← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 161

Sashe 84

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakinsa da Hameed yashiga yayi wanka tun dazu yasa ya kwanta kawai ana kallon sama all maganganun da Ya Mustapa yamai na yawo akansa especially part din hakkinta since that’s wat she needs yanzu medically, he wants Janna baiso ya shiga wuta sai kawai yaji he’s ready, wayansa yadauka yabude browser yayi googling how to have the best sex with your wife, danne kunya yayi yana kallon pictures to be honest he knows all this kawai dai he wants to do it well ne, har kusan raba dare yayi yana tara ilimi akan jima’i akansa yana research some har rufe fuska yake yi.
EPISODE 4️⃣9️⃣

Kasa bacci Asmeey tayi all through the night saidai bacci barawo ya kwasheta. Wuraren 6 bayan tayi sallan safe ta tashi tadauki wayanta tanajin nauyin Aya sosai ko Ya Aysha ma haka but yau dole tai magana da dayansu, wayan Ya Aya tai dialing takira gabaki dayanta tama manta da damuwan Mom, fushin Ya Hamad ke damunta sosai azuciya, ringing daya Aya ta daga tace “Asmeey ke lafiya da sassafe haka?” Dan shiru tayi sai chan tace “uhnnn Ya Aysha uhnnn….uhnn” Ya Aysha tace “me haka kike i’i’na? Tell me” ahankali tana rage murya tace “Ya ake bama miji hakuri idan yayi fushi?” Dan murmushi Ya Aysha tayi tace “laifin me kikama Hamadi me hakuri haryay fushi haka”? Shiru tayi da kyar tace “nidai ki fadamin” kwafa Aysha tayi tace “munafuka idan yayi tsami maji, yanzu dai gayu zakici na bala’i dake daga hankalin namiji kinada kayan bacci na yan iska?” Akunyace ta rufe fuska tace “a’ah” Ya Aysha tace “kashhh natuna ba’a miki akwati ba, tom kawai dai use any clothe kikeda shi mai kyau get dressed tunda baki iya girki danace kimai girki but kimai shagwaba na bala’i mai tada hankali kina shigewa jikinshi makesure kina kamshi sosai, then ki lallashesa da kalamai masu dadi na soyayya da lallabawa kinji” gyadamata kai tayi tace “tom” Ya Aysha tace “kinashan magungunan dana aiko kuwa” gyadamata kai tayi tace “kullum sai Mamie ta bani nasha” tace “tom sai anjima zanje na shirya natafi office” taa katse wayan shiru tayi tunda this morning zasu hospital idan sun dawo da daddare zata bashi hakuri, ta wuce bayi tayi wanka tafito tabuga gayu cikin wani lace black and red tadauki gyale red da takalminta red da jaka red duka kayanta kap Baba yasa an kwashe ko pencil nata ba’a bari agida ba, dan kwalliya tayi a fuska tadauki red lipstick ta shafa tafashe kanta da turare, ko kadan batai kama da mai zuwa hospital ba sai mai zuwa gidan biki riga da skirt din yamata kyau, bude kofan tayi tafito daidai Hamad dake sanye da native milk jumper shima yafito kayan sunmai kyau na bala’i, ganin Asmeey saida ya dakata ya tsaya itama tadan kalleshi saikuma ta sunnar da kanta kasa ahankali tace “ina kwana” da gangan yaki amsawa yawuce yace “let’s go” kuka taji yazo mata tadaure tabisa tana sauka daga stairs Abba da Mamie na kallonsu Hameed yariga yatafi aiki dan yau Monday. Mamie tace “Masha Allah anfito kuyi breakfast dai kafin kutafi” ahankali Asmeey tace “Mamie ya jiki Abba ina kwana” kanta Mamie tashafa tace “naji sauki kinyi kyau abinki je dinning kuyi breakfast” dinning suka wuce harda Hamad tea yazuba a cup yakai baki itama ta hada tea madara tanaci da soyayyen doya da sauce na gizzard da akayi bini bini tana satan kallonsa amman baya kallonta gashi yaci gayu yayi kyau, mikewa yayi yace “meet me a mota” yawuce yafice tabisa da kallo hawaye na taruwan mata amman ta hadiye tagama tamike, Mamie da Abba sukace adawo lpy.

Fitowa tayi, ginin da akeyi takalla yau katako suke sawa asama abin na gudu sosai, horn ya danna mata ganin ta tsaya tana kallon gini masu aikin sai kallonta suke dan basu taba ganinta bama susan akwai tsaleliyar budurwa agidan ba, dasauri tayi wajen motan tabude gaba ta shiga ta zauna kawai taga Hamad yayo kanta baya tayi da sauri gabanta na faduwa suka hada ido ta runtse dan yayi kaman zaiyi kissing nata, handky dinsa yasa kan lips nata yashiga goge red lipstick din tass yagama yakoma yazauna yace “kada ki kara saka this thing idan zaki fita you are married” yakunna motan harya ja taji ciki ciki yace “this is for husband alone adaki not for any huhahu” dan kallonsa tayi ya kirne fuska kaman bashi yayi maganan ba saitai dan murmushi, maganan ya mugun bata dariya, aiko zata sakashi anjima da daddare, sukahau titi kusan 20min sukakai hospital din, kashe motan yayi yaciro wayansa yakira Ya Mustapa taji yace “ok” sannan yakatse yajuyo yakalleta hada idanu sukayi da sauri ta sauke kanta kasa yace “let’s go” fitowa yayi itama tafito tana zagayowa ta side dinsa ya tsareta da idanu daidai tazo dab dashi taga ya mika hannu yakama gyalenta yahade rai yana yafa mata da kyau akunyace ta sunnar da kanta sai yawuce tabishi suka jero sai kallonsu ake, Ya Mustapa ma daya fito reception din yana jiransu kallonsu yadingayi sunyi bala’in kyau, suka shiga ciki akunyace Asmeey ta gaida Ya Mustapa ya amsa yace “let’s go” wani wani abokisa likitan kashi yakai Asmeey Dr ya warware kullum yace “daga hannun mugani” gently kaman mai tsoro tadaga hannun saitaji no more pains saidai tsami da hannun ke mata Dr yace “amman ina ganin ba full karaya bane cus ya warke da wuri da yawa just kuyi Xray to be sure then that is it” Ya Mustapa yace “thank you so much” suka wuce sai dakin xray aka mata hoto sharp sharp akabama Ya Mustapa yaduba hannunta ya hade tass yasake kaima Dr yadawo yasamesu yace “hannun Amarya ya warke” Asmeey taboye fuskanta, anatse Ya Musty yakaita office na Nurses yace “stay here bari na ari mijinki na minti daya okay” gyadamai kai tayi yace “come with me Hamad” He really wants to examine Hamad and rule out yaron baida wani issue akwai maganin dayakeso yabasa inhar yau yasha maganin bai nemi yarinyar nan agado ba toh Hamad needs to see a doctor baida lafiya, idan kuma ya nemeta simply means kaninsa nada lafiya, office dinsa suka shiga fridge Ya Mustapa yabude yadauki ruwa yazo yajawo drawer sa yaciro wani kwali na magani, magani dayane tal yaballo maganin yamikama Hamad maganin da ruwa yace “take kasha”shifa Hamad bayason magani hakan yasa yace “ba abinda kemin ciwo Yaya” rasa abinda Ya Mustapha zaice yasa yace “I look at your neck just now har yanzu is a bit red na yajin nan jini ne awajen u need to take this yayi calming nerves naka down take it karamin magani ne my friend” bayan yasoba ya amsa Ya Musty na kallonshi yajefa abaki yasha ruwa yana tabe baki. Ya Mustapa aransa yace “I just wanna be sure bakada any medical issue Hamad cus lamarinka yasoma bani tsoro, this maganin will start working in the next 10-11hours yake zama active ajiki, around 9 ko 10 nadare kenan yau, so Hamad bazai taba zarganshi ba baiso yaron yadena ganin girmansa” azahiri yace “shikenan kaje gida kuma apply Vaseline awuyan wuce kutafi” ahankali yace “motanka fa” yace “kuje dashi wani aboki na will drop me agida anjima saina dauka” tashi yayi yace “thank you Yaya” yayi kofa yafice wajen Asmeey yaje tana ganinshi tamike tabisa suka fito mota suka shiga suka wuce gida uppan baice mata ba.

Parking yayi zatamai magana harya fice hakan yasa tafito sukai flat suna bude kofa sukaga duka matan yayyinsu agidan sunzo gaida Mamie ganin Hamad da Asmeey sunyi mahaukacin kyau sai suka fara guda Hamad kawai yajuya yafice itakuma Asmeey tashigo tazo gefen Mamie ta zauna Mamie tana karban hannunta tace “barka barka hannu ya warke” ahankali tace “ina yininku Anty” duk suka amsa suna dariya Asmeey takalli Mamie tace “Mamie mezan dafamiki na warke” dariya Mamie tayi da dukansu Mamie tace “angama abinci yanzu karki damu zakiyi abinci wataran” gyadama Mamie kai tayi suka dinga hira Mamie takirata kitchen dudda batada lpy tabata magungunan ta tasha tabata pepper soup tazo dinning tazauna tanaci.
Wuraren 6 matan brothers dinsu duk suka tafi Mamie takoma sama turare tahada takai dakinsu ta kunna sannan tafada wanka tayo alwala sallan magrib tayi sannan tazo tashafa mai ta tsaya gaban kayanta tana neman wanne zatasa dazaisa Ya Hamadi ya hakura tanaso tai kyau sosai yau.
EPISODE 5️⃣0️⃣

Saita rasa wani kayama zatasa cikin duka kayanta, tai shiru chan ta hango wani super dress cikin kayan da Ya Aya tasaya mata, akwai wani red half sexy gown mai mahaukacin kyau dan material din na glittering looks more like a dinner party dress, tana ganin kayan tai murmushi tace “this is it!” Taciro ta ijiye kan gado dazu Anty Asiya ta tayata karasa tsifan kanta so zama tayi tana kallon madubi tawani partitioning gashin nata into two, tanada ribbons dayawa taciro red ta kama gashin, ta makala red clips masu kyau, batamayi komi in her face ba but she looks damn cute already, kayan kwalliyanta taciro tazuba agado tashiga yin makeup, wlh Mom bamata fadowa ranta ta Hamad kawai take, gyara brows nata tayi tashafa smoky eyeshadow a idanunta tayi eye liner jan bakin dazu ta dauka tana tuna meyace kawai tai murmushi tashafa kunya Asmeey she looks so bitch kaman ba itaba lipstick din just changed the game, sallan Isha’i aka Kira hakan yasa ta maida komi wardrobe tasa hijabi tai salla sannan ta linke dadduma ta ijiye
Chapter 84 · 0% Book details