← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 161

Sashe 109

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari around 9 akace mai tuki yazo ta shirya hijab tasa suka tafi awa daya ne Hamad yace adinga mata by 10:15 tadawo Hameed yace “sakon ki na daki daga mijinki” daki taji taga jakan MacBook dasauri tabude taga laptop guda biyu daya yarubuta Munir akai, waya ma biyu daya yarubuta Munir sai headphone shima yarubuta Munir akai ta kwalama Munir kira yazo Munir kaman zai haukace suka fito falo Ya Hameed yataya Asmeey setup shi Munir nayi da kansa yace “yanzu sai rubutu ko”? Ta gyadamai kai tana murmushi rannan sunyi waya tamai godiya.

Aranan da night takejin zancen zuwa umaran su saitahau kuka ai zai karar da kudin kuma an gama komi na Umaran zasu tafi on 18th of November daganan Mamie da ita zasu wuce Dubai sayo kayan akwatinsu Mamie taje Dubai couple of times but tun zamanin da lokacin Baba nada kudi, Asmeey was so happy itada matan yayyin harda Baba da Kawu da Abba da Mamie nan aka fara shirye shirye while Munir zai tafi gobe cus school medicine no be beans.
Saida tai kuka da Munir sai tafi yaga shatara na arziki haka yatafi gidan yadawo just iya da Mamie kullum tana fita car lesson tadawo zata danyi rubutu despite everything she misses mijinta sosai wlh, gashi xuwa uamaransu sai approaching yake.

Rannan tayi suka tafi bata taba shiga jirgi ba tarike Mamie daga baya tadawo daidai sabida yanda aketa hira zuwa Umara da Famiky da dadi kwanansu 15 itada Mamie suka wuce Dubai duk abinda tazaba ake saya akwatinta dana Zee iri daya just difference of colors akai komi kwnansu bakwai suka dawo Mamie notice tun wannan period din da Asmeey tayi tun Hamad na nan haryau bata karaba sai kawai tadingajin dadi tana kula da yarinyar sosai akman bata gayama kowa komiba har Baba tabarma cikinta, while gidansu ana renovating Wanda ake ginawa yayi nisa akasa bikinsu January 20th Asmeey was so happy Ya Hameed yakaita aka fara papers nata da komi cus Hamadi yazo biki tarezasu koma family gabaki daya ska shiga shirin bikin Asmeey da Hamad, Hameed da Zainab.
EPISODE 7️⃣6️⃣

BONUS💃

Har yau aiki ake agidan an gama renovation na waje, compound interlock, flower garden, kitchen da falo da staircase, gidan yadawo na yan gayu sosai, an gama dakin Mamie so Abba yadawo nata ana nasa sai nasu Hameed sai hallway din saikuma nasu Asmeey.

Today is 19th of December duka duka satinsu daya da dawowa daga dubai, tayi wani mahaukacin haske, fatanta yayi kyau amman bata iyacin abinci sosai, so kwata kwata batai kibaba sai uban nono dake kara tasowa sunyi shar kaman zasuce tass, Mamie is trying for her, the way take selecting abinci da ita akema haka datagaji but Mamie bata gajiya gashi batason kamshin abinci abinda yasa ma yanzu idan ta sauka kasa taje fita suje driving me which yanzu ta iya ana mata process na license ma kawai Ya Hamad baya taba yarda ta fita anguwa ne tun gidan Zee dataje rannan sai saloon Hameed ke kaita yajirata adawo da ita tarasa mesa baya bari tafita at all at least kodan layinsu ne tafita da motanta but baya bari.

Yau tun safe datai breakfast take bacci sai yanzu around 12 taji cikinta nawani irin juyawa tashi tayi zaune tana kama cikinta doguwan rigane na atampa ajikinta babu hula akanta kitson kanta yayi kyau tadade batai ciwon ciki ba hakan saiyasa ta tuna ai tama dade batai MP ba, tun Ya Hamadi na nan fa tayi har yau, shine zaizo yau yafara mata haka dafa gadon tayi ta yunkura zata tashi taje bayi tana mikewa taji jiri na dibanta hakan yasa ba shiri takama gadonsu tarike ahankali tace “Mamie!” But shiru kulle idanunta tayi tashiga tafiya tana dafa bango tana layi at dsame time cikinta nawani irin ciwo tace “Ma….” Daidai ta buge da kofa dan juya mata dakin yake, kofan tashiga bugawa tana Ma….mi….. tana sulalewa kasa daidai Ya Hameed yaci gayu cikin wata shadda yafito fita zaiyi, jin ana buga kofa kadan kadan yasa yabi kofofin wajen da kallo ganin dakinsu Hamad yasa yayi wajen dasauri daidai Asmeey na Maaa…..tana haki dasauri yataba kofan anatse yace “Asmeey” saikuma yaji shiru dasauri yabude kofan kofanma sai bai budu duka ba sabida tana wajen akwance tarike cikinta idanunta na juyawa dasauri Hameed yace “Mamie! Mamie!”Yatura dakin yashiga da sauri yana dukawa gabanta yana kallon kofa yana kiran Mamie kadan kadan Asmeey ke bude idanunta dake juyawa she could see yanda Hameed ke kallon kofa yana maganan da bataji all she’s seeing is Ya Hamad, duk uban azaban ciwo hannunta tamika ahankali takama hannunsa bakinta na motsin. “Yaayaa” juyowa Hameed yayi dasauri yace “Asmeey” yanda idanunta ke juyawa tarike hannunsa gam yasa sai kawai ya ciccibeta ya dauka daidai Mamie na zuwa tace “meya sameta?” Dasauri yace “Mamie let’s go to the hospital since Yaya baya kasan dauko hijabi” yana maganan yashiga tafiya da Asmeey yana sauka Asmeey na kallonsa sosai da juyayyun idanu tana motsi da baki tana magana da ba’aji har motansa yakaita ya ijiyeta abaya zai taso tarikesa da muryan da baya fita tace “yaushe kadawo Yaya” tsayawa Hameed yayi yana kallonta her lips are still shaking tana kallonsa idanunta ajuye hakanan kawai yaji gabansa yafadi dasauri yazare hannunta daga hannunta daidai Mamie na zuwa yafito Mamie tashiga tazauna tana rikota tace “Asmeey meya sameki” murya kasa kasa tace “Yaya kadawo! Yaya kadawo” jin sambatun datake yasa Mamie ta taba kanta tace “Subhanallahi mugun zazzabine ajikinta, kara gudu Hameed bari nakira Abban ku” kara gudu yayi bini bini yana kallon Asmeey ta madubi har sukakai asibitin su Ya Mustapa ansan Mamie da Hameed aka karbi Asmeey sharp sharp akai admitting Hameed yace “nagayama Hamadi Mamie?” Dasauri Mamie tace “kasansa zai rude yahau kuka awajen bari muji tukunna kira Yayanku” daidai Abba na zuwa ya zauna kusa da Mamie suna jiran Dr, chan saiga Dr yafito yakira su Mama duka suka bisa yayi murmushi yace “to Mama da Abba congratulations za’a sami jika!” Murmushi Abba da Mamie sukayi hakama Hameed aransa yace “dan iska Hamadi ai wlh saina gayama su Ya Faisal” Dr yace “tana dauke da juna biyu na kimanin sati takwas wato wata biyu” Hamad yace “just few days to Hamadi yayi tafiya yamata ciki kai wannan yaro”Dr yace “but tanada malaria sosai and malaria baida kyau ajikin mai ciki zamu riketa anan zuwa gobe haka, dan Allah aka koma gida let her be on bed rest kartai aiki sannan ya zamto tana cikin kwanciyan hankali always saikuma ba hayaniya ko damuwa sannan next week inda hali ku kawota tafara Antinatal” Mamie da Abba suka gyadamai kai sai murmushi suke Dr yace “anjima kadan zaku iya ganinta” tashi Abba sukayi suka godema Dr suka fito Abba na fito daidai number Baba dan kiransa Baba na dauka Abba yace “to barka barka Allah fa ya albarkaci zuri’a Muhammadu Sani, wannan karan Jikan namu ne namu namu”
Maganan Abba yasa Baba yagane Asmeey na dauke da juna biyu yace “ahhh Alhamdulillah Alhamdulilah ubangiji Allah ya dayyaba yasa albarka, Allah ya raya tana ina”? Abba yace “muna asibiti ba lafiya wai tanada malaria za’a rikemu dai zuwa gobe” Baba yace “Toh Allah yakara mata lafiya Allah ya sauketa lpy” Abba yace “Ameen Ameen” sauki sallama Baba was very very happy

Wajajen 9 Asmeey ke bude idanunta ahankali Hameed kadai tagani zaune kan kujera da waya a kunnensa Mamie kuma na salla, alamun motsin mutum yasa yakalli gadon dasauri ganin Asmeey na kokarin tashi zaune yasa yace “I will call u later” ya katse wayan yazo wajen gadon yace “careful Asmeey bari na tada gadon” taba botun yayi katifan yataso tashiga bin dakin da kallo cikin rashin karfi saikuma ta kalli Ya Hameed dake kallonta tace “ina Yaya?” Hameed na kallonta yace “wani Yayan?” Cikin raunin murya tace “Ya Hamad” dan murmushi yayi yace “aiko kinata sumbatu da sunansa dazu to yana chan kasan nan” fashewa da kuka tayi ahankali tace “wlh na gansa” tasowa Mamie data sallame salla tayi tace “kindaiga Hameed dai ko Asmeey” ahankali Asmeey tace “Mamie wlh na gansa shiya daukeni” zama Mamie tayi kusada ita tace “Hameed yajiyoki yazo ya daukeki” dasauri ta kalli Hameed, mugun kallo ya watsamata yawuce abinsa yafita daga dakin, Mamie tace “mezakici?” Fuskanta ta share tace “tea” tea Mami tamata ta karba tana kallon tea brain dinta na kokarin recalling taga Ya Hamad har tana rike hannunsa, ai tasan Ya Hameed baida idanu kaman na Ya Hamad dazu har idanun Ya Hamadi tagani, da kyar tasha tea akazo aka mata wasu allura nan da nan tayi wani bacci koda Hameed yadawo tayi bacci ko kallonta baiyiba yama Mamie sallama yatafi.
Ba’a sanar da Hamad ba anaso sai an koma gida, washe gari aka sallamesu aka bata magunguna.
**
Chapter 109 · 0% Book details