← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 161

Sashe 108

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zuwa falo Umma tace “kuje ciki abinku kunga ni kallo zanyi kabarina nake jira” hannun Asmeey takama tace “muje” tashi Asmeey tayi tana bata ledan şu sweet data kawo Zee ta karba tace “nagode Allah ampana” suka tafi dakinsu, dakinta very simple katifa yar daidai akasa but a gyare ko’ina na kamshi, hijabinta cire ta ijiye tana sanye da atampa mai kyau tawuce kitchen takawo ma Asmeey ruwa da komi datayi Asmeey tazaro idanu takasa magana Zee tace “saikin cinye kuma” akunyace Asmeey tace “nagode” tai shiru batasan mezatace ba banda Ramla sister ta no any girl in her life, ahankali Zee tace “congratulations Ya Hamad, Allah ya taimaka, Allah ya barku tare” akunyace tace “Ameen” Zee tace “to ci abinci tunda baki iya hira ba” Dan murmushi Asmeey tayi tadauki shawarma tabude tafara ci, itama Zee ta dauka tafara ci, tace “Baba yau yakira Abba wai wata uku za’asa January zai kama ko?” Murmushi Asmeey tayi ta gyadamata kai, Zee tace “I am very happy Ya Hameed yace tare za’a hada bikinmu ko”? Gyadamata kai Asmeey tayi, Zee tace “Asmeey kinada yau yaranku keda Ya Hamadi zasuyi kama da larabawa” murmushi Asmeey tayi tace “kema haka kinada kyau sosai” Zee tayi murmushi ahankali Asmeey tace “a ina kuka hadu da Ya Hameed”? Zee na murmushi tace “a bank dinsu access bank” tayi dariya tace “ana tara kudin ankon kawata makotanmu ne, anjima muka fita zan nuna miki gidansu shikenan bansan ya akayi ba scammers suka kirani nabada BVN haka aka kwashe kudin naje bank dinsu inata kuka shi kadai ya lallasheni yabani hakuri harda ruwa yagayamin yanda zanyi yabani number sa kan nakirasa” tayi shiru tace “nayi duka abubuwan dayace nayi na bank da court but kudin bai dawoba nafada masa kinsan meyayi sai kawai yabani kudin har 60k kyauta fa” Asmeey tace “wow” murmushi Zee tayi tace “haka na kaimusu kudin nace na fasa tara kudi gashi gashi, shine mukan gaisa kinsan haryau har gobe yatashi tsokanata mai anko yake cemin” dan dariya Asmeey tayi bata tabajin labarin soyayya ba sai yau, Zee tace “kefa an ina kuka hadu? Though ku cousins ne but ya kuka fara soyayya?” Shiru Asmeey tayi tarasa mezata ce saikuma tai wani cute smile tace “hadamu akayi Ya Hameed bai fadamiki ba?” Girgiza mata kai Zee tayi tace “yagayamin twin nasa yayi aure dakukaje hutun salla shikenan” dan shiru Asmeey tayi takalli Zee sai kawai taji she likes the girl ahankali tace “yanzu inason Ya….Hamad….” Awani irin hankali kaman munafuka tace “so….sai” wani irin murmushi Zee tayi saitaji Asmeey ta burgeta zatai magana sai wayan Asmeey yahau ringing Snapchat video call cus koda yaushe datanta a kunne faduwa gabanta yayi ganin Ya Hamad ne sai taji tana kunyan tadauki video call din harya katse takasa dauka Zee tace “ki dauki wayanki bari kiga nama fita na dubo abinda nasaka a wuta” Zee ta tashi tafita daidai Ya Hamad na kara kira bata ganinshi a screen din sai saman dakin da POP keda bala’in kyau gently tasa hannu ta dauka tadan kara fuskanta kadan daidai shima Hamadi na karo fuskansa kadan from the way yayi position na face dinsa kasan baitaba video call a rayuwansa ba wani irin washe baki Asmeey tayi ganin fuskansa tadan sauke idanunta kasa ganin kallonta yake sosai yasauke ijiyan zuciya gently yace “muga kitson” gyadamai kai tayi tashiga kokarin zare dankwalinta tana bending yana kallonta sauka idanunsa sukayi a boobs nata dasukai flashing dan bata daidaita wayan ba daidai ta nunamai kitso, da kyar yace “yayi kyau lemme switch to normal call” kawai taga yacire video call din wani iri taji cus she wanted to see him, saitai shiru jin shima yayi shiru yasa ahankali tace “ina kwana” jitayi muryansa yayi kasa sosai yace “how are you? Kunzo gidansu Zee?” Gyadamai kai tayi tace “eh” ahankali yace “is she nice to you?” Gyadamai kai tayi tace “yes I like her” dan shiru yayi yace “okay, we will talk idan kin koma gida” ahankali tace “okay bye” shima ahankali yace “bye” ya katse wayan.
EPISODE 7️⃣5️⃣

Partially edited episode!
Wani kuka ne yatasoma Asmeey daurewa tayi dan tana gidan mutane tahana kanta yi Zee tadawo suka cigaba da hira.
**

Mom kwananta biyu a hospital aka sallameta Aya spoke to Baba tabashi hakuri for everything hakan yasa yacema Mom yadawo da ita duk uban taurin kanta saitaji a portion from her worries is gone, let her focus tasami lafiya and take her drugs and just stay peaceful da Baba shima Fawaz bari ta daure ta mance dashi zuwa taji sauki cus health is wealth, but what she’s cooking on her mind har tittle tama abin da YAKIN KARSHE! Baridai taji sauki, har yau kuma taki tambaya ina Munir dudda she miss yaronta cus tasan suna hutu a school, ina yaje? But bakin hali yahana ta tambaya gani take kaman taci baya.

5 dot Ya Hameed yayi parking a kofar gidan tareda Munir suka kirasu fitowa Zee tayi tareda Asmeey sukai hugging juna sukai sallama bayan tabata yaji me dadi data dakawa Mamie Hameed yadanyi waving nata agabansu akunyace takoma ciki suka tafi gida, suna shiga gidansu taga wasu jerin sababbin motoci guda hudu agidan batasan mesaba hakanan mai jan fentin duk sai yafi mata kyau saukowa sukayi tanata kallon motocin daidai Mamie na fitowa tana murmushi Asmeey tai wajen Mamie da gudu Mamie tace “baki nan zazzabi zai kamani banda surutu babu uban abinda Hameed da Munir ke sani sun cikamin gida da ihu wai kwallo suke kallo, zokiga abinda Hamadi ya siyamana”

Mami ta taba ash color motan wajen tace “ga tawa” Asmeey tazaro idanu cikeda murna kafin tai magana Mamie ta taba baka tace “gata Abban ku” Asmeey tabude baki, Mamie ta taba gray tace “gata Hameed” zatai magana Mamie ta taba jan tace “ga taki inji mijinki!” Chak Asmeey ta tsaya saita kara kallon Mamie, saita kalli Munir saikuma ta kalli Ya Jameed kafin takara kallon Mamie da so much confusion tace “t……t…..ta….wa?” Cus kaman bataji Mamie da kyau ba, Mamie ta kalli Hameed dake murmushi tace “bata makullin motan ta Hameed” Hameed yaciro hadadden key motanta yamika mata yace “take ur car key from your husband” chak Asmeey ta sankare like kodai mafarki take itane mai mota karban key Munir yayi yakama hannunta yace “ga makullin motan ki nan” kallon makullin tayi hawaye ya sauka sai kawai tasaki jakanta akasa tayi wajen Mamie da gudu ta rungume Mamie tafashe da kuka tace “Mamie Yaya yasiyamin mota nine mai motan nan ni Mamie?” Waya Hameed yaciro yana mata video Mamie tace “kece Asmeey” sai kawai Asmeey tahau tsalle tana rike da hannun Mamie itane mai mota Mamie tace “bude motan kishiga dena tsalle” dasauri ta zagaya tabude tana kuka sosai tai bismillah ya shiga Munir yashigo yana nuna mata yanda ake kunnawa ta kunna ta danna uban horn haba sai dariya takalli Munir tace “wai da gaske ni Yaya yasiyama mota yar karama dani?” Yanzu nine mai this fine car?” The way Asmeey was super happy made everyone happy da kyar dasauri tace “ina jakana? Wayata” wayanta Munir yadauko mata number Ya Hamad takira but kaman baya online saita mikamai wayan itama bata cika yin hoto ba amman tace yimin hotuna, posing tadingayi a mota na shirme da yarinta da cuteness da menene Munir ma hotunan harda videos tana shirme a motan da wanda take surutu ni yar karama Yaya zai siyawa mota duka Munir Yama Ya Hamad forwarding anan snap sannan duk aka koma cikin gida Hameed yace “anyi magana da driver Baba tsohone mai hankali zai fara koya miki tuki gobe dan ni mammakeki zan banson shirme” dariya tayi tawuce sama tazauna agado tana murmushi sosai tasake kiransa baya shiga ta kwanta tai shiru jin ana kiran magrib ta tashi tai salla she’s so happy tanaso ta gayama sisters nata ba hali sabida abinda Baba yace tahakura tafada baya tai wanka tazo tai salla.

Wuraren 12 nadare harta fara bacci wayanta yahau ringing da sauri tabude idanu tasaki pillow data rungume wanda yanzu bata iya bacci bata rungume sa ba takai wayan kunne kafin tai magana calmly Hamad yace “you know you’re the most beautiful girl I’ve ever seen in my life ko” dan murmushi tayi yace “I just finished watching all ur videos I’m glad I made you happy, do you love your car?” Gyadamai kai tayi da sauri cikin muryan bacci tace “yes! I love it sosai, I love the color, thank you so much Yaya, Allah yamaka albarka!! Allah yakara budi, Allah ya linkamaka dubunsu” Shiru yayi yana sauraronta kaman addu’an tamai dadi asanyaye yace “I can give you the world inhar it will make u this happy that u were today harda tsalle zaki karyamin Mamie” murmushi tayi sosai there’s something tun ranan daya tafi takeson yamata maganan letters datamai but baiyiba that means bai bude ba, ahankali yace “wat i want from you is to be happy, just like today, idan aka kawo miki laptop dinki start writing, get busy before you know it lokaci yatafi har na dawo kokizo okay”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “promise me u will not be crying again!” Ahankali tace “I promise” murmushi yamata yace “good girl nima natura miki pictures dina sorry sai yau natura” dasauri ta katse wayan ta duba chat nasa hotonsa ne yawanci wanda aka masa da baima sani ba sai guda daya rak wanda yamata yana zaune adaki dawani polo mai bala’in kyau white looking damn handsome ta tsaya tanata kallon hoton sai kawai taima hoton reply da I love you Yaya!Hamad baitaba tunanin zata iya gayamai haka a chats ba yace “I love you too thank you for being my wife! I love all the letters you wrote me don’t worry babu wacce zan kalla a nan” dasauri tafita daga chats din dan basically abinda tadinga rubutawa a letters din is karka kalli wasu mata karka kula kowa kaji Yaya inasonka😅😅 karka ma yan office dinku mata murmushi kadinga daure fuska daya bude dariya yadingayi.
Haka takoma bacci.
Chapter 108 · 0% Book details