asmeey tai wani irin ihu da baya fitowa sosai Mom tace “Shegiya jaka kawai duk sanda akamin magana akanki sai kinji ajikinki” zata ijiye bucket din sai kuma ta daga bucket din ta shiga bugama Asmeey tana rafka mata duk ta inda ta samu Asmeey na wani irin kuka tana kare fuskanta da hannayenta akasan bayi, Mom ta jefar da bucket din daya fashe tajuya tafita daga bayin tarufe bayin tana huci sosai. Kaya tawuce ta chanza sannan tafita daga dakin tawuce kitchen dan yauma Baba na side nata. Kusan 1hr tana akasan bayin ahaka sannan ta dafa bango ta lallaba ta tashi ta zauna ta kankame jikinta, this is the reason jiya she tried to protect Munir cus bataso Mom tafaramai Irin wannan dukan gwara ita ayita mata dan tama fara sabawa, sosai takejin sanyi but unless Mom ce tazo ta budeta bata isa ba tafito da kanta ba, wani irin zama tayi kaman almajira tana kallon window bayin hawaye na fita daga idanunta kadan kadan har wajajen 5:30 na yamma sannan taji an shigo flat din. Tana wajen akazo aka bude kofan bayin dasauri takalli Mom jikinta na rawa muryanta baya fita sosai tace “I am sorry Mom” wani kallo Mom tamata ta daka mata tsawa tashi kicire kaya, zabura tayi tamike tsaye da kyar tana dafa bango ta shiga cire kayan Mom na kallonta hawaye sake kwararo mata daga idanu sukayi Mom tace “yayyinki basu taba ja da dokana ba and look at them they’re living a very fruitful life, I will say this to you for the last last! The next time zan ce kiyi abu ki kiyi, na hanaki abu kikiyi, konace kiyi abu ki kiyi wlh wlh zam share sunanki daga cikin yaran dana haifa Alhamdulillah bake kadai gareni ba” daidai tacire rigan yarage sauran pant and bra hannayenta duk ciwo sabida yanda tadinga kare fuskanta dasu da Mom na bugamata bucket, Mom ta mata wani mugun kallo tace “ko ina zakikai girman nono oho jaka kawai saina kaiki an ciresu cus suke saki feeling kaman kin girma bakisan zan iya tattakaki ba kokinkai shakera dari, juya nagani” juyawa tayi Mom tabi bayan nata da kallo duk shaida na dukan shekaran jiya juyawa tayi takoma daki chan ta dawo da magani a hannu ta bude tafara shafamata tana fada tace “kunyi waya da Fawaz”? Gyadama Mom kai tayi alamun eh, Mom tadanyi shiru chan cikin kakkausan murya tace “I choosed him for you! Shizaki aura, shi kadai ne namijin dana yarda dashi in your life kuma bance you should get distracted da soyayya ba, tsakani ki dashi biyayya, your top pariority shine ki gama Law school da good grade, sai bayan kin gama law school zan turashi yaga Babanku asa rana ko ayi biki kinakan NYSC ko bayan NYSC so ki saki jiki dashi yarone mai tarbiya i choosed him for you jiya nina kirashi kotu dan yazo ya ganki dudda ya sanki tun kina little gurl, sister shi kawar yayanki Aya ne u remember right?” Gyadama Mom kai tayi jikinta har sannan rawa yake Mom tace “shima I told him banso yayi distracting naki da soyayya focus on your goals am I clear” ahankali tace “yes Mom” Mom tace “all the files dana baki gobe zaki bani summary kowani case I don’t bloody care how u will do it, get out of my bayi” dasauri ta dauki riganta tadan juyama Mom baya tana maida riganta Mom na kallonta kusan Asmeey tafi yayyinta duka nono har Ramla datake gani tanada shi, ina zatakai nono haka God she’s just turned 21 batason hakan ko kadan, wucewa tayi tafita daga bayin tana tafiya kadan kadan tafice gwanin ban tausayi tana fita Munir na shigowa da sauri tayi gefe zata wuceshi yakama hannunta chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yana kallonta yace “why did u cry? Did Mom beat u again? Are your clothes wet? Ruwa ta watsa miki?” Fizge hannunta tayi da sauri ta kakalo murmushi tace “bayi na wanke ma Mom yes I cried but sabida ta hakura, jeka bama Mom hakuri kaima Munir” Dan Jim Munir yayi yana kallonta tausayin Asmeey yakeji sosai hakan yasa ta turashi ganin yana kokarin magana yawuce side na Mom itama tawuce.