← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 161

Sashe 31

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tashi tayi tai magriba tana kan dadduma Mamie tashigo da plate na nama da abinci tace “Ma’u yaya jikin da sauki?” Gyadama Mamie kai tayi tai murmushi mai kyau, Mamie ta ijiye plate din takai hannunta ta shafa kumatun daya sabe, jan shima yaragu tace “tuntuni kina daki ci abinci kije ki tayani share dakina su Areef duk sun zubamin cincin akasa zaki iya?” Dasauri ta gyadama Mamie kai dan tuntuni tagaji da zama without purpose, itama Mamie that’s why tadan sata aikin, Mamie ta mike tace “bari na koma backyard muna chan idan kin gama kinaso kizo kizo kinji” sake gyadama Mamie kai tayi tace “toh naji” fita Mamie tayi daga dakin tai shiru tana kallon abinci da batada apatite na ci sai kawai ta ijiye, tashi tayi tadauki blue gyalenta ta yafa tafito babu kowa a falo store ta shiga ta dauko broom da packer tafito tawuce sama daganan bene tanajin muryan maza da dan yawa daga dakinsu Ya Hamad karasa hayowa sama tayi takalli dakinsu kofansu arufe hakan yasa tawuce dakin Mamie, ahankali tabude kofan dakin kamshi mai dadi AC ma a kunne dakin duhu banda hasken dake shigowa ta kofan data bude wanda yake na nan corridor babu any haske a dakin, normally dakin akwai switch tanan gefen kofa but yadena aiki sai switch din wajen gado haka tasaki kofan ta shigo ta ijiye broom da packer kofan ya shiga rufe kanshi kadan kadan itakuma tawuce wajen gadon daidai kofan yakarasa rufuwa kamshin dataji ajikin Ya Hamadi taji awajen amman bata kawo komiba ta mika hannu ahankali ta danna switch din wutan dakin yakawo idanunta suka sauka kan Ya Hamadi dake kwance kan gadon Mamie idanunshi a lumshe yana sanye da wata faran t-shirt na polo da wandon kayan sallanshi da alamu bacci ne yadan sace shi adakin Mamie yabar dakin sabida baki dan taji muryan maza datana shigowa.
Faduwa gabanta yayi dummm! Saita dan koma baya dasauri ta tsaya tana kallonshi the way he’s sleeping peacefully, dogayen bakaken gashin idanunshi sun rufu ruff fuskanshi na sheki kaman me yin skincare, yamata wani kwarjini a idanunta kaman me, kasa koda motsi tayi sai kallon fuskanshi take kirjinta nawani irin racing kaman akwai wani abu dake kama kafafunta yana pulling nata zuwa gaban gadon, taka kafarta tashiga yi daya bayan daya tana zuwa gab da gadon ta tsaya daidai bakin gadon tana kallonshi tai shiru kaman wawiya kaman wacce is confuse akwai wani kalan abun datakeji tunda tai girma tai wayau arayuwanta kullum she’s feeling tense at any moment cikin tashin hankali take da fargaba da tsoro both boko da islamiyya da gida gudun Mom tsoronta da gudun karta mata laifi, she don’t know what happened yesterday was the first ever time she felt peace azuciyanta the little moment that she shared with Ya Hamadi ganinshi gives her wani internal peace, tafiyan shi, maganan shi, kallonshi, duk yana sa taji wani natsuwa acikinta da bata taba sani ba akwai kalan natsuwar, tarrr Hamad ya bude idanunshi sabida kamshin bodymist nata that’s so calming, it’s smell’s fruity with notes na amber and slight oud, hada idanu sukayi eyes nashi looks freaking wild idan yatashi daga bacci sabida kwallin he looks like wani aljanin misira da mahaukacin tsoro tajuya zata gudu karaf yakama bakin gyalenta bawai yawani rike da karfi bane hakan yasa gyalen yazame daga kanta gashinta suka wani bayyana ta tsaya chak batare data juyoba sai tahau kame kame. “Ummm Ma…Mamie tace nazo na gyara dakin su Areef sun bata bansan kana ciki ba sorry” yakai kusan 5secs yana kallon bayanta which is so unlike him dan babu wata mace dayake tsayawa ya kalla arayuwanshi banda Mamin sa sannan yasaki gyalenta yatashi daga gadon ahankali yasauka yadan gyara riganshi ya saukar kasa da kyau, yasaka slippers dinshi dake wajen sannan yazo yawuce ta gefenta yafita tabi bayansa da kallo har saida yafita tawani duka tana dafa kirjinta, wat is wrong with her? Takai kusan 5mins aduke awajen sannan ta mike tsaye tawuce wajen gadon danta gyara sannan tayi shara wayanshi tagani agadon iPhone XR yar karama size na wayan, ko ita 11 pro max take amfani dashi, gently tadauki wayan, wayan kamshi, samin kanta tayi da zama abakin gadon Mamie takai wayan ahankali zuwa hancinta tana shinshinawa wayan smells exactly like him, ijiyan zuciya ta sauke wayan smells exactly like him is so calmling, vibrating wayan yayi hakan yasa da sauri ta sauko da wayan ta kalli screen din taga whatsapp message ne from number da babu suna. “Please talk to me Hamadi” saikuma wayan yasake vibrating another message na shigowa from same number “I am madly in love with you Hussain! Aneesah ce!” Hakanan wani abu Asmeey taji a wuyanta why did she even carry the phone? Maisa wayanshi ba key? Maisa notification nashi aren’t hidden? Vibration wayan yasake vibrating another message ya shigo “I was able to trace your house nazo ance kunzo Bauchi salla” daci wuyanta yahauyi sosai tana kallon screen din kawai taga ruwa ya diga akan screen din hakan yasa da sauri takai dayan hannunta tadaura saman idanunta taji ashe kuka take daidai an bude kofan dakin dasauri ta dago kanta hada idanu sukayi da Hamad daya hade giran sama da kasa yana kallon wayansa dake hannunta da sauri ta ijiye wayan akan gado tawuce bayin Mamie da gudu ta shiga tana maida kofan tana rufewa, yadan jima tsaye awajen yana kallon kofan cus yaga hawaye kan fuskanta sannan yashigo yazo gaban gadon yadauki wayanshi yaga bata shiga wayan ba but he saw the messages shima, sake kallon bayin yayi na kusan 3secs sannan yawuce yafita yarufo kofan hakan yasa ta fito idanunta sunyi ja gadon Mamie kawai tawuce ta gyara sannan ta share dakin tass tafito da packer da broom sai sunan Aneesa ke yawo aranta kitchen ta wuce ta zubar sannan takoma daki tai sallan isha’i ko’ina Gwaggo take oho ita kadaice agidan su Ramla ma duk basa ta kanta toh salla ake kowa is happy wake zama adaki sai ita abincin ta dauka spoon tayi tahauci duk ranta abace yake ijiye wa tayi tadauki magungunanta dan kawai tayi bacci ta sha tarasa yanda zatayi ranta sai baci yake sai kawai taja karaman tsaki. “Aneesah sunan ma ko dadi” Mtsww taja tsaki sai kawai ta kwanta har Gwaggo tashigo mutane da dama sun shigo duk taki juyowa an dauka bacci takeyi nan ko baccin bai dauketa ba sai around 12 nadare.

Wuraren biyar ta tashi daga bacci akan dadduma taga Gwaggo data tsareta da idanu tace “sannu tashi kije kiyi salla Yayyinki Aya da Aysha duk sun kirani jiya da daddare amman kinyi bacci sunmin barka da salla sunce ki kirasu” gyadama Gwaggo kai tayi tawuce bayi brush tayi ta dauro alwala tafito tazo gefen Gwaggo tai dalla data idar tai azkar sannan tajuyo ta kalli Gwaggo ahankali tace “ina kwana Gwaggo” washe mata baki Gwaggo tayi tace “jibi yanda kika fara kumari dana dagaki daga gaban uwarki ohh wallahi Asama bakiyi dacen uwa ba” sauke kanta kasa tayi tasa hannu ta dauki wayan Gwaggo dake wajen ta mike zatai kofa Gwaggo tace “wayan ne har sai kin fita” murmushi tayi tabude kofan tafice waje tafice tana dialing number Ya Aya da ringing daya taga an katse tana kira back
Chapter 31 · 0% Book details