← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 161

Sashe 117

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Turesu Hamad yashigayi sukaki sakinsa kaman zaiyi kuka yadago kansa looking for who to rescue him daga hannunsu akunyace yace “Yayaaa” ahankali Ya Mustapa yashiga zuwa anatse, Ya Abdullahi yace “wlh Ya Doctor karka shiga maganan nan, yanda maganan nan ya tsayamin a wuya, he must explain o” Faisal yace “munafukin yaro yadinga buga coitus yana tumurmusan yar mutane babu wanda yasani saidai ya tafi ya barmana result of good knacking! Sannu sharp shooter Hamadi” fizge kansa Hamad yayi da sauri yawani fada jikin Ya Mustapa ya rungumesa asanyaye kunya kaman zai kashesa, ahankali yace “ina yini Yaya” biyosa zasuyi, Ya Mustapa ya daka musu tsawa yace “leave this boy alone me haka kukeyi an airport? Zanci muku mutunci fa” Kyalesa duk sukayi kowa na kwafa, Hameed yaja jakansa Ya Mustapa yace “let’s go” dagowa Hamadi yayi suka shiga tafiya yana gefen Ya Mustapa yaki yarda ya kalli any one of them kunya kaman zai kashesa wlh shi yasan daman ya shiga uku yadawo yanda sukasan Asmeey is pregnant dinnan, kowa yasan meyayi yanzu, suna zuwa waje motan Ya Mustapa yayi dayaga na dane har yanzu mesa bai chanza mota ba yadai shiga yayi shiru Faisal da Abdullahi suka shiga mota daya Hameed shima ya shiga motan Ya Mustapa, gida suka wuce sukai parking Hamadi yafito wani sanyin dadi da peace yaji jama’a home is just home kawai and home is where the heart belongs and no place like home, gidansu yafimai hadadden gidansa a DC sau miliyan, labule Mamie tadaga hangota Hamad yayi sai kawai yashiga sauri yawuce Mamie na bude kofa yana kaiwa wajen kaman wani dan yaro yace “Mamie” yawani hugging Mamie Mamie ta kankamesa sosai tace “Hamadi! Kainake gani haka? Kaine” ta kankamesa, Gwaggo ta taso tace “wai ke kadaine mai yaron nan” sakin Hamad Mamie tayi Gwaggo tazo zata rungumesa kaman matsoraci yadan koma baya Mamie ta girgizamai kai hakan yasa ya tsaya da kyar ta rungumesa tace “Hamadi yadawo yadawo” Hamad yadan koma baya ta sakesa Abba dake falo yace “kubarsa ya shigo mana” ahankali suka matsa ya shigo kansa akasa yaga Ammi da Mama yace “ina yini ku” atare sukace “sannu da zuwa Hamad yayi hanya” Mama sai kallonsa take to karya aka musu ne ance suna kasarwaje tareda Asmeey gasa shi kadai yadawo, tadai hadiye maganan ganin ko kallon inda take Mamie batayi, ahankali Hamadi yawuce wajen Abba daya mike yana masa murmushi zai duka ya gaida Abba abba kawia ya rungumesa cikeda so yace “ahlan wa sahlan marhaba dasu lale ya hanya Hamadi” sakinsa Abba yayi anatse yace “Alhamdulillah” suka zauna aka shigo aka zazzauna Mamie da Ammi da Mmaa suka shiga fito da abinci Hamad yadan saci kallon ko’ina a falon saikuma yakalli su Mamie dake fitowa daga kitchen harda dan kara lekawa kowa yana luradashi, Ijiye abincin sukayi Mamie tawuce sama dakinsu ta shiga wanda tasan Asmeey tai bacci yanda tasha uban aman nan kuma yau excitement yasa batai baccin rana ba kwata kwata allah sa ta iya tashi, tana kwance akan gado sanye da atampan jikinta ko wankan dare batayiba balle chanza kaya Mamie tadan bubbugata tace “Asmeey, Asmeey” amman ko gezau batayiba Mamie ta girgiza kai tace “Allah sarki ciki kenan, yammatana anyi ciki kalli yanda bacci ya shigeta” bargo kawai Mamie taja tarufa mata tabude kofa tafito tashiga saukowa Hamad yakalli benen da sauri kowa na lurada shi, Mamie tadan kalli Hamad daya maida kansa kasa da sauri tace “yau gabaki daya batai baccin rana ba, nayi nayi ta tashi taki” anatse Ya Mustapa yace “gwara dakika barta Mamie tashinsu a bacci is not good yana samusu migraine and other ciwo” dan boyayyen ijiyan zuciya Hamad yasauke yashigacin abincin da tsakura yake but yaci still cus yayi missing abincin Mamie, yanaso yatashi yatafi sama amman yasan yana tashi yayyinsa will eat him raw Abba yayi gyaran murya yace “Doctor sha biyu tayi a tashi kowa yaje gida wajen iyalinsa, Hamadi jekai wanka kahuta” mikewa yayyin sukayi Hamadi ma haka sukai sallama suka wuce Hamadi yawuce sama Hameed natayasa daukan jakansa har sama zuwa gaban dakinsa yawuce dakinsa ya shige shikuma Hamad ahankali yasa hannu yabude dakinsu gabansa kawai sai faduwa yake ya shiga ciki Asmeey yagani kwance agado maida kofan yayi yarufe without making a sound yasa key, yajuyo yakalleta tana sanye dawani brown atampa mai red pattern yamata kyau sosai kanta babu dankwali amman tayi kyau, kitsonta sunyi kyau sosai she’s deeply asleep tana sauke ijiyan zuciya ahankali, gently yashiga wucewa har zuwa gaban gadon ya tsaya yana kallonta kafin ahankali ya zauna yamika hannunsa daya yakama hannunta kafin gently yakai dayan hannunsa yadaura saman cikinta murya chan ciki yace “Assalamu Alaykum Habibty and my little one, why are u making Momma sleep too much? Momma couldn’t even wait for Abee because of you? Haka zamuyi? Uhm little baby”? Yayi shiru yana murmushi sai kawai yahau kallon fuskan Asmeey wani irin tausayi da sonta na shigansa duk namijin da bazai tausayama matarsa mai ciki ba baida imani, the way Asmeey was happy akan dawowansa to finds her sleeping yanzu just shows the journey na bringing human into this world is not easy, u have no control about rayuwanka from d day kayi ciki har zuwa haihuwa da sanda zaka aurar da yaro, murya chan kasa feeling very greatful to Allah daya basa ciki, and thankful to Asmeey for being the source of this blessing yace “thank you for doing this journey for me Husnahhh” ta rame sosai but he promise he will take care of her harsai tasami lafiya jikinta yadawo bazai kara bari tai komi ita kadai ba, he will show her this pregnancy banbancin kawai shine ajikinta ne but this journey is so for both of them, he will be her support and her strength, he will be he comfort and peace, he will gives her the entire world if needed sef, cus he extremely love matarsa and loves their child datake dauke dashi.

Har wajen biyun dare yana zaune awajen just watching her sleep and turns yana rike da hannunta still sannan yatashi ahankali yawuce bayi yana kallon basket nasu babu kayan wanki ko daya bayi yashiga yaga ta jika under wears nata guda uku a karamin bowl kafin yayi wanka ya wanke mata ya shanya mata a igiya sannan yayi wanka, yafito yaciro jallabiya yasa she told him about batason turare sai baisa ba yadawo ya shimfida dadduma yahau salla har asubahi yazo gadon yakara rufamata bargo da kyau sannan tawuce yafita yatafi mosque.
Chapter 117 · 0% Book details