Sashe 26
Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tana bude kofa da saida gidan kap ya amsa. “Ihuuuuuuuu zatai kisan kai jama’a ataimaka zatai kissan kai!” Tundaga su Mamie da Ammi dake backyard dasu Ya Mustapa da Hamad dasu Baba dake masallaci harda Ustaz da su Ya Hameed saida aka fito da gudu ana yowa flat din jin ihun Gwaggo, Mom ta dauke kai daga kallon Gwaggo dake ihu babu ko dar a zuciyanta ta shake wuyan rigan Asmeey dake kyarma tace “I said apologize now!” Ta daka mata tsawa ahankali cikin muryan ban tausayi jikinta na rawa sosai tace “so….so…sorry” “Sorry Wa ne”? Mom ta sake dauketa da mari a same kumatu for the second time mercilessly, Gwaggo tai ihu ta taho tana ture Mom tace “wai ke yarnan bataki bace ko yar riko ce?” Mom dako gezau batayi ba da tureta da Gwaggo keyi tana rike da Asmeey tace “speak!” Bakinta na wani kalan rawa tace “so……sorry Ya Ramla” daidai lokacin su Ya Mustapa na shigowa falon Ya Hamad biyeda shi, awani kalan zuciye Mom ta hankada Asmeey saitin center table dake tsakiyan falon da mugun karfi sai kasa tamugun buge da center table din a gefen cikinta daidai kan idon Baba dasu Mama da kowa hadda matan su Ya Mustapa, Mom tajuya fuuuu tawuce stairs Baba kawai yayi mutuwan tsaye yakasa magana ganin yanda Mom ta buga yarsa da center table mugun buguwa ma, Gwaggo ganin yanda yarta sandarewa tayi ta kankame awajen cike da mamaki kowa na falon was freeze har ita Mama yar fadan Mom, Mamie ce ta iya motsi cikin kowa takarasa tsakiyan dakin ta duka tasa hannu ta dago Asmeey data kasa motsi idanunta har lokacin duhu duhun mari suke mata, ahankali Mamie tace “Ma’u sannu tashi, kinji ciwo”? Jikinta na wani irin kyarma totally destabilize ga lallen da aka mata ya dame duka har center table yabaci shima da lallin da sauri ta girgizama Mamie kai har lokacin bata gani da kyau ga kunya yagama kasheta ga jikinta rawa kawai yake, tajuyo tana kokarin neman Mom dabata gani a falon ba kowa na kallonta, ahankali Mamie tace “Doctor zoka dubata” dasauri Asmeey ta kalli Mamie jikinta na rawa yana kyarma amman takakalo murmushi muryanta ciki ciki yayi rauni tace “babu abinda kemin ciwo ai ban buge ba” dasauri Yusra tace “duk Ya Ramla taja Mom ta daketa and she lied cus Ya Hamad ai bata cemiki wawuya ba kene kika kirata wawiya because of ice cream” ran Ammi taji yabaci tashigo tsakar falon tace “are you the reason aka daketa haka? Ramla do you even love your sister? Kalli kumatunta, kalli lallinta, kalli yanda jikinta ke bari, bakida imani ne Ramla ke ba mai marba Asmeey ice cream bane bakene babba ba? Wace kalan muguwa ce ke”? Tadaga hannu zata daketa Abba yace “dakata! Karki daketa!Yarane ba’a raba yara da irin kananun fada haka musamman wajen rabo amata afuwa, Husna” da sauri Asmeey ta kalli Abba idanunta sunyi firfirr ba hawaye tace “uhmmm na’am Abba” magana Abba zaiyi but sai yayi shiruuu ganin yanayin yarinyar yace “kaita ta wanke hannayenta da kafafun Maman Doctor, Nana ku gyara inda yabaci da lallen” yunkurin dagata Mamie tayi tace “tashi muje” Asmeey takasa tashi bakinta zaiyi magana sai kawai ta kasa sai hawaye yataru a idanunta ta juyar da fuskanta irin na neman inda zata saka kanta dinnan Mamie ahankali tace “zo Asmeey come” Mamie zata kamata Asmeey zata fita daga jikinta takasa da sauri ta shige jikin Mamie duk yanda takeso ta daure ta danne takasa tafashe da kuka sosai jikin Mamie mara kara sai shesheka da jikinta dake motsi irin kukan nan mai taba zuciya tana huci mai bala’in zafi a jikin Mamie, Baba ya yunkura zai wuce sama Abba yarikemai hannu alamun no dan yaga yanda Baba ya zuciya kuma babu kyau hukunci acikin fushi hakan yasa ya tsaya, Munir yawuce ahankali wajen ya tsugunna kusa da Mamie da Asmeey ke jikinta yadaga hannunsa yadaura saman bayan Asmeey yayi shiruu idanunsa sunyi jazur, ahankali Hamad yajuya yafice daga falon yarufo kofa, Gwaggo da sai alokacin tadawo daidai tace “toh wlh wlh tunda dai abinda akema yarnan agidan nan kenan zan tattarata natafi da ita, kuma dagayau tabar shashin nan, idan uwarta ta isa tazo inda nake ta tabata, bantaba ganin muguwa Uwa irin mahaifiyarta ba, wlh kekuma sarai ai kinsan halin uwarta koda tamiki laifi ai sai ki rufamata asiri ba yar uwarki bace? Kuma ai kina sane ai haushi takeji ansata tayi lalli alhalin tahana ba dole ta dirketa ba, ga lallin nan tasa yabaci hankalinta ya kwanta, Mara Imani da idanunta kaman na mutan da, saisa Allah yahanata tsayi kaman in kifeta da kwando, muguwa dunkulen magi kawia ai gajeren mutum akwai bakin hali” Gwaggo na fadin haka ta karaso takama hannun Asmeey dake jikin Mamie tace “tashi muje” fitoda ita daga jikinta Mamie tayi tace “tashi kuje Asmeey” idanunta akasa taki kallon kowa ta kasa tashi, rai abace Baba yace “badake ake magana ba tashi” ahankali ta tashi da dauriya da kyar, Gwaggo tariketa tajawota aka mammatsa suka taho Ya Mustapa yabi yanda ke tafiya da kallo dakuma gefen cikinta suka fice sai kawai Mamie itama tabisu abaya haka sauran matayen, Mama kuma tawuce sama abinta wajen Mom danta bata hakuri Ya Mustapa yajuya yafito kowa ma yafito. Flat din su Mamie Gwaggo tashiga da ita har lokacin fada take sosai dakin dake kasa tawuce dan ita duk dakunan kasa nakowani flat nata ne cus duk inda taga dama take kwana tabude tashiga tace “wuce kije ki wanke hannunki” wucewa tayi ahankali ta shiga bayin ta maida kofan tarufe takarasa wajen wash hand basin tadaga hannuwanta da akama lalle duk sun gwalje both baki da jan tai shiru sai kawai hawaye suka sauko daga idanunta tabude tap din ta wanke hannayen tasss and lallin yayi mata bala’in kyau inda ta gwalje ne yayi wani iri, lallin yayi dan ja, Kuka takeso tayi but saita hana kanta gabanta har lokacin faduwa yake, Mom sai fadomata take arai bazata taba kwana anan ba sabida kar ran Mom yabaci zata bari Gwaggo tai bacci saita tafi wanke, kafafunta tayi suma tass ta dauro alwala dan batai salla ba ta kalli kumatunta da sunyi jaa sosai abunka da fara ko yaya aka mareta kalan fatar fuskanta saiya chanza towel na bayin tasa ta tsane fuskanta sannan tabude bayin tafito Mamie tagani tsaye kusa da bayin tace “alwala kikayi?” Dasauri ta gyadama Mamie kai tana kakalo murmushi tace “eh banyi salla ba shizanyi yanzu” Mamie na kallonta tace “babu abinda ke miki ciwo?” Gyadama Mamie kai tayi Gwaggo tace “wannan ai ko zata mutu bazata fadi ba uwarsu yanda kikasan ta tsafesu ni zoki salla muje falo muci abincin dare yunwa nakeji”dan takowa Mamie tayi dab da ita gently takai hannunta ta daura saman kumatunta dayayi ja tana kallon idanunta, wlh tunda Mom ta mareta koda yanzu tai alwala tasa ruwa a fuskanta bataji sanyin dataji kaman sanyin dataji yanzu da Mamie ta daura hannunta kan kuncinta ba sai jikinta yayi sanyi sai taji jikinta ta ciki yadaina radadi cikin murya mai sanyi dakuma so Mamie tace “ya isa! Calm down zanma Mamanki magana dakaina kinji, next time koma menene karkima nagaba dake rashin kunya, kinfi kowa sanin mahaifiyarki macece mai bama yaranta tarbiya yanda yakamata bata yarda danta ko yarta ya taka na gabansa ba, next time respect Ramla kinji no matter what don’t talk back at her just like yanda Mom bazata bar su Yusra ko su Nana sumiki rashin kunya ba kema bazataso kima na gabanki ba, but ya isa okay” gyadama Mamie kai tayi idanunta na cicciko da hawaye, ahankali Mamie takai hannunta gefen cikinta tace “wajen namiki ciwo nasa Doctor yakawo miki magani?”Girgizamata kai tayi tace “a’a bayayi” Mamie tace “to yi salla abinki” Gwaggo taja tsaki tace “wlh takara taba yarnan tagani yo ita ubanwa naga tana girmamawa? Girmamani take? Mata sai girman kai jitake tafi kowa sabida tayi boko, bokon da agidan d’ana tayi kuma da kudinsa banza kai shashasha muzuba ni da ita zan nuna mata matsayinta” Mamie dai tawuce tafita Asmeey ta dauki hijabin datagani kan gadon wajen tasaka tai salla magrib da isha’i ma da akayi Gwaggo da tunda tafara salla take kallonta tace “kiwa Allah Asama kitashi kicire hijabin nan muje muci abinci cikina sai kuka yake” tashi tayi ta cire hijabin tawarware mayafinta tasa aka yadan sauko mata shoulder Gwaggo tai gaba ta biyota abaya su Ya Mustapa duk suna falon Ball ma suke kallo a tv falon da Ya Abdallah da Ya Faisal da matarsa ke basa abinci, shi kadaine be ciba sai Ya Hameed shima.