← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 161

Sashe 103

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da asubahi yatashi he’s missing zuwa masallaci, jin kiran salla, one of this days zai zagaya area yaga idan zaiga wani mosque around, daddumansa ya shimfida yayi salla ya idar yayi shiru yana tunanin Asmeey, wlh abukace yake, he needs matarsa, he needs her beside him, ga sanyi yanaji, takalmin data sayamai ya kalla, sai kawai yadaura hannu saman maransa yayi addu’a, Allah ya dubesa sai kawai gaban nasa ya kwanta, Al’Qur’aninsa yakaranta har saida gari yasoma haske sannan yatashi yashiga bayi yayi wanka yafito yahada coffee yasha da dan dambun naman Mamie ya maida komi fridge yadawo daki yafara shiryawa.
Shiryawa yayi cikin wani black suit daidai jikinsa dayamai bala’in kyau, ya daura necktie yasa covershoe, kagansa bazaka dauka Hamad bane he’s fair so he look American sef, kallon madubi yayi saiyaga kaman bashiba gabansa faduwa yayi, he’s feeling nervous, wat if yakasa introducing software nasa da kyau? What if he got shy? What if he stutter? Agogo ya kalla is 9:58 hakan yasa ya zauna yadauki wayarsa Mamie yakira dake zaune kusada Asmeey data gama kwara amai takoma bacci, Gwaggo tace zazzabin kawazucin Hamad Asmeey keyi, tashi Mami tayi tabar dakin sannan ta dauki wayan ganin number kasan waje da gudu ta dauka tace “Hamadi” murya chan kasa yace “Mamie” kaman yana gabanta anatse Mamie tace “ya kake? Ya wajen? Kana lafiya? Menene yarona?” Dan shiru yayi sai chan yace “Mamie gabana nata faduwa!” Ahankali Mamie tace “mesa?” Dan ijiyan zuciya ya sauke yace “yau zan fara zuwa kamfanin by 11, yanzu goma na shirya but nakasa fita” ahankali yace “i am scared Mamie”dan murmushi Mamie tayi koda yana yaro he’s very brilliant but idan an kirasa za’a basa kyauta baya yarda yaje wani zubin saidai takama hannunsa yana boye fuskansa ajikinta suje, murmushi tayi tace “kayi azkar yau?” Gyadamata kai yayi yace “eh!” Anatse Mamie tace “being scared, feeling nervous is a normal thing and it’s okay dan kanajin hakan!” Mamie tadanyi shiru tace “kahadiye fears dinka! Face it! Kaikaci gasan nan so nothing can pull you down, kaje wajen nan kanuna musu kai jarumina ne kaji Hamadi?” Gyadamai Mamie kai yayi ahankali, Mamie tayi dan murmushi tace “they will love you cus nobody comes in contact da Hamadi na dabazai so shi ba, a ina zaka hadu da lawyer ka da Ya Mustapa yabada ku?” Anatse yace “a gaban building din” Mamie ta gyadamai kai tace “wuce kutafi kafin kashiga wajen ka karanta Allahumma Lasahala…..” gyadamata kai yayi yace “okay” saikuma ahankali yace “ina Asmeey?” Dan murmushi Mamie tayi taboyemai tace “suna tareda Munir a parlor yasata kallon cartoon, ta warware so don’t u worry” dan ijiyan zuciya yasauke yace “tom Alhamdulillah, bye Mamie” “bye Allah yabada sa’a” karfi yaji ya shigesa yamike yadauki jakansa da laptop dinsa ke ciki yafito yawuce kofa yana budewa security na tsaye yace “good morning Sir” Gyadamai kai Hamad yayi, yasa hannu ya karbi jakan Hamad suka wuce kasa yau wata arniya benz aka daukesa da ita yashiga baya har champagne an ijiye masa but baitaba ba bayashan alcaholic drink, he’s feeling nervous wayansa ne yay kara, lawyer yamasa message ya iso suna kaiwa suka daukesa yace “Hamadi kaine ka girma haka?” Adan kunyace Hamad yayi murmushi tunda yazo sai yau yaga wanda ya iya hausa shima bawani sosai ba dan anan aka haifesa, hutu kawai yake kaisu Nigeria, ciki suka shiga kai Hamad baitaba ganin kampani haka ba mai kyau, parking sukayi suka fito Lawyer mai suna Kamal ya gyarama Hamadi necktie da suit nasa yace “Masha Allah kayi kyau muje” security yayi gaba suka shiga elavator sai sama 15th floor sukaje kofan na budewa Hamad yaga mutane ma’aikata maza da mata sunkai 100 ana tafi sosai ganinsa. “Welcome Mr Hussain!” Sai chan gawani mutum dayaci mahaukacin hadadden suit yazo wajen rikeda flowers yakalli Hamad dan sunada hotonsa da komi na passport yamikamai flowers yace “welcome champion, Mr Hussain Hamad Abubakar! We are honored to have you here” kan Hamad na kasa ya karba yace “thank you Sir” CEO ya tsaya yana kallonsa sai yayi murmushi love at first sight sunada wani believe na yaro mai kaman disorder disorder haka are damn genius, a resume na Hamad he made mention he’s a shy person bayason too much crowd, and pictures and seeing him in reality sai yaji damn he love the guy, hannu yamikama Hamadi alamun gaisuwa dan kallonsa Hamad yayi looking somehow wired kafin ahankali yamika masa hannunsa yayi murmushi yace “let’s go” wucewa sukayi tareda Hamad lawyer da some team na biyeda su abaya, Hamad baitaba ganin conference room this fine ba zama akayi ga bottle water agaban kowa sannan aka fara main event din, aka bama Hamad main floor yamusu introducing software din kafin asalin rannan lunch.
Tashi yayi daga kujera dauke da system dinsa ahankali yatafi gaban smart board ya kunna system nasa kowa na kallonsa gabansa nadan faduwa saiya tuna da Mamie then Asmeey then Ya Mustapa, addu’a yadan karanto aransa, babu wanda yama gayamai ga yanda zaiyi connecting system dinsa to smart board din kawai yayi yadauki remote sannan ya kalli kowa na dakin da full confidence cikin harshen turencin sa mai dadi da zaki just simple layman accent yace “good morning ladies and gentlemen, I’m Hussain Hamad Abubakar from Nigeria and I designed this software name it SOFT AI, so what makes this SOFT AI different from all other AI in the global market? What are its’ unique features?” Wato shi farin jini, da ilimi dakuma baiwa duka na Allah ne, dan conference room din nan dayake dauke da mutane kusan 27 babu wanda baiji Allah ya daura masa son Hamad ba nothing like racism ko shi baki ne ina, all they see is potential na yaron da kalan kudin dazasu samu daga jikinsa and how genius the boy is, dudda he’s a little bit wiredo guy but that is also a spec da sukaji they extremely love, Hamad na gama presenting CEO yamike tsaye daga kujeransa yana tafi yana kallon Hamad hakan yasa kowama yatashi yanama Hamad tafi ana kallonsa sauke kansa kasa yayi eyes dinsa na twitching kadan kadan sabida yanda ake kallonsa ana masa tafi he’s not use to it, shima Barrister Kamal sai murmushi yake yanama Ya Mustapa sending video dayayi har yanda ake tafama Hamad sannan yadawo aka zauna sai next is reviewing document da agreement nan ne bangaren Barrister yafara duba komi Kamal yanama Hamad explanation, abu na farko is sunaso su daukesa yadawo permanent staff nasu, banda kudin dazasu biyasa na albashi still yanada some percentage a software daya musu developing for each user dayazo yayi amfani da abun Hamad nada 5 percent from koma mene akai generating daga user, they will take care of accommodation nasa, health insurance, access to many incentives ciki harda summer and winter vacation to country of his choice all expense paid trip, car, security, yanada two major break in a year da he can decide at any time yakeso yaje sai option na kawo any family member with kid if any, Hamdala Hamad yayi bayan Lawyer yagaya masa komi yanuna ya yarda yayi signing CEO ma yayi signing akai clapping ana raising toast dabai shaba cus is alcaholic drink.

Sannan aka kawo katon board check na kudin dayaci wato 500MillionDollars akace yazo ayi picture da kyar ya daure yaje shiya tsaya kusa da CEO da kyar aka musu picture, dudda haka saida ya karkata kai camera man yace sai an sake CEO yakalli Hamad yace “is that okay Mr Hussain?” Gyadamai kai Hamadi yayi this time around da kyar da kyar ya kalli camera aka dauka shima Kamal ya dauka sannan aka dawo aka zazzauna aka shiga kawo lafiyayyen abinci ana cigaba da meeting ana mai introducing team nasa yanada secretary wata mace baturiya, yanada attendee daga gobe zai fara aiki sabida dole ayi adjusting akuma yi kare kare akan software ta yanda it will go with standard na Microsoft, so he needs to also work with chief IT tech nasu shima yazo suka gaisa da Hamad wani wired guy dashi kaman mahaukaci but guru ne like Hamad, and Hamad kinda like him sunansa Ali from Lebanese, balarabe ne but irin wayanda basa sallan nan but lokacin salla shiyakai Hamad prayer room yaje sukayi shida Kamal kafin şu dawo ayi finalizing komi agama meeting secretary takai Hamad office dinsa Ya Allah! Sai Hamad yayi shiru is this really him? Baitaba sani in his life zaiyi aiki in this kind office ba, Office nashi kaman wani AI design office sabida kyau Secretary tace “looking forward to start working with you Mr Hussain I’m Mona” gyadamata kai yayi yawuce kawai suka tafi elevator sukaje suka shiga mota suna fitowa Kamal yace “tom sai munyi waya natura maka pictures da video a watsapp” Hamad ya gyadamai kai suka wuce, yana zaune motan yana kallon hanya wayan tasa tai kara na message yana dagawa yaga alert $500million dollars ya sauka sai yayi shiru yana kallon kudin is this kudi his yanzu? Shi? Shi Hamad din da ba komi ba? Shi Hamad da yan uwansa ke basa kudi? Aka hada kudi akamai aure? Aka sayamai machine? Aka ginamai gida? Shine mai kudin nan? Shi? He’s inside car yanaso yayi sujjada ba hali but saiya kifa kansa a chair ahankali yace “Alhamdulillah!” Duk wanda yayi dogaro ga Allah hakika Allah ya isar masa, baitabajin wani iri ko yacema Allah mesa bai basa aiki ba dudda yan uwnasa sub samu tare yagama school da Hameed tare sukai applying aikin banki Hameed as accountant shi as IT, cus lokacin Ya Mustapa yatura musu offer two slot din ake nema har interview sunje Hameed yaci shi baiciba baitaba feeling bad ba yasan his time will come, no matter situation dakake cikin dont feel pressure komi na hannun Allah within a blink on an eye Allah can change your life.
Chapter 103 · 0% Book details