← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 161

Sashe 102

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wani abu taji muryansa yamata uwa ya kwance makullin datasaka na dauriya a zuciyanta, kawai saita fashe mai dawani irin kuka mai sanyi yet piercing heart, Hamad ya lumshe idanu yana jingina kansa jikin kujera ya sauke ijiyan zuciya ahankali, cikin muryan lallashi da tsantsan so yace “I am sorry Baby, kiyafemin….” Cikin murya mai bala’in rauni Asmeey tace “ka…k….ka….tafi…k…a…barni“ kukan is not even making her talk properly, murya chan ciki yace “kinaso nakasa yin abinda nazo yi anan?” Cikin muryan kuka tace “ah’ahh” ahankali cikin murya mara kwari yace “kukan nan yana dagamin hankali sama da komi, I will come back soon and get u kinji”? Gyadamai kai tayi kaman yana gani yace “stop crying now and wipe those tears” bayan hannunta takai kam fuskan ta goge hawayen tass, murya chan kasa Hamad yace “I love you alot!” Wasu fresh hawaye ne suka zubomata kaman zata kurma ihu ita kawai mijinta yadawo she don’t think she can do this rayuwa babu shi, ahankali yasake cewa “Asmeey” ganin he’s seriously disturbed yasa ta gyara muryanta tace “kakai gida?” Murya chan kasa yace “no ina mota ne”? Ahankali cikin tsananin son Hamad tace “kaci abinci toh?” Sanyi sosai Hamad yaji da tambayan yace “no but zanci nakai gida, kinci abinci?” Gyadamai kai tayi tace “eh tareda Abba” shiru yayi saikuma ahankali for the second time yace “I miss u” dan kukan datake rike taji yasake dawo mata muryanta na rawa tace “yaushe zaka dawo?” Allah sarki tabasa tausayi, from the way she talks kasan she couldn’t hold it in any longer Asmeey is missing him kaman zatace wayyo Allah, dan dakewa yayi yace “soon! But kidena kuka kinji, idan wani abu yasameki I will not be able to cope, u mean alot to me Asmeey, when u are not crying i get strength nayi all work sabida nadawo dawuri, but when I am worried sabida ke I will not be productive” gyadamai kai Asmeey tayi, ta share fuskanta ta saita muryanta da kyau tace “wazai kaika gida?” Ahankali yace “dreba dawani security personnel haka kaman escort ne” gyadamai kai tayi, Hamad yace “Ya Hameed yakawo miki Ice cream”? Gyadamai kai tayi tace “eh, nagode” murmushi yayi yace “okay, me kikeso nasa akawo miki gobe”?Ahankali tace “bakomi” gyadamata kai yayi yace “idan gari yawaye gobe i will be busy, zasu kaini police station for wasu formalities da documentation sai kuma bank, jibi shine zanje office nasu and meet with the CEO tareda lawyer na daganan aiki zai fara” gyadamai kai tayi tace “Allah bada sa’a Yaya” “Ameen matar Yaya” dan murmushi tayi, ahankali tace “garin nada kyau?” Gyadamata kai yayi yace “yes yafi Nigeria kyau, u will love it here but akwai sanyi” murya chan kasa tace “yaushe zakamin ho….ton…..k..ka?” Shiru Hamad yayi saikuma yasaki dan murmushi jin matarsa is asking for abinda yayi hating d most wato pictures amman saiyace “zan miki pictures gobe in sha Allah, download Snapchat a wayanki zansa Munir yamiki adding dina” gyadamainkai tayi tace “okay” yasake yayi shiru kafin anatse yace “I have to go now, zan basu wayansu gobe I will call u with my new number” gyadamai kai tayi zuciyanta yasake mata badadi kaman karya tafi saitaji kaman batada lpy, ahankali Hamadi yace “Baby” murya chan kasa tace “uhmm” anatse yace “be eating and stop getting worried everything is going to be okay, we will see soon kinji” gyadamai kai tayi hawaye na cika idanunta murya chan kasa yace “I love you Asmeey” kasa amsawa tayi ta katse wayan dasauri takifa kanta a filo tana kuka saida aka tada salla ta tashi tai asuba tahau gado bacci yayi gaba da ita Mamie ita tashigo dakin tadauki wayan Hameed dazai tafi aiki tabasa.

Wuraren 10 Asmeey ta tashi da mugun zazzabi, wasa wasa Asmeey tafara ciwo rashin lafiya saida Mamie takira Musty yazo magunguna yabata da allura bayan ya duba jikinta, akace kar wanda ya gayama Hamad, rannan all through Hamadi bai iya yakira ba ko bai iya yayi sim din bane oho hakan yakara damunta kuka kawai shine aikinta.

Tunda ya shiga garin they welcome him with flowers masu kyau aka daukesa awata latest tesla mobile car, wani skyscraper apartment aka kaisa lafiyayye 34th floor ne suite dinshi security yace “this is ur suite Sir you can change the password anytime u want” yabude mai kofan kunga gidan Hamad Ya Allah wani lafiyayen apartment ne an gyara komi harda decorating is a one bedroom glass apartment falon nada girma gawasu fararen chair ga mahaukacin fine kitchen ta gefe dayan yanunamai bedroom wani hamsakin gado an ijiye abubuwa da yawa agadon ansa welcome Mr Hamad, saikuma computer room nasa kunga computers da desktop da aka ijiyema Hamad all courtesy of Microsoft ga abinci da dama security yace “make yourself at home Sir, your appointment tommorow is 10AM” Gyadamai kai Hamadi yayi yawuce yatafi Hamad ya tsaya yayi shiru a katon dakin yana kallon duniya gabaki daya ta glasses din yana tunanin inama shi da Asmeey natare.
Wanka yayi yabude akwatinsa ya jera komi a drawer abubuwan Mamie yaciro he’s hungry cake yaci sai yazo yadan ci fruits daya gani awajen all other things bai taba ba shima kasa bacci yayi saidai barawo ya daukesa sabida tunanin Asmeey.

Washe garin nan sai yamma suka dawo dan saida aka budemai komi yadawo gida ya kara gyara suit dazaisa dan gobe ne zaije aslin Microsoft office by 11 na safe.
EPISODE 6️⃣9️⃣
Chapter 102 · 0% Book details