← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 161

Sashe 21

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

✍🏻M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn

EPISODE 9️⃣
Dakinsu ta shiga bayi tashiga tai wanka dan batai wanka ba tun safe fitowa tayi tabude sip taciro wani gown na atampa mai kyau yanada blue floweres shiryawa tsaf tayi tasaka sannan tazo gaban madubi takalli fuskanta har lokacin fuskan yayi ja sai kawai taji har kunya kunya takeji ma tafita mai ta dauka ta shafa a fuskanta sannan tazo dauki kwalli tasaka duk dan tai looking normal hakan saiya rage redness na fuskanta amman saitayi bala’in kyau gashinta ta warware a wanke yake har tsakiyan bayanta gashi baki gwanin kyau batada full gashi sai tsayi but is scanty and silky combing tayi sai kawai ta dauki blue veil ta yafa tadan fesa bodyspray dinta ta tashi ta kalli madubi murmushi tayi saita fito ta sauko kasa babu kowa a falo saita fita tana tafiya ahankali zuwa wajen masu kitso Ramla dahar an gama mata kitso tace “wat happen to fuskanki?” Zama tayi kan tabarma tace “faduwa nayi laaaa lallinki yayi kyau Ya Ramla” tai maganan da sauri dan ta kauda maganan, takalli lallin Yusra tace “Yusri iyyeee Irin naki za’a min” Yusri ta washe baki Amina tace “Ya Asmeey kiyi irin kitsona” dasauri tace “shiko zanyi” Yusra tace “ga Mom tafito” wani kalan faduwa gaban Asmeey yayi da sauri ta sauke kanta kasa Mom tashiga tahowa wajen fuskanta kaman bata taba dariya aduniya ba tana sanye dawani simple gown na Cotten irin na Egypt din nan masu manyan mayafi sai wani mashahiurin kamshi take idanunta akan Asmeey dataga tai wanka harda chanza kaya, Yusra na ganinta tayi murmushi tace “Mom saura ni ana gamama Amina za’amin kitsona asamin beads” Amina tace “Mommy lalle na yayi kyau” dan murmushi kadan tayi tace “yayi sosai” takalli Asmeey da kanta ke kada cikeda authority da isa da iko tace “ayi miki kitso only banda lalle” ba Asmeey kadai ba hatta su Yusra yara da su masu lallen da masu kitson da Ramla saida suka kalli Mom, wani iri Asmeey taji cus tanason lalle duk salla Allah yasani lalli da kitso da saka sabon kaya are the measure things she looks forward too, amman saita gyadama Mom kai ahankali muryanta nadan breaking tace “tt….toh Mom” strictly Mom tace “good! You’re going to law school bayan sallan nan, henna kowani iri is not allowed” sake gyadama Mom kai tayi ahankali kanta akasa, Mom tajuya tawuce abinta batare data kara kallonsu ba tana tafiya kaman itace mai gidan masu lalle da kitso suka bita da kallo asace ana mamakin gadaran matan, duk yanda Asmeey taso ta daure takasa kawai saiga hawaye sharrr dasauri takai bayan hannu ta share kafin wani ya lura dan kanta na kasa, me lallen tace “menene law school Ramla?” Ahankali Ramla tace “makarantan dakake zuwa kazama cikakken lawyer, da gaske ba’a barin lalle” mai lallen tace “amman ai yanzu lalle nan da nan yake gogewa kuma shampo na goge lalle lokacin yayi aisaita goge lallen” Ramla tace “tunda Mom tace kartayi kartayi mubar maganan nidai” Asmeey tai shiru zuciyanta baya mata dadi kawai kitson ma kaman kartayi but tasan Baba zaiyi magana, haka aka gama na Yusra sai akahau mata kitso shiku mai bala’in kyau yan kanana ana cikin mata Kawu ya iso daga Gombe.
Chapter 21 · 0% Book details