← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 161

Sashe 64

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Duk dakin sai yayi badadi babushi aciki ganin Ya Hameed dazu yasa kawai sai yanzu tafito sanye da hijabi Mamie tasa mata abinci kadan taci Ya Musty yashigo gidan sanye da lab coat yace “Asmeey” akunyace tace “ina yini Yaya” waje yasamu yana zama yace “ya hannun lemme take a look” hannun ya karba ya dudduba yace “kina healing fast gaskiya kinashan maganinki”? Ahankali tace “yau ban sha ba ban gansa ba” Yaya yace “maybe a manta dashi a Bauchi ina mijinki”? Akunyace ta sunnar dakai tace “bayanan” sai ta juya zata koma sama Ya Mustapa yace “zauna kici abincin ki Mamie hala taje salla ko?” Gyadamai kai tayi yace “Gwaggo kuma ya tafi gidan mutane ko” gyadamai kai tayi tacd “this old woman I know by now those people are regretting abinda yasa suka bama yarsu sunan Gwaggo” “Nakawo maka abinci Yaya”? Girgiza mata kai yayi yana bata ledan hannunsa da surutu yasa ya manta yace “this is for u” bude ledan tayi taga ice cream ne na cold stone murmushi tayi tace “thank you Yaya” Ya Mustapa yace “nazo naga Mamie ne yanzu zan koma hospital zanyi har night yau saisa nazo na ganta kafin tace bata ganni yau gabaki daya ba” daidai nan Mamie tazo shima Hameed yashigo rikeda wara a hannu yamikama Asmeey yace “take Zee loves it maybe kema haka shine nasayo miki” dan murmushi tayi akunyace tace “thank you Yaya”bakaramin dadin hakan Mamie taji ba yanda suke sonta, Asmeey ta tashi saita shiga kitchen freezer su tabude tasaka ice cream din waran kuma tadauki wani small kula tasa aciki Mamie tace “me kikeyi a kitchen” fitowa tayi Mamie tace “ina abun naki bazakici ba?” Da zuciya daya tace “sai Ya Hamadi yadawo na nunamai tukunna” ba Mamie kadai ba har Ya Mustapa da Hameed saida suka kalleta wlh sai sukaji ta burgesu sosai, Ya Mustapa was seriously impress but duk sai basu nuna komi ba kartaji kunya, Mamie tace “a fridge kikasa ice cream din”? Gyadamai Mamie kai tayi tace “eh, warana kuma a kula” dan murmushi Mamie tayi tace “yayi kyau” suka cigaba da hira, Mamie last last saida tasa Ya Mustapa cin abinci da Hameed sai kallonsu Asmeey take Mamie na son yaranta sosai sosai, hira suke Ya Mustapa na bata labari kafin around 3 yace “bari naje naga masu aikin nan na haka foundation sunce yau zasusa, Hameed gobe sai office ko?” Gyadamai kai yayi yace “yes Yaya hutu ya kare” Ya Mustapa yace “okay sai anjiman ku” yatafi shikuma Ya Hameed yakira Zee wayan yabama Asmeey yace “ga Zee” ahankali ta amsa Zee tace “Asmeey” dan zaro idanu Asmeey tayi akunyace tace “na’am ina wuni” Mamie ta harari Hameed dake wani murmushi tawuce kitchen abinta, Zee tace “congratulations on your wedding Allah sanya alheri” sunnar dakai Asmeey tayi takasa amsawa, Zee tace “in sha Allah zamu hadu soon nace ma Ya Hameed yabani number ki” ahankali Asmeey tace “nima zan karbi number ki” Zee tace “shikenan sai munyi waya bye” mikama Hameed wayan Asmeey tayi yatashi daga dinning din yawuce sama Mamie tazo suka zauna Mamie na bata labari daban daban.

Har akai la’asar taje tayi tasake dawowa falon suna hira da Mamie karan bude gate taji dasauri takalli window Mamie ta tsare yarinyar da idanu Asmeey na son Hamad fa, takosa yadawo, tashi Mamie tayi tace “bari na dauko wayana na barsa a kitchen” Mamie na wucewa kitchen dasauri Asmeey ta tashi tayi wajen window ta leka, Ya Hamad ta hango kan machine yana parking ga kwalin indomie ta gabansa dawani leda, wani cute smile tasaki tana kallon yanda yasa black shade a idanunshi, tuntuni Mamie ke kallonta but kawai saitadanyi motsi dayasa takoma kujera da sauri ta zauna kaman bata taba tashi ba Mamie kuma tafito rike da wayan tana dannawa daidai an taba door din da sallama Hamad yashigo rike da kwalin indomie dawata yar leda a hannunsa ganin Mamie afalo sai yaji wani irin kunya but ya daure da kyar yakarasa falon wajen Mamie ahankali yace “Mamie” sai ya ijiye ledan da kwalin kusada ita yace “take” zai wuce da sauri Mamie tace “kabama matarka mana Hamadi gidan nan babu mai cin indomie sai ita ai ko Asmeey” akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa shikuma Hamad yayi sama yaki juyowa Mamie tace “yau naga munafukan yara” takalli Asmeey tace “dau abubuwan ki kiduba” akunyace Asmeey tadauki ledan ta duba kwalin conflex ne, sai roban eclairs sweet, sai short bread biscuits guda 5, da chocolate guda biyu, Mamie tace “I said it naki ne yake wani bani” akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa Hameed ya sauko yana zuwa wajen yace “waye mai abun dadi haka”? Yakai hannu zai dauki chocholate Mamie ta bugi hannunsa tace “mijinta ya sayo mata abu kadauka” dasauri yace “Hamadi yadawo ne Mamie?” Eh Mamie tafadi tace “tayata kai kwalin indomie nan store Hameed” dauka yayi yana mamakin Hamadi aranshi yawuce kitchen, Mamie takalleta tace “kekuma kwashe abubuwan ki kitafi daki mijinki yadawo” gyadama Mamie kai tayi ta maida komi jakan, Hameed yafito daga kitchen yafita itakuma tawuce kitchen ice cream dinta ta dauko da kulan wata tarike duka tawuce sama Mamie na kallonta ahankali tace “Alhamdulillah Alhamdulilah Ya Allah” ahankali tabude kofansu dago kansa Hamadi yayi yakalleta maida kofan tayi tarufe ya kalleta da abubuwan data kwaso tana support da karyayyen hannunta ahankali kaman mai tsoro tadanzo kusa dashi murya kan kasa tace “thank you Ya Hamadi” dauke Kai yayi daga kallonta sabida cute smile din datayi komawa gado tayi ta ijiye ledan ta sai tadawo wajen yasake juyowa ya kalleta ice cream din ta ijiye agabansa da kulan waran tabude tanuna waran murya kasa kasa tace “Ya Hameed yabani wara dazu, Ya Doctor ya kawomin Ice cream” kallon komi yayi saikuma ya kalleta idanunta na kasa har lokacin ahankali yace “mesa bakici ba”? Ahankali tace “saina nuna maka” shiruu yayi yana kallonta maganan really melt his heart yace “to kije kici” gyadamai kai tayi tace “tom” saita juya saikuma ta tsaya batare data juyoba kaman maijin nauyin magana tace “zakasha ice cream?”Ahankali yace “I don’t take ice cream” murya kasa kasa tace “wara fa?” “I don’t like it” gyadamai kai tayi tawuce ta zauna akan gado tabude waran da ice cream dakuma chocolate tashiga kakkarya chocolates din tasa a ice cream din Hamad yadan juyo ya kalleta she was eating it and smiling tana kara kallon ledan chocholate din daya mata dadi, she looks so happy da he got carried away looking at her, bata iya cinye waran ba but ice cream din ta shanye ta tashi taja drawer gefen gadon tazuba komi awajen ta ijiye conflex tadauki ledan da roban ice cream zatai kofa yace “Husnah” dasauri tajuyo suka hada ido yace “I will take everything out jeki zauna” ahankali ta ijiye komi saitaje ta zauna saikuma tayi shiru saita kwanta kawai tanata kallonshi he’s always working desktop computer kome yakeyi oho, tashi yayi dasauri tadauke idanunta daga kallonsa daukan abubuwan yayi yafita dasu Hameed yagani afalo yahade fuska Hameed yace “indomie and chocolate buyer” kitchen yawuce baicemai komi ba yana fitowa yaga Hameed tsaye yarike waist, Hameed yace “na shigo naga kanata murzama yar mutane hannu Hamad” juyawa Hamad yayi yakoma kitchen dayake Mamie kadaine yace “Mamieee Hameed” juyowa Mamie tayi taga Hameed dake jiran Hamad gaban kitchen tace “wlh Hameed zankira Abban ku nakai karanka ha’a” dariya Hameed yayi yace “shikenan nayi shiru Mamie” Mamie tace “tafi abinka” wucewa Hamad yayi Hameed kaman zaiyi kuka yace “Mamie dan Allah nima kumin aure wlh kaman inta ihu nakeji, yanzu danaga yanda Hamadi keji da matarsa kaman inta kuka, i am missing Mamieeeeee, aure Rahama ne just one day but my brother is glowingggg!” Mamie ta girgiza kai tace “Allah ya shirya kai Hameed!.”
EPISODE 3️⃣3️⃣
Chapter 64 · 0% Book details