← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 161

Sashe 22

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi duka yaran sukayi bata tashi ba Ramla tace “tashi muje mu gaida su Kawu” ahankali ta tashi suka wuce wajen motansu, wani magidanci na mai kama da Abba na Kano sosai tareda wata mata da yara mata, Matar tace “ana kitso ne Asmeey ba’a gama ba” dasauri Asmeey tace “eh Mama” ta rungume “Nana da Baby tace “Nana, Babyyyy” suma suka rungumeta Nana is 15, Baby kuma 12 sai sauran yaran Maza ne guda hudu, daidai nan Kawu ya gama magana da masu gadi yazo wajen yaran duka suka gaidasa idanunsa nakan Asmeey yace “meya sameki a fuska Asma’u”kafin tai magana Yusra tace “faduwa tayi Kawu” ahankali yace “sannu bakiji wani ciwon bako” gyadamai kai tayi tayi murmushi still ya tsareta da idanu dan kaman mari daidai Baba na fitowa daga flat, Mom da Ammi kuma suna zuwa daga backyard, wani kallo Mom tama Asmeey hakan yasa tajuya ahankali tawuce takoma wajen kitso, Baba yayi hugging dan uwansa cikeda farin ciki suka shiga gaisawa while masu gadi na kai kayansu side nasu, Asmeey takoma wajen kitso tazauna aka cigaba tana kallon yanda kowa ke murna, su Nana suka taho wajen basuyi lalle ba suma Ramla tace “kuje kuhuta ku chanza kaya kar lallen yabata wannan sai kuzo amuku” wucewa sukayi dan chanza kayan. Suna chanza kaya suka dawo, suna cikin kitson Munir yazo wajen kaman bacci ma yayi dan idanunsa yayi ja bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey ana mata kitso ba dudda yana ganin fuskanta yasan aikin Mom ne yazo wajen yadan harari Nana dake kallonshi yace “ni tsaran wasankine kike kallona” kallon Ramla Asmeey tayi Ramla ma takalli Asmeey suka wani kwashe da dariya bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey tayi dariya ba, Ramla tace “sannu Ya Munir itakuma Nana jibi yanda tawani sunnar dakai kaman irin Ya Mustapa asalin Babban yayanmu namata magana” hararan Ya Ramla yayi yasake tamke fuska sosai shi adole babba sannan yakalli Asmeey yace “Mom is calling you” yajuya abinsa, faduwa gaban Asmeey yayi sosai ta tashi da rabin gashi akitse tawuce Nana tadan saci kallon Munir da tun tana yar karama take sonshi Ramla tace “dalla kidena tsoronshi” murmushi tayi tace “cikamin ido yake Ya Ramla” baki Ramla tabude tace “Munir din ahhh babban magana” shigowa falon sukayi ga Baba da Kawu akan carpet sunashan shayi dake kamshi sosai Baba dake kallon Asmeey tun shigowanta yace “ina zaki da gashi haka ba kallabi” da sauri ta taba kan tace “Mom ke kirana yanzu na manta da kallabin wajen kitso ne” gyadamata kai Baba ta wuce sama afalon Mom taga Mama, Mom na shiri da Mama sosai da Kawu but Mamie kano ne dai basu cika shiri ba dakuma Abba suma bawai fada suke ba kawai dai haka suke sunfi shiri da Ammi su, Mama dakecin samosa tace “Hajiya Salima I trust you dan Allah Asmeey ma ki sama mata gangariyan miji gaskiya dan matar manya ce yarinyar nan ga kyau ga diri dudda naga sai karewa take maybe zullumin zuwa law school ne” akunyace Asmeey tadan sauke fuskanta kasa, Mom tahade fuska tace “zonan” rawa hannayenta suka fara har Mama saida ta lura amman taja baki tai shiru kafin ta shiga black book din Mom, wucewa Asmeey tayi gaban Mamanta wani kallo Mom tamata tace “wuce ki daukomin kayan dana dinkama Maman ki da wanda na dinka miki dasu Nana” wucewa tayi bedroom din Mom, Mama tace “ohh baki gajiya Hajiya Salima! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah kara girma da daraja” kawo kayan Asmeey tayi bakin Mama har kunne Mom nada kudi so manyan exclusive atampopi ne Mama tace “Allah dai yaja zamaninki wlh Babansu Aya shi kanshi yasan yayi dace saisa har yau har gobe kece yar gaban goshi, Aya zatazo namata godiya ko, mijinta ya fitar da zakka dubu dari biyar ta aikamin wlh” murmushi Mom tayi na isa irin abin nan takeso Asmeey ta kalli Mom tace “Mom natafi”? Mom tace “yaron nan has been calling you go and talk to him kafin ki koma” wani iri Asmeey taji, badaman yakira bata dagaba saiya kira Mom, wucewa tayi tafita daga dakin, dakinsu ta wuce ta zauna kan gadonsu tadauki wayan taga 5miss calls nashi, instead of takirashi back sai kawai ta kwanta ahankali kan gadon tarike wayan a hannu within 2mins bacci mai dadi ya kwasheta cus tun asuba data tashi bata koma bacci ba tana wajen Mom, kusan 1hr tana bacci sannan wayanta ya shiga ringing firgigit tabude idanu tana tashi zaune tana mamakin yanda bacci ya saceta haka, daukan wayan tayi takai kunnenta ahankali tace “hello” “Wifey how are you”? Abu taji ya tokare mata wuya she hates d name sosai, da kyar tace “fine” yana murmushi da tana iyaji a muryansa yace “sorry banzo ba har yau ban dawo garin ba sai yau, ya shirye shiryen salla ni da Mommy na zamuzo washegarin salla” gyadamai kai tayi batace komiba cus bama tasan mezata ce ba, matse murya yayi yace “I can’t wait to see you my wife Asma’u” wani iri jikin Asmeey yamata ta runtse idanu, Fawaz yace “kullum sainaga fuskanki a bacci, I don’t know why I love you this much, me kikamin”? Kin magana tayi Fawaz yace “wai yaushe zaki dainajin kunyan mijinki eh? Relax and talk to me babu abinda yakai muryanki dadi arayuwana”? Murya chan kasa mai dari dari tace “kitso akemin zan koma akarasa” dan shiru yayi he feels kaman bata sonshi but he don’t care, ahankali yace “okay kije toh zan kira anjima take care” dasauri ta katse wayan ta ijiye wayan akan gado tanemi another blue veil karamin veil tadaura saman kanta sannan tafito Ammi tagani tana fitowa daga dakinta kaman itama ta hauro tai salla ne ganin kanta bangare daya himm bangare daya a kwance tace “meya faru ba’a gama miki kitso ba har yanzu Asmeey kowa yayi nashi kitson agidan nan?”ahankali tace “Ammi bacci ne ya kwasheni a daki” hararanta Ammi tayi tace “wuce ni kafin in mangareki awajen nan yarinya kaman mage”wucewa tayi tafita sauka kasa Ammi biyeda ita tabude kofa tafice Baba tagani da kanshi yana bude gate murmushi yalwace a fuskanshi, motan su Abba na danno kai dan nasu ne agaba hakanan gaban Asmeey yawani fadi shigowan motan zaro idanu tayi tace “Ammi Gwaggo ta iso”? Daidai nan yaran wajen lalle harda su Ramla da Munir dake wajen dasu Nana suka kwaso da gudu suna ihun. “Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyoooo” Kashe motan akayi Abba ne yafara fitowa yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunsa atare duka yaran gidan sukai kan Abba. “Abba oyoyoooo!” Abba yabude hannunshi dukan uban yaran ya rungumesu, Mamie ma tafito ta zagayo ta dayan bangaren yaran suka saki Abba ta zago ta gaban motan suka rungumeta, Ammi dahar ta wuce tajuyo takalli Asmeey dake tsaye tace “wuce muje kiyi gaisuwa” hakanan kawai saitaji tabajin kunya da nauyi tadajan gyalenta gaba, tawuce wajen Mamie data tsareta da idanu, sai kawai Asmeey taji tanajin kunyan su Mamie suga fuskanta dan jawo gyalenta gaba tayi tadan tsaya gaban Mamie, Mamie dake kallonta tasaki yaran tace “Ma’u kene haka zonan” batai wata wata ba dan tana bala’in son Mamie taje ta rungume Mamie tace “Mamiee” murmushi sosai Mamie tayi tace “Asmeey” Ramla ma tazo aguje dasu Nana suka rungume Mamie, Baba yabudema Gwaggo mota yakamota tafito dan kafafun sunyi tsami tace “Muhammadu Sani wai Bauchin nan kullum kara nisa yake Ne?” Yaran najin muryan Gwaggo duk suka arto, Gwaggo Gwaggo sun kusa kada Gwaggo, Baba yamusu tsawa. “wai bazaku bi Gwaggo ahankali ba” saukowa kowa yayi su Ya Mustapa da matayensu duk sai gaisawa ake, Mom da Mama suka fito atare sai gaishe gaishe ake everyone looks so happy har lokacin Asmeey na tsaye kusada Mamie, Baba yashiga bin ko’ina da kallo Abba dake lura da shi yace “me kake nema Muhammad” Baba dake kalle kalle yace “Yaya naga tundaga kan Mustapha har Hassan nagani amman banga Hussaini ba, ina Hamadi”? Kawu yace “ai wannan ka sanshi” girgixakai kawai Abba yayi yace “yana mota” anatse Baba yawuce wajen motan kai tsaye yabude kofan gaba yace “Hussaini har yanzu dai halin nan na nan to sauko, fito” kowa na compound din juyowa yayi jin maganan da Baba yayi, ahankali Asmeey dake tsaye kusada Mamie gaban motan da Baba yabude tajuyo daidai Hamad na fitowa daga motan kanshi akasa cike da bala’in natsuwa sai kawai gently akuma natse yaduka ahankali gaban Baba yace “ina yini Baba!” Dawani irin sauri Baba yataroshi yace “tashi tashi Son ya gajiyan hanya yakuma karfin jiki? Aikin ya warke ko”? Gyadama Baba kai yayi still kanshi na ahaka yace “Kawu ina wuni” Kawu na murmushi yace “Hamadi lpy lau ya karfin jiki Allah dai ya karamana lafiya gabaki daya” dan shafa kanshi yayi kadan saikuma yatako kadan zuwa dan nesa da Mom dake tsaye tareda Ammi da Mama sai kawai ya duka yace “Mommy ina yininku” bayabo ba fallasa Mom tace “barka da zuwa Hamad” Ammi tace “tashi tashi kaida bakada lpy mike” mikewa tsaye yayi sai yadan waiga, Gwaggo dake kallonshi tace “yanzu zai nemi Maman shi” aiko aka kwashe da dariya harda Mamie sai kawai ya sauke kanshi akunyace, Baba yace “kumuje kumuje bismillah” Yaran suka shiga gaida yayyinsu, Asmeey takalli Hameed tace “ina yini Yaya?” “Wat happen to your face?”Juyowa Mom tayi ta kalli Hameed sannan ta kadakai tai wucewarta Asmeey tace “faduwa nayi” dan hararanta yayi tasauke kai dasauri tajuya zata gaida Ya Hamad yawuce abinshi ko kallon inda take baiyiba instead of yaje flat dinsu Baba sai kawai yawuce flat din dinsu m Ya Mustapa ya kalleshi saikuma ya kyaleshi, dan satan kallonshi Asmeey tayi Ramla taja hannunta tace “muje ciki” suka wuce flat nasu. Duk zama akayi Baba yakalli kowa na falon ganin babu Hamad yasa yace “ina Hamad”? Ya Faisal yace “yawuce chan side din” hada ido Asmeey tayi da Mom data ℳ𝒶𝓉𝒶𝓇 wani mugun kallo mikewa tayi da sauri zata fice Baba yace “ina zaki?” Ahankali tace “zanje akarasamin kitso ne” Baba yace “je flat din Abban ku ki kiramin Yayanki Hamad kafin kije wajen kitson” gyadama Baba kai tayi tajuya tawuce hakanan taji gabanta ya fadi, duk babban salla anan Bauchi sukeyi every year tana ganinshi sau
Chapter 22 · 0% Book details