← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 161

Sashe 32

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Wucewa tayi parking space ta boye bayan wani mota tadauki wayan kafin tai magana Ya Aya tace “Asmeeeey” wani irin Asmeey taji zuciyanta yayi she missed her sister Mom ta hanata kiransu sukuma hardly calls hawaye kawai ya sauko daga idanunta da sauri tasa hannu ta share cikin muryan dake nuna tana kuka tace “na’am ina kwana” shiru Aya tayi saikuma softly tace “cry cry Baby wai har yanzu bakisan kinyi girma ba” shiru tasakeyi batai magana ba, dan ijiyan zuciya Aya ta sauke tace “I secretly talks to Munir and nayi magana da Mom ma” tasake yin shiru sannan tace “Asmeey Mom has always been like this, Mom nada zafi and she’s harsh but duk tana haka sabida mu zama wani abu ne, look at me I’m a nurse today ga Ya Aysha kullum kika kunna TVC news zaki ganta, kalleki is all thanks to Mom kika gama Law at 20 yanzu sauranki Law school, look at Munir 400level Medicine Mom raised amazing kids kawai dai approach nata is harsh all of us know this” gyadamata kai Asmeey tayi tana kuka mara sauti, Ya Aya tace “ke da Munir should stop feeling kaman Mom hates the two of you, besides the Mom dana sani bata dukan daya wuce saurin kai mari idan tana koya ma karatu bakayi ba ko wani abu data saka highest ta daddakeka ajiki oh tana miki sama da haka?” Lumshe idanu Asmeey tayi ita kadai tasan me Mom kemata muryanta nadan cracking sabida kuka tace “a’a” Aya tace “kingani ya isa stop crying ai yau zanzo Aysha ne bazata iya zuwa ba sai kun dawo daga kauye sabida sunje salla a Abuja tareda family mijinta zanzo yau” murya chan kasa dake cracking tace “Ya Aya please take me with you idan zaki koma” dan shiru tayi tace “tom nazo i will try again kaman yanda na sabayi but Mom bata bari let’s see idan this time zata yarda” gyadamata kai tayi ahankali Aya tace “kije ki gaida Mom today wat you did jiya was very wrong and tell her sorry kinji” gyadama Aya kai tayi tace “tom” ahankali Ya Aya tace “akwai wani abu dakikeson gayamin”? Girgiza kai tayi tace “a’a” ijiyan zuciya Aya tasauke tace “akwai plenty clothes dana saya miki zan kawo miki yau harda very very fine abayas masu kyau” murmushi tayi tace “thank you Ya Aya nakira Ya Aysha?” Ahankali tace “no you don’t have to I will talk to her, okay Baby Sis bye take care” ahankali tace “tom bye” zare wayan tayi daga kunne ta kifa kanta akan kafafunta tana kuka but mara sauti batajin dadin rayuwanta at all duk ta tashi daga bacci she feels inama bata tashi ba tai tai bacci haka kawai sabida Mom saukan abu me taushi taji asaman hannayenta dake kan knees din hakan yasa ta dago kanta ahankali wani soft handky ne mai bala’in taushi dake kamshi gashi so warm dasauri ta dago kanta bayanshi ta iya gani dan yawuce yana sanye da farin jallabiya ya sanya farin hula na kwankwasa kaji hadisi kamshin hanky kawai taji tasan Ya Hamad ne rike hanky tayi ahankali da hannayenta sannan ta matse takai saman fuskanta wani lumshe idanu tayi feeling super calm and warm dan sanyin asuba dukya hura hancinta kusan 1good minutes tana ahaka sannan tace mike tsaye tafara tafiya ahankali tawuce flat dinsu tabude kofa ta shiga duk yaran basa falo wucewa stairs tayi tana kallon side din Mom gabanta na faduwa tawuce falon Baba tai sallama tareda bude kofan, Baba na zaune tareda Abba duk suka bita da kallo tace “ina kwanan ku Baba da Abba” Abba yace “Ya jikin kin tashi lpy” “Alhamdulillah ta amsa kanta na kasa” ahankali Baba yace “why did u come to this side”? Kanta na kasan tace “nazo na gaisheku ne Baba” shiru yayi bai kara magana ba tamike tsaye tafice side din Ammi ta wuce tabude kofa sai alokacin taga duka yaran harda su Nana da Ramla duk suna wajen tayi wajensu Ramla tace “ke baccin lafiya kike tayi jiya” murmushi tayi tace “maganin da Ya Mustapa yabani ne” daidai Ammi tafito daga bedroom dinta tace “Ammi ina kwana” Ammi tayi murmushi tace “Asmeey yaya jikin an tashi lpy” ahankali tace “lafiya lau” Nana ta kalla tabata wayan Gwaggo tace “tayani kaima Gwaggo” tana maganan tamike tayi kofa suka bita da kallo tana bude koda daidai itama Mom na bude kofan side nata suka hada idanu ta ganta tana fitowa daga side din Ammi ta dauke kanta sai kawai tajuya takoma dakin tarufe kofan yanda kirjin Asmeey ke bugawa kaman zai dare.
Ahankali take tafiya tai wajen kofan ta tsaya hannuwanta na rawa takasa bude kofan handky na hannunta ta matsa sannan taji karfi da jarumta yazo mata ta daga hannu tabude kofan ahankali tareda sallama chan kasa Mom na zaune afalonta kan dogon kujera tayi crossing kafa daya kan daya ga table gefenta da sliced fruits ke kai sai wani journal haka data rike a hannu da glasses a idanunta tana dubawa ko nuna alamun da tasan mutum na wajen batayiba maida kofan Asmeey tayi tarufe ta shigo dakin tana tafiya kaman wacce akama kaciya da kyar tazo tsakiyan dakin tana facing Mom tai kneeling ta zube guiwowi akasa ko Baba dasu Abba bata musu kalan gaisuwan nan muryanta na rawa tace “good morning Mom” Idan banza tai motsi Mom ma tai motsi next page ma tabude na journal din datake karantawa tadauki fork na fruits taci, zuciyan Asmeey harwani girgiza yake, bakinta na rawa tace “Mom dan Allah dan Allah kiyaf….fe…min, Mommy I am sorry” sake bude next page Mom tayi tadauki slice na grape tasaka abaki saida ta cinye tass sannan ta sauke journal din ta ijiye akan kujera tajuyo da kanta tama Asmeey wani irin kallon kaman zatazo ta kasheta har lahira komawa baya Asmeey tayi ta jingina da kujeran wajen Mom tawani kada kafa tafara huci tadaga hannunta ta bugi kirjinta dake wani tense sound tace “ni zaki gani jiya ki zubar Asmeey!”? Dasauri Asmeey ta girgiza kanta arude tace “Mo…..” hannu Mom ta daga mata hakan yasa ta hadiye magananan, Mom tace “ni uwarki dana dauki cikinki wata tara na raineki kawowa yau zaki kalla ki zubar Asma’u! Ina kwana, good morning bai hadani dake jiya ba rather you went and join my enemies” Mom tayi wani dariya tana karkada kafa tana kallon Asmeey tasake dukan kirji da karfin gaske tace “Asam’u dangin Babanki da kikasan basa sona da akwai yanda zasuyi tundaga kan makiran tsohuwar dayake kira da uwarsa da yayinsa Abubakar da shi dayan Kawu da munafukar matarsa maman doctor da tuni sun fitar da ni, mutum daya ke sona kap dangin su itace Maman su Nana amman shine kikaje cikinsu aka rikeki ana kula da ke ana baki magani an saki cikinsu ana gulma dake, opportunity da basu samu jikin yarana na amana Aya da Aysha shine yanzu ke sun samu ajikinki, ubanki ma ya jonasu yau rana na biyu bai kulani ba baikuma shigo dakina ba hmmmm” tasake murmushi tana kada kafafu tace “wallahi wallahi kome zakuyi saidai kuyi kinga gidan nan zama daram banga uban daya isa ya fitar dani ba wlh nasha karfinku gabaki daya ai ba tun yau akeso a kadani ba tun kafin ahaifeki to nasha karfinku kinganni nan nan gani nan bari, dake da su kuma karo wasu su jona jam’iyyan ku baku isa kuja dani ba, na taka inda kaf dinsu babu wanda ya take ke kin sani! Kinsan the kind of people I deal with, me suke da shi? Shi Abubakar din dayake fama da kasuwancinsa na kayan hatsi dayake surviving da kyar jari yakare? Koshi dansa Mustapa da ke aikin likita surgeon? Nawane salary nashi? Cus naga shine ai abin alfaharinsu agidan abin tunkahonsu kenan, koko shi Abdullahi dayake aiki a wani NGO yana fama ana turasu kauyuka koyama yara ABCD? Ko shi Faisal dake kirari yazama lawyer yana fama har yau baitaba cin case daya ba, ko shi Hameed dake fama da bank dinsa da ake biyansa baikai 150k salary ba, koko shi Hamad din da har yau ba aiki? Sis baida shi sai abinda Yayinsa da ubansa suka tsammai? Yana saida data online” tama Asmeey dake girgiza kai tana goge hawaye da hijabinta wani kallo, Mom tace “shi Kawun naki ma ba’a sashi a lissafi saisa nakeba matarsa kudi nasaka su Aya suna matarsa zakka cus she’s loyal to me to tell me saisa takejin dadi, me zasu nunamin? Me sukeda shi? Waye su kap dinsu? Ke I handle case na vise president I won! Da na yarda na karbi appointment na Abuja da tuni Allah kadai yasan mena zaba but bansan Babanki na nan ni ina wani waje, bar ganina haka Babanki dakikaga ina zama dashi sabida mijinane danakeso amman ubanki baida kudin dazai nunamin Asmeey, inada mazan dasuka fisa, so fara tundaga kansa da dangin nasa Billahillazi ni Salima nafi karfinsu, nasha karfinsu, kuma babu abinda wani shege ko shegiya ya isa yamin ke kin sani!” Mom tayi maganan tana dukan kujeran datake kai a zaune saida yayi kara Asmeey ta manne da kujera tana kuka Mom namata wani kallo tace “the only reason dayasa bazanci ubanki da durun uwar ubanki ba sabida mijinki zaizo yau da mamarsa ne amman wlh wlh saina gwada miki ke karaman yar iska ce Asama’u, zan kuma nunamiki ke yar kiyashi ce agaban Giwa, zan takeki na wuce batare danasan nayi ba, Shegiya wulakantacciya, kaskantacciya, Allah yahanaki farin ciki arayuwanki!”Dasauri Asmeey ta kalleta, Mom tace “Wlh bazaki tabajin farin ciki ba har abada yar bura’uba sainaci ubanki wlh jaka kawai karuwa!”?Wani irin kuka Asmeey tafashe dashi tana kallon Mom duka zagin nan da addu’o’in nan babu wanda Mom bata saba mata ba, she keeps saying this prayers, goge idanunta tayi gwanin ban tausayi hawaye still na zubowa tace “dan Allah kiyakuri Momy kiyafe mini kinji Mom” haukacewa Mom tayi tadauki journal na gefenta tawani wurgo mata amman bai sameta ba Mom ta zabura ta mike tana dunkulle hannu tace “ke zan kasheki fa na huta Asmeey na tsaneki, na ganki jinake kaman na halakaki, karatu yau kwana nawa bakiyi ba? Kuma bazance kiyi ba ki koma wajen yan uwan ubanki zaki sha mamakin abinda zan miki wuce kifita ki shirya karfe daya mijinki zaizo gidahuma kawai jaka” kasa tashi tayi sabida yanda Mom take a tsaye rarrafe tayi tawuce saida takai wajen kofa ta iya mikewa ta tashi tabude kofan tafita tana share fuskanta tawuce dakinsu Munir daya labe abayan wani kujera awajen yataso dan yaji komi cus yazo ya gaida Mom ne shima yaji magananta.
💫UWA KO UKUBA?💫
Chapter 32 · 0% Book details