← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 161

Sashe 12

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 4 yadawo daga masallaci wayanshi yafara ringing, screen din yakalla ganin Ya Mustapa ne yasa yadauka Ya Mustapha yace “start coming ina hospital” gyadamai kai yayi tareda katse wayan yafada bayi wanka yasakeyi batare daya bari ruwa yashiga ciwon ba sannin babu kowa yasa yafito yazo wajen kofansu yasa key sannan ya tsaya gaban wardobe nasu yana budewa yaga aikin Hameed kawai yazaro wani dark blue jean da t-shirt fari ya shirya tsaf kayan sunmai bala’in kyau turare ya fesa yadauki p-cap dark blue yasa akanshi, he loves wearing p-cap sabida iska sannan yadauki wani black shade, he always put on shade idan zai fita cus idanunshi somehow makes people to be looking at him both men and women kuma he hates that, wayanshi yadauka yasa a aljihu yadauki wani key dake saman side drawer shi yasa wani easy pam yafito yana tafiya ahankali looking expensive and classy kaman wasu designers yasaka, Mamie na zaune tana sauraron wani wa’azi a Sunna tv taji kamshinsa hakan yasa tadago sai kawai ta tsareshi da ido Masha Allah! Hamad is simply handsome kawai karasowa falon yayi tace “zaka fita?” Gyadamata kai yayi tace “ina zaka?” “wajen Doctor a asibiti” gyadamai kai tayi tace “jekadauki key mota na kaje dashi” girgiza mata kai yayi yace “da machine dina zani” shiru Mamie tayi tace “Tom saika dawo ayi gudu ahankali” gyadamata kai yayi yafice wajen lipan dake tsakar gidan fari yaje yadaga katsa yadauki tsuma ya goggoge yadade bai fita ba he hardly go out baida wajen zuwa idan yafita kawai da dalili, tass ya goge machine din dayayi kura sannan ya warware glass din yasaka ya kara gyara p-cap dinshi yahaukan machine din yayi wani irin kyau ya kunna machine din mai gadinsu yabudemai gate yafice.
Kusan 30min yabata cus saida ya tsaya yashamai sannan yakai hospital din yayi parking yaki shiga yaciro wayanshi yakira yayanshi, Mustapa na zaune yaga kiranshi kawai ya girgiza kai yatashi batare daya daga ba yadauki key yafito yaganshi yace “let’s go to my car” ya wurgamai key yace “drive nagaji” karba yayi suka wuce shiya jasu har zuwa computer village wani shago na slot Mustapa yace “you know wat u want pick up” shiru yadanyi Ya Mustapa yace “muje” wucewa sukayi direct wajen wani desktop yafara zuwa na dell yana duba spec din, HP EliteOne 800, 200 G45420 All-inOne G3Touchscreen... AiO - 6th Gen....CORE 13 11. This is the perfect desktop dayake bukata for his kind of work but ganin kudin #1,600,500.00 kawai saiya wuce da sauri yana duba wasu saiya juyo yakalli yayanshi yanunamai na wani 700k yace “this” Mustapa yakalla sai kawai yawuce yakalli mai shagon yanunamai na farkon yace “wannan mukeso” dasauri Hamad yazo kusada shi murya chan kasa yace “Yaya the money is too much” anatse Ya Mustapa yace “but this is the spec your kind of job needs, don’t think about the money think about abubuwan dazakayi dasu kasan how worried I was da desktop dinka ya lalace, you are stuck a software da kake developing sabida rashin desktop, I know Abba baida karfi sosai zamu karamai burden ne bayan responsibility na kanshi da yan uwansa, look at kudin daya kashe na kayan salla dudda baida shi kaman da but bazai taba dena abun nan ba cus it’s something daya saba yi batun yauba, even if it’s all my salary I will use it to get this for you, kai kadaine cikinmu da har yanzu baka kama wani takamaiman aiki ba and ka kama hanya desktop ya lalace just let me do my duty” daidai yaciro katinshi Hamad ya kalli katin na UBA dinshi ne which is salary account nashi maybe ma all his savings ne zaiyi using cus duka duka salary Doctor nawane, he has family ga dawainiyan su Abba, gashi ba’a dade damai operation ba duk sun kashe kudi” duk sai jikinshi yayi wani iri, zare kudin akayi aka bashi ATM dinshi back mai shagon ya dauko kwalin brand new desktop din yaba sales boy nashi yace “take it to their car” suka bishi suka fita ana kokari sawa a both kaman ance Musty yajuyo yaga wata yar matashiya tana kokarin bude motanta tashiga amman sai kallon Hamad da hankali shi ke kan abinda ake sawa a booth yake, dan murmushi yayi da gangan yadan taba Hamad yace “Hamadi ana magana dakai look over there” juyowa Hamad yayi yakalli yayanshi ya kalli inda yake nunamai cus yadauka wani abune ganin wata ke kallonshi dawani irin sauri yadauke kai yarufe booth yawuce yakoma driver seat ya zauna yajawo kofa yarufe itakuma yarinyar ta taho harda dan gudunta sai kawai tai knocking gaban motan Hamad yadago kai yakalleta dan glass din motar tinted ne bata iya ganoshi yaki bude kofan yajuya yana jiran Ya Mustapa yashigo subar wajen, ganin Hamad yaki bude kofan yasa Ya Mustapa yazagayo yabude kofan dasauri Hamad ya kalleshi, Ya Mustapa yace “ana magana dakai sauke glass” kaman zai mutu dan haushi ya sauke glass din, da sauri yarinyar cikin turenci tace “you are Mr Hamad ko? The Tech genius” Hamad ya dauke kanshi yaki magana yaki kallonta, yarinyar tai murmushi takalli Ya Mustapa tace “it’s him I know him, he developed wani EHR software for my Dad’s hospital ranan dayazo yamusu installing nataba ganinshi can I have your digit please” wlh kazo wajen zaka dauka da Ya Mustapa ake magana cus Hamad doesn’t even look like wanda akema magana ko kallon yarinyar bayayi Ya Mustapa ke kallonta, dan sanyi jikin yarinyar yayi saitai murmushi takalli Ya Mustapa tace “sorry for approaching you guys” tawuce da sauri jikinta yayi sanyi tayi motanta shikuma Hamad yatada motan yaja dasauri abinsa sundanyi nisa a hanya yasake kallonsa saikuma yayi shiru, Hospital suka wuce saida yayi parking motan a parking space zai bude yafita calmly Ya Mustapa yace “Hamadi!” Sauke hannunsa Hamad yayi kawai saiya kasa dago kanshi cus somehow and deep down yasan maganan da Ya Mustapa zaimai. Anatse yace “bawai sabida this incident na this girl that happened a while ago ne nake maka maganan nan ba, I’m just talking to you sabida yakamata” yayi shiru saikuma murya chan kasa yace “Hamadi bakaso kai aure ne?” Rasa inda Hamad zaisa kanshi yayi gashi he can’t walk out on Ya Mustapa kaman yanda yakema Hameed sai kawai yakai hannunshi yataba p-cap dinshi yawani janyo shi yama rasa yanda zaiyi duk Doctor na kallonshi, ahankali yace “I’ve seen and heard Hameed spoke to budurwanshi countless time infact rannan he gave her phone ta gaidani i guess Zainab sunanta idan ban manta ba” yayi shiru yana kallonshi yace “there’s no one in your life Hamadi, all of us munyi aure saura ku twins” yasake shiru yace “the whole point na this conversation is Hamad i know how u are and how you get but try and give a lady chance a rayuwanka dole kai aure one day, eventually, kaima ka haifi naka yaran at least maybe matarka will be official first ever friend naka tunda bakada su kaima kadinga samin natsuwa ajikin iyalinka” dawani irin sauri Hamad ya juyar da kanshi yana facing glass na kofa har pcap nashi nataba glass din, Ya Mustapa duk yana kallonshi wlh baitaba sanin maza can be this shy ba sai akan kanninsa this particular Hamad, dan ijiyan zuciya yasauke yace “fita kadauki bike naka lemme follow u abaya nakawoma desktop din u can’t carry it a bike” dasauri yabude mota yafita Ya Mustapa na zaune yabishi da kallo har zuwa wajen bike nasu kusan Hamad yafi dukansu kyau dudda shida Hameed are look alike but still yafi Hameed kyau far far he has lots of features naban mamaki, ga jiki mai kyau, jikinshi kaman dan gym and baya gym kawai he run daily saida akamai aikin nan yadena, he’s tall and he’s huge though ba sosai ba ga dimple ga idanunshi da zaka rantse yanasa kwalli and kwayan idanunshi are squeaky clean farare tass dasu kwaiduwan idon baki sidik girls are crushing on him right from school days but kowacce saidai ta hakura cus kokinmai magana bazai amsaba shi ko maza baya kulawa balle mata baida magana saita kama ko nan nan in this hospital week din da he was admitted saida wata nurse tazo ta samai ta gayamai wlh tana bala’in son kanninshi dan Allah yagayamai ahaka kawai ya amsata dazaran yafadanma Hamad maganan nan baya kara takowa this hospital ma. Fitowa yayi ganin yawuce yashiga mazaunin driver yaja motan har zuwa gida Hamad yarigashi kaiwa yana compund yana jiranshi yana parking yatafi booth yabude yadauki kwalin sannan yakalli Yayanshi ahankali yace “Jazakallah Yaya” murmushi Mustapa yayi yace “go and set it up” wucewa yayi yana biyeda shi har sama.
Chapter 12 · 0% Book details