← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 161

Sashe 81

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wanka tayi tafito wani gown tasaka da hijab tai salla saitai shiru kan dadduma tana kallon kayan data ciro saikuma ahankali tace mesa ban tafiba? Fuskan Ya Hamad tagani ahankali kaman wata marainiya ta kwanta kan dadduma tana kuka saikuma ta lallaba ta tashi tacire hijabin tawuce tashiga kwashe kayan nata tana maidawa wardrobe wlh hakanan taji bazata iya tafiya ba bazata iyaba and for the first time in her life saitaji damuwan fushin Ya Hamad over shadow tunanin Mom da rashin kashe kanta da batayiba, tsaf ta maida komi tasa hannu ta tattara kudin tawuce ta ijiye akan desk dinshi, tsintsiya tawuce tadauka tazo zata fara shara danta kwashe maganin beran kawai she now realize bata taba share dakin nan da kanta ba tunda tazo fidan nan kullum Ya Hamad keyi kuka taji yazo mata mai kyau tazauna tayi ta koshi sannan tashiga shara ta share komi ta kwashe ta zuba akwandon shara tazo ta gyara gadon da hannu daya takara zama akasa ahankali tai shiru tana kallon kofa knocking, akayi dasauri ta dago kanta ana bude kofan Hameed tagani rikeda plate na abinci dasauri ta sauke kanta kasa tanajin wani kunyansa, maida kofan yayi yarufe yana kallon yanda ta gyara ko’ina aransa yace “ohh my bro don charm this girl finish Asmeey you are a goner, kitafi mana mugani bayan Hamad yagama siye zuciyanki” zama yayi ahankali akasa kan carpet din ya ijiye abincin agabanta yace “even though nace zan zazzaneki that does not mean zan barki da yunwa, now eat” abincin ta kalla ahankali saikuma ta kalleshi suka hada ido ita yake kallo duk tausayi ma take bashi, hawaye ne suka zubo daga idanunta ahankali tace “I am sorry Ya Hameed I am sorryyyyyy” murmushi yamata yace “kintaba ganin yaya yayi fushi da kanwa I was never angry with u dazu ma u piss me off yasa nace zan zaneki but I will never do that so kike Hamad ya shakeni ke kinsan karfin mijin nan naki kuwa”? Yazaro idanu yace “yafi Antony Joshua wannan wrestler din karfi fa, na tabamai mata ai sunan Hameed sorry, Oya it’s okay eat” bude kofan akayi Faisal yace “is there water here ko no water”
Ya Abdullahi biye dashi yace “I come bearing drinkssssss” coke da Fanta a hannunsa making wani funny gesture dayasa tayi murmushi hawaye na gangaro mata feeling so bad akan abinda tace akansu wai sun tsaneta sai kawai ta fashe da kuka duk sai sukazo suka zauna suka zagayeta Ya Abdullahi yace “it’s okay Asmeey” Faisal yace “ya isa kinji Asaman Gwaggo” one thing she understand is men are so easy going da matane su probably da basu yafemata ba but look at them, ahankali tace “Yaya dan Allah karku gayama Mamie abinda nayi dan Allah” atare dukansu sukasa hannu a lips sukace. “Pinky promise” Coke Ya Abdullahi yabude mata yace “gashi take” amsa tayi ahankali yace “but don’t ever ever ever think of suicide kinji ke musulmace idan kika kara kalan tunanin lokacin ne zamuyi fushi dake sosai right boys” tare sukace right! Ya Abdullahi yace “Hameed karo abincin duk muci tare naga nata duk ya biyamin rai” tashi Hameed yayi yace “shikenan nadawo in charge of kitchen yanzu” yafice chan sai gashi da katon plate na abinci da spoons kawai duk suka zauna wajen sunaci tare tareda ita suna surutu she felt better suka gama suka fice da plates tashi tayi ahankali tayi kofa budewa tayi tafito tana kalle kalle.

Dakin Mamie tabude ahankali ta shiga zaune taga Mamie da farkawanta kenan babu kowa adakin tana ganin Asmeey tace “zo Asmeey naga goshinki Subhanallahi dünya kumbura” wani iri Asmeey taji how could she even blame this woman meya sameta dazu kawai dawani gudu tayi wajen Mamie kawai ta rungume Mamie tahau kuka tace “I am sorry Mamie I am sorry”
Dagota Mamie tayi tace “common I am fine ya isa dena kukan haka jibi udanunki tuntuni kike kuka ko? Bagani lafiya ta kalau ba komi yawuce ya isa”
Mamie ta sharemata idanu tana murmushi, Abba ne yashigo yace “ahh kin tashi akwai abinda ke miki ciwo”? Girgizamai kai Mamie tace “babu abinda ke damuna Alhamdulillah” tashi Asmeey tayi tafice danta basu waje takoma dakinta saita kwanta agado tai shiru tana kallon kujera da desk din Ya Hamad tarasa yanda zatayi taji dadi she miss him badly.
EPISODE 4️⃣7️⃣

Komawa hotel nasu Mom tayi kawai tai parking tana maida numfashi sabida kalan gudun datayi ahanya gabanta sai fadi yake tadaura hannunta saman kirji tanajin bugin zuciyanta da kyar tadawo daidai, bata tabaji gabanta ya fadi akan wani sama da Fawaz, shi ne wanda shi tasan soyayya ne but yau dataga idanun Hamad saitaji zuciyanta ya buga rasss and that is a very bad feeling for her guts, duk wanda zata kalla gabanta yafadi means bazata taba samun nasara akansa ba, zata wahala saisa ga Fawaz nan haryau fama take, this is just gut nata da believe, mesa tai feeling towards Hamad? Does that mean bazata taba iyacin galaba akan Jobless mental boy din nan ba? Does that mean bazata iya raba aurensu ba ko mene? Noo tayaya wannan yaron zai iya shan karfinta waye shi? Shiru tayi tana tunani daban daban sai kuma ta dafa kanta as long as bata bama Fawaz Asmeey ba batada zaman lafiya da kwanciyan hankali the only way she can escape that is idan yarinyar ta mutu dole yahakura Asmeey should better take maganin nan let her end this problem quick but yanzu mezata gayama Fawax? Tacemai sunyi tafiya da Asmeey wani gari biki ko mene? Tasake shiruuu tana tunani wayanta ta daga takira Fawaz kaman jira yake ya amsa yace “Yaya kin daukomin matana?” Rudewa tayi but saita danne sabida karya gane tace “sunyi tafiya da ita wai zuwa kaduna!” “Dan mecin babar sa matana zai dauka yaje honeymoon da ita wani gari”? Dasauri Mom tace “no ba shine yayi tafiyan da ita ba, Maman su tai tafiya da ita zuwa Abuja bikin diyar sister ta but next week zasu dawo suna dawowa I will get her” Fawaz yayi shiruuu Mim tace “hello kaji” wayan kawai ya katse Mom tace “ohh ni Salima!”

Har dare Asmeey bataga Hamad gabaki daya bama yana gidan baya gidan oho bata sani ba ta bala’in damu bata taba sanin zata damu haka ba ya hakura da ita ne? Ko yahakura da aurensu ne tunda ita tace batason auren tagaji? Sai kawai taji deep down bataso aurensu yakare lips dinta ta shafa tana tuna yanda just jiyan in the morning he kissed her kafin su fita saitai shiru takai hannunta tadaura akan lips dinta hawaye na gangarowa idanunta, she knows maganganun ta na dazu she sounded so ungreatful, itama mema yakaita tace Mamie ne tafara pushing Mom? Maganan kwata kwata bai dace ba cus Mamie did that because of her, Mamie was even crying sabida tausayinta why did she said that? Maganan sounds kaman batason Mamie koma menene bai kamata tace ba’a sonta an barta ita kadaiba, dudda tana cikin azaba she remember yanda Hamad hugged her ya shafi yajin helped her she sounded so mean incensitibe Naf rashin kunya yaushe tazama haka? When did she become this? Hawaye ne yashiga zubo mata sai juye juye take takada bacci takasa tashi tamayi wankan dare.
Chapter 81 · 0% Book details