← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 161

Sashe 14

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

EPISODE 6️⃣
Yanda muryan Mom ke amsawa a dakin har cikin y’ayan hanjin cikin Asmeey takeji, duk yanda takai ga tsorota saidataji no she have to help kaninta, daurewa tayi tafito daga bayan Munir ta shiga gabanshi tana maidashi bayanta ta boyeshi tama kasa kallon Mom sabida tsoro da fargaba, muryanta kaman na mai koyan magana tace “Mm….Mom baice komiba game dake, kawai firanmu muke ko Munir” Munir yaki magana kaman da gunki take magana, arude Asmeey tadan kalli Mom dake huci tace “Mom Allah baice komiba maganan mu muk…..” Tassss! Mom ta dauramata mari da saida tayi baya baya kaman zata fadi Mom ta matsar da ita gefe tana hankadata tana kalle kalle a dakin taga igiyan chajin lantern tazaroshi tazo dab da Munir dake tsaye kikam cus kawai yaji zuciyanshi yabushe yagaji da abubuwan Mom, Mom tace “I said repeat everything daka fadi”kasa magana yayi jikinshi still rawa yake but yaki kallonta, Mom tadakamai tsawa tace “you called me annoying? Kana cewa Allah sa sister ka ta sami miji that will take her away from me? You wished inama wanchan matan ne maman ka? Gani nan say everything to my face talk” tadaga wayan wutan zata zugamai da gudu Asmeey tashiga in between them kawai ta rungume Munir bulalan sai ajikinshi, tafashe da kuka sosai tace “Mom kiyakuri Munir is a small boy he doesn’t know wat he is saying, he said it amman he didn’t mean it is just anger” ran Mom abace sosai tace “wallahi idan baki saki yaron nan ba zan miki jina jina zan halakaki Asma’u! I know kece ke koyamai mugun halin nan, saki yaron nan nace” sosai Asmeey ke kuka ta kankame Munir cus tasan Mom duk sanda tayi fushi haka zata iya sumar dakai ita tasaba but not Munir, she knows yanda Munir keda jin kunya Mom tamai duka zai dingajin kunyan su Yusra da Amina, cikin muryan kuka da tausayi tace “Mom kiyakuri please, Munir tell Mommy sorry” kaman bada Munir take magana ba yaki cewa uppan, Mom tawani kama rigan Asmeey tajawota Asmeey taki sakin Munir tana kuka sosai bata tabama Mom gardama hakaba sai yau kawai zuciya yakwashi Mom tashiga kaimata duka tako’ina da wayan tace “zan kasheki kuwa dan ubanki Munir ko zan kasheki kuma sainaci ubansa” shi kanshi Munir kokarin ture Asmeey yake dukan ya sauka akanshi taki sakinsa, Mom ta zagaya danta sami Munir Asmeey tasake zagayawa tana kareshi muryanta so weak tace “Mommy don’t beat my brother please” Ammi tashiga knocking kofan tana jijigawa daga waje. “Maman Aya! Maman Aya Dan Allah kiyakuri kidena dukan yaran nan da magriban nan dan Allah kekam” Asmeey da muryanta ba karfi tace “apologize to Mom Munir” cikin kunkuni yana nishi kaman zai fashe sabida zuciya yadaga murya yace “fisabilillahi Annabi yadaki yaranshi ne? Malam bai taba karanta mana a seera Annabi Muhammad SAW yadaki yaransa su Nana Fatima da wayan wutaba or always slapping yaransa ba, anything Mom tace muyi we do it, we obey Mom all the time why will she be beating us kullum especially you? Ke jaka ce? Are you animal dazata dinga duka all the time? We are children we make mistakes is her duty to correct us why will she be beating u and me? Why will Mom be beating me a parlor in front of su Yusra how will my younger ones respect me? I am an adult Mom saita dinga dukana, kuma ni hostel zan koma nabar mata gidan since she’s an abusive mother!”Lahaula wala quwata illabillahi aliyul azeem yanda maganganun Munir suka daki zuciyan Mom batasan sanda tayo kanshi ba tace “yau saina hallaka ka dan ubanka Munir cikashi Asmeey” awani irin zuciye ta fizge Asmeey ta jefar saida Asmeey ta buge da bango sosai ta zube akasa Mom tadaga wayan zata kaima Munir duka yarike wayan gam cikeda zuciya hawaye na fitowa daga idanunshi sosai yana huci yana kallon Mom kaman zai rama Mom tace “au dambe zakai dani Munir?Dambe zakai dani? Fine ga bulalan zaneni” tasakinmai wayan dasauri yasaki wayan akasa yana huci Mom tace “nadauka kakai matsayi yanzu since u talk back at me u can beat me eh pick that cane and beat me” yaki motsi, Mom ta zubamai mari da saida yayi baya zai fadi tsabagen yanda ya shigeshi, Mom tace “wlh yau idan bakasa hannu ka dakeni ba Munir take out all this anger on me I will not leave here, baka tsaneni this much har kana cewa inama banine na haifeka ba oya beat me” kokarin tashi Asmeey take tana kuka sosai tama kasa danta bugu, ganin Munir yaki komi sai huci yake yasa Mom ta fizgoshi da karfi tace “look into my eyes and beat me kaji adult Mr Munir adult, grown up saurayi” Munir yaki kallon Mom, mari Mom tasake dauramai tace “fight me, daki mahaifiyarka kaji!” Yunkurawa Asmeey tayi da kyar ta taso tazo wajen takama hannun Mom dake wuyan Munir tana wani irin kuka tace “Mom you’re hurting his neck please kiyakuri Mommy dan Allah” yanda ran Mommy ke baci batasan sanda tasaki Munir ta yankama Asmeey mari a fuska dayasa jini ya barke daga hancinta ba tace “yaushe kikai girman ki kama hannuna kirike waye ke Asma’u kaskantacciya dake” baya Asmeey tayi zata fadi dasauri Munir yariketa yana daga riganshi yasa asaman hancinta sai alokacin yafashe da kuka yana kallonta yace “stop involving kanki nina mata laifi not you takashe ni is not your business eh, she hates you the most so ke zatafi duka not me just like now, stay out of this Asmeeey” girgizamai kai Asmeey tayi tace “I will always protect you” zuciyan Mom na tafarfasa tace “au Allah okay then” kawai ta tsugunna tadauki wayan Asmeey zata yunkuro abunka danamiji Munir kawai yariketa gam ya kareta ya kankameta Mom dukansu take tako’ina, ta finciko Asmeey daga jikinsa tashiga jibgarta bana wasaba Ammi kaman zata karya kofan yaran na kuka sosai, wani mahaukacin buga kofan akayi. “Salima!” Chak Mom ta tsaya, cikin kakkausan murya Baba yace “kika kashemin yara wlh wlh sai anjimu dake aduniyan nan gabaki daya ba garin nan ba!” Yarda wayan Mom tayi takallesu dukansu biyun sun galabaita sosai takalli Munir tace “I’m not done with you” tawuce kofa tabude Baba ne tsaye gaban kofan sai Ammi ga yaran suna ganin Mom dukansu harda Ramla suka boye abayan Ammi, Baba yama Mom wani kallo taki kallonshi tawuce fuuuu Baba yashiga dakin Ammi biye dashi, ganin Asmeey da Munir kawai Baba yaji kanshi yadauki zafi, ranshi yabaci sosai, Munir yakama kawai yasa ajikinshi daya fashe da kuka sosai Ammi taja Asmeey da jini kebin hancinta tace “Subhanallahi, Subhanallahi, bani ruwa Ramla abayin nan yi maza, kira Dr Alhaji”Baba na rike da da Munir dashi ma ya daku amman namiji namiji ne huci kawai yake ba kuka yana kallon Asmeey dakaman numfashi na neman kufce mata, Ammi na share mata fuska Baba yamike yana daga Munir yaron yama kasa tashi da kyau Baba yarikeshi yafitar dashi yakaishi mota ya ijiye yazo shida Ammi suka dauki Asmeey suka fito da ita sukasa a mota muryanshi har baya fita sabida bacin rai yace “ki zauna da sauran yaran lemme take them to nearby hospital” gyadamai kai Ammi tayi tawuce yabude baya ya zauna baya kusada Asmeey ya daura kanta kan cinyanshi driver shi ya shiga gaba aka jasu sai asibiti.
Chapter 14 · 0% Book details