← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 161

Sashe 4

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE 2️⃣ Wuraren 3 yashiga bude idanunshi asanyaye, alluran ko magungunan ne da Ya Mustapa ya bashi really made him sleep, gently yatashi zaune yazare drip daga hannunshi daya kare, yadan shafa fuskanshi sannan yasauke fararen tsaftatattun kafafunshi akasa yamike tsaye ahankali, he’s tall kusan yamafi Ya Mustapa Dr tsayi kawai manyanta shi Dr zai nunamai dakuma shekaru da teba haka dan shi baida teba kuma baida rama, wani irin full fitted body gareshi, bayinsu yashiga brush yasakeyi cus bayajin dadin bakinshi at all, fitowa yayi ya chanza singlet na jikinshi yasaka wani yadauki wani black t-shirt yana kokarin sawa aka shigo dakin dasauri yakalli kofa Mamie ce hakan yasa yayi sauri yakarasa saka rigan yadan kalli Mami data tsaya saikuma ya sauke kanshi kasa murya chan kasa yace “Mamie” tahowa cikin dakin Mami tayi zuwa inda yake ta tsaya dab dashi hannunta tadaga ahankali takai fuskanshi ta shafa gefen kuncinshi tace “yajikin? Meke maka ciwo yanzu eh?” Murya chan kasa yace “bakomi” shiru Mamie tayi tana kallonshi sannan tace “salla zakayi bari na shimfida maka dadduma karka fita zuwa masallaci” Mamie tasa hannu tadauki dadduman su dake kan stool ta shimfidamai tace “zoto kayi” tahowa yayi yahau kan dadduman ya kabbarta salla itakuma Mamie ta zauna nan bakin gadon Hameed dan shine close to dadduman tana kallonsa, from the way yake salla ahankali kasan wajen namai ciwo har yanzu, idar da salla yayi yasake juyowa ya kalli Mamie sai kawai ya kwanto gently yadaura kanshi kan cinyan Mamie yayi shiruuuu, shafamai kai tayi tace “mezan dafamaka? Akwai waina da miya zakaci?” Girgiza mata kai yayi alamun no, murya chan kasa tace “tell me mezakaci” daidai lokacin aka bude kofan dakin Gwaggo ne tashigo tareda wani matashi dake kama sosai da Hamad exactly shima fari ne saidai baida idanu kaman na Hamad yana sanye da suit yana kallon Hamad da dan damuwa kan idanunshi, yana ganinsu ya yunkura zai tashi Mamie ta hanashi Gwaggo tace “kaganshi babu wanda yakeso agidan nan sai uwarsa, yafara mata kuskuskus kaman munafuki uwa shi kadai ta haifa” dauke kai yayi Mamie tayi murmushi Hameed ya wuce Gwaggo dake tsaye nan koda yashigo cikin dakin zuwa gaban Hamad ya duka tareda dafa kafadanshi, cikeda damuwa yace “wat happened to you Hamadi? Mesa baka fadamin bakada lafiya ba? Meke maka ciwo?” Dauke kai Hamad yayi, murya chan kasa yace “I am fine” kallon Mamie Hameed yayi da idanu Mamie ta girgizamai kai hakan yasa bai kara tambayanshi meke damunshi ba yace “are you hungry? Tashi muje muci abinci a waje” ahankali ya yunkuro zaiyi magana Gwaggo tace “wannan ne zai bika wani waje baki kawai kake batawa Hameed ai wlh saidai idan Mamarshi tasa baki shine zai bika, ka manta ranan daka kaisa wani faty haka yaron nan yaşa kafa ahanya yadawo gida” ahankali Mamie tace “Hameed barshi karku fita cus he can’t even walk properly bari zansa abinci nakawo muku maybe idan zakuci tare zaidan ci” Mami ta yunkura zata tashi da sauri shima Hamad yatashi, murmushi Hameed yayi shidai Hamad bayason Gwaggo tun suna yara, bawai ya tsaneta bane kawai surutunta da ihu da maganganu ne bayaso, ganin yatashi yasa Mamie ta kalleshi tace “ina kuma zaka”? Gwaggo tace “zai gudu mana ni Gwaggon shi dodo ina dakinsu” kin kallon Gwaggo yayi Mamie ita kanta batason wannan dabi’an nashi na kin kakarsa, Hakan yasa tace “go back and seat! Can’t you see she’s worried sick about you” Mamie tajuya tafita yawuce yazauna dab da Hameed duk Hameed na kallonshi, baimaso ya zauna shi kadai kan gadonsa Gwaggo tazo ta zauna kusadashi, da ne abubuwan Hamad ke damunshi but yanzu he’s so used to it wlh, yakalli Gwagggo dakebin Hamad da kallo duk sai yaji ba dadi yace “Gwaggo ki zauna mana salon anjima kifara mana kuka da daddare kafafunki sun fara zugi” zama tayi kan carpet dinsu tana kallon Hamad still tace “kaman kasani yau nahayo benen nan yafi akirga sabida wannan yaron dabaison mutanen, kai Hameed duk matar da Husainin nan naka zai aura zatasha fama” mikewa Hamad yayi, hakan yasa Hameed yakalleshi yadanyi dariya yace “common seat” ko kallonsu baiyiba yawuce wajen kofa Gwaggo tace “tohh ni wanan yaro dabaku yan biyu bane da sainace ba Abubakar bane ya haifesa ba yoo wannan wani irin hali ne yaro sai miskilanci ga kin jama’a, ga, ga, ga eh dan ubansa ya dauka nazo ganin fuskan nan nasa mai kama dana mata ne?” Dan murmushi Hameed yayi Gwaggo tace “atoh da lafiyansa kalau ai babu abinda zanzoyi inda yake dan ba kaunata yake ba, Hamad ya tsaneni narasa menamai uwarsa kawai yaron nan yakeso, dazaran nazo waje zai tashi yabar wajen, ya tsaneni ina dalili saisa da Babanku zai dawo dani nan naki biyoshi sabida nasan Hamadi baya sona Uwarsa Batula kawai yakeso duk tabi ta hure masa kunne” ta rushe da kuka, ahankali Hameed yace “Gwaggo mehaka kidena kuka, mesa zakice Hamadi baya sonki ke kadai yakema haka eh? Mu yan uwansa kulamu yake? Ni yanzu kinga ya kulani? Eh”? Dankwali Gwaggo ta kwanto daga kanta ta warware tana goge fuskanta ga gashin kanta dayama kare sunyi fari kal tace “nagani kam” Hameed yace “to kingani akan mene zaki dinga kuka, haka Allah yayo Hamad kitamai addu’a, amman bai tsani kowa ba kinji Gwaggo kinga baida lafiya, kina kukan nan kara tadamai da hankali kike dena toh” rushewa tasakeyi da kuka sosai tace “yooo ai yanason Uwarsa Fatimatu Batul, nida na tayata rainanku ana haihoka na karbeka na rike, saida tasake nakuda nakusan awa guda cur sannan ta haihosa shima na amshesa, baka gansa ba lokacin gabaki dayansa yayi kalan ruwan kwai wai jondus (jaundice) aka haifesa da ita, ga uwarsa ba lafiya haka nina dinga lura daku har taji sauki, kai kasha madara amman akai juyin duniya shi yasha yaki hakafa uwarku na cuta da bamata hayyacinta aka kamasa aka daurasa kan mama yasha, halama saisa yake cuta kullum sabida ya zuge na jikin uwarku alokacin, saida aka cire mata mahaifa gabaki daya kuma shine yakusan kasheta dan yaki fitowa daga ciki, kuma shine tundaga asibiti har yau yake damunta da cuta daban daban ai ban manta dakomi ba, nida nai wahalar sa wai nine yanzu zai taso ya tsana bayaso” dariya kawai Hameed kerike wa yace “toh kiyakuri Gwaggo” Mamie tadade tsaye gaban dakin sannan tabude kofa tashigo Gwaggo ta watsamata harara Mamie ta kalli Hameed tace “ina yake?” “He left the room Mamie” Mamie tadan kalli Gwaggo tace “Gwaggo kiyakuri tashi muje” kaman jira Gwaggo take tace “ohh Allah kana gwadamin ni kike cema nazo nafita daga dakin jikokina eh Batola kin rabani da Hamadi yanzu da Hassan zaki rabani shima” dan lumshe idanu Mamie tayi tabude tace “bahaka bane Gwaggo kiyakuri daman na dauka zaki sauka kasa ne bari naje” ihu Gwaggo tahau yi tace “eh kitafi wlh duk abinda akemin agidan nan zan sanar da Abubakar duk anbi an rabani da jikokina” ijiyan zuciya Mamie ta sauke tawuce tafita direct dakinta tawuce tabude tashiga Hamad na kwance kan gadonta jin an bude kofa ya kallo kofan daure fuska Mamie tayi tareda folding hands a kirji tace “wat are you doing here? Ba cewa nayi zan kawo muku abinci kaida Hameed ba”? Dan sauke kanshi kasa yayi yace “I’m not hungry” karasowa dakin Mamie tayi zuwa gaban gado tadan sassauta murya tace “mesa kabar dakin sabida Gwaggo? Cinyeka zatayi? Why do you always make her cry eh Hamadi? Can’t you see how she deeply loves you eh? She was worried sick sabida kai, the least you could do is kadan zauna ko bazaka kulata ba seeing you makes her happy, Hamadi why are you like this eh? When will you stop giving me headache? Yaushe zaka chanza halin nan eh? We are your family idan kayi haka awaje it’s okay but us fa, banda mu wa kake da shi? Mesa kake gudun Gwaggo not just she kowa ma why why why Hamad? Kullum ina daga kafa ina cewa ka girma zaka dena idan yanzu your 33 baka chanza ba sai kakai 50yrs zaka chanza eh?” Kanshi na kasa yana sauraron Mamie murya ciki ciki asanyaye yace “sorry Mamie” cikin fushi tace “I don’t want your sorry katashi kaje kuci abinci and tell her sorry” gyadamata kai yayi yatashi zaune ahankali sannan ya sauka daga gadon gently sabida ciwo yawuce ta gefen Mamie yafice tabishi da kallo tai shiru tana nazarin sa, Hameed na zaune yafaracin wainan Gwaggo namai zuba Hamad yabude kofan da sallama chan kasa ya shigo daga Gwaggo har Hameed suka bishi da kallo, Ya tsaya awajen yakasa tahowa ciki Hameed yadauke kai yacigaba da cin abinci abunsa Gwaggo tace “taho zokaci abincin ka kona maka fura zaka sha?” Girgiza mata kai yayi yana tsaye bai kalleta ba, wani washe baki Gwaggo tayi tace “yauwa toh dan Albarka zoka zauna kaci ko guda daya ne kaji” ahankali ya shiga tahowa Gwaggo ta matsamai da sauri gently yazo ahankali yashiga zama yadan kama gefen cikinsa Hameed yabishi da kallo Gwaggo tace “Wajen aikin ka kema ciwo?” Girgiza mata kai yayi yajuyo yasa hannu yadauki spoon ya gutsiri masan kadan yasa a miya yakai baki dan yatsine fuska kadan yayi Hameed yace “is it too spicy for you?” Girgizamai kai yayi yana taunawa kaman wanda akasa dole yaci, Gwaggo dake kallonshi batako kyafta idanu tace “miyan yayi yaji ne”? Girgiza mata kai yayi daidai ana bude kofan wani magidanci dake kama da Ya Mustapha yashigo rikeda yaro a hannunsa yana kallon Hamadi yace “Hamad ya jikin?” Dan kallonshi yayi daidai yaron yasauka daga jikin Babanshi yataho wajen Hamadi da gudu daukanshi Hamad yayi for the first time yasaki murmushi sosai dimples dinshi suka fito da white fararen hakoransa yaron ma ya k washe baki, Gwaggo tace “Areef narasa meya gani a jikin Hamadi dayake sonshi haka” karasowa cikin dakin Ya Abdallah yayi yace “ai ba Areef ba harsu Akram da Abdool dukansu haka sukeson Hamad, Areef oya come Uncle Hamadi is sick today” makema Babansa kafada yaron yayi, Hameed ya ballama Areef harara aiko ya tsala ihu yana shiga jikin Hamad garin haka ya takemai ciwo wani kalan runtse idanu da karfin gaske Hamad yayi dayasa Hameed da sauri
Chapter 4 · 0% Book details