← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 161

Sashe 80

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Asmeey tajuya azuciye zata cigaba da ciro kayanta na sip saikuma taji takasa sai kawai takifa kanta a kofan wardrobe din tana wani irin kuka mai bala’in sosai zuciya tabama Abba da Ya Mustapa tausayi Abba yariketa yakamata saiya zaunar da ita akasa yakalli Mustapa yace “bani goran ruwanchan kagani” dasauri Ya Mustapa yakawo bottle water dake kan desk yabude yabama Abba ya karba tofa addu’a yayi ciki na sanyaya duciya yadafa kan Asmeey yace “sha ruwan nan” da kyar Asmeey ta iyashan kadan Abba yacire ruwan daga bakinta yashafa kanta yana kallon yanda take wani irin kuka ta taba zuciyanta tace “Abba na shiga uku na lalace wlh na bani Abba, Abba zuciyana yanamin kaman yafi komi na duniyan nan nauyi, Abba mutuwa baifimini ba da irin yanda zuciyana keyi? Eh”? Abba yace “kowani dan Adam da tasa kalan jarabawa aduniya kuma kashe kanka da kanka haramun ne wuta zaki shiga direct sannan kinyi wahalan banza, kingama wahala na duniya kisha wahala dan Allah baya karban ran wayanda suka kashe kansu ta sauki, kikagama wahala ki mutu kije kabari ki wahala kije lahira ki wahala toh ina dalili? Asmeey ina tauhidin ki? Ina tawakkul dinki? Ina Imani da kaddara dinki mai kyau da mara kyau? Ina yarda cewa komi daga Allah ne? Eh Asmeey?” Tana wani kalan kallon Baba face “Abba yaya zanyi kasan yanda zuciyana kemin sabida abinda Mom tama Mamie? Abba abin yamin ciwo sama da kowa, Abba kaga sabida ni Baba yasaki mahaifiyata! Sabida ni Mom bata magana da Ya Aya, bata shiri da Munir! Munir haushin Mom yakeji sabida ni! Sabida ni Mom ta tsaneku gabaki daya! Abba everything is happening because of me, this beautiful house, this beautiful family da kowa ke murmushi kullum baku fada bakujin haushin kowa yau because of me sabida kun shigo dani gidan nan komi ya chanza!”Abba I think ni kambun baka ce duk inda na taka ko na shiga fitina na bini banda good luck, bantaba jin ance Mamie batada lafiya ba but sabida ni Mamie na gado ba lafiya everything’s na faruwa because of me me me me meeeeee, Abba Abba ku barni natafi I don’t want to be reason dazaisa wani abu yasami Mamie koya sami gidanku koya sameku, Abba ni yar Mom ce kome tamin is okay wlh nasaba but is not okay ya shafeku nacigaba da zama anan more and more abubuwa will happen tayaya zan kalleku? How can I look at you all bayan nasan I am the reason for everything”? Ya Mustapa yakusan kuka forget some maganganun Asmeey akwai shirme da yarinta but now datakema Abba addressing abun he understood where the girl is coming from she’s feeling extremely guilty because of Mamie, bama ta kanta da ciwonta takeba ta Mamie take and she feels barinta nan will make everything okay koba komi tanada certainty cewa Mom bazata kara zuwa ba so kowa will be safe.
Kanta Baba yashafa yace “stop blaming kanki for mistake na mahaifiyarki! Abinda yasami Mamie Allah yariga ya kaddara hakan zai faru and it’s okay komi yawuce, koda wasa kada ki kara kuskuren fadin cewa mun tsaneki ko wasu maganganu makamantan haka koda ace baki auren Hamadi ke diyata sannan kuma kannin su Faisal I know yarana they will never hate you saima suyi protecting naki kinji” gyadama Abba kai yayi yace “magana ta wuce banson kara jinta karki kara tunanin kashe kanki wannan rayuwan Allah ne ya baki shiya halittoki shi kadai keda ikon karbanta ki gujema azaban Allah sannan kiyi istigifari da abinda kika aikata na kusan kashe kanki just now”

Sosai wani tsoron Allah ya shigeta tace “Astagafurullah!” Abba yace “konmayi salla?” Girgixamai kai tayi anatse yace “tashi kije kiyi salla kiyi wanka zansa mai girki takawo miki abinci” gyadama Abba kai tayi Abba ya yunkura zai miki ahankali tarikeshi Abba yajuyo ya kalleta yunkurowa tayi sai kawai tayi kneeling agabansa tahade hannuwanta biyu tafashe da kuka tace “Abba I am sorry kayafemin, Ya Mustapa kuyakuri dan Allah bazan karaba, I am very sorry” murmushi Abba yayi sosai anatse yace “nahakura Doctor kaima kahakura?” Gyadamata kai yayi yace “tashi kije kiyi wanka komi yawuce”tashi tayi ahankali su Abba suka wuce suka fita suka kullo mata kofa tsayawa tayi takalli kudin da Ya Hamad ya watsamata akan gado sai taji kukan dayafi na dazu yazo mata sosai, Abba duk suka juyo kukan Abba zai koma Ya Doctor yarike Abba tareda girgizamata kai yace “she’s crying sabida mijinta ne yanzu, kabarsu Abba zasu shirya, kuma mubar Hamad yayi fushi karkamai maganan ya shirya da ita, Asmeey na bukatan tasan daraja da kima da mutunci dakuma matsayin mijinta arayuwanta, bakaga da kanta takasa cigaba da fito da kayan ba? Ai bamu cemata karta tafi ba shima kuma yabarta ta tafi, she needs to know mahinmacin mijinta Abba next time bazata kara irin kuskuren nan ba, sun sami rashin fahimta su biyu dudda Hamad bai fahimceta da manufanta kaman yanda mu yanzu muka fahimceta ba, but abinda yamata was very good Abba! Shine mijinta and yes shine mijinta! Comparison na uwa da mata is a no no dudda itama yarinta yasa tai maganan she didn’t mean it, but gwara daya mata haka next time suka sami wani matsala bazata sake kalan kuskuren nan ba” ijiyan zuciya Abba ya sauke he respect thought na Dr sosai a yaransa sabida yanada hankali da hikima sosai yace “amman kana gani auren nan zaiyi lasting wannan mayyar mata tazo kano”? Murmushi Dr yayi yace “Abba babu abinda zai sami aurensu sabida yarannan sunason junansu sama da yanda su kansu suka sani and type of love nasu is not something that is easy to break, Asmeey da kanta tace daza tafi da kanta kuma takasa cigaba da ciro kaya, dakuma kanta da zauna tana kuka, dakuma kanta tabamu hakuri, Abba she’s gradually developing love for Hamadi that is getting stronger than tsoron datakema mahaifiyarta, da ace dane da tuni ta tafi but kalla dudda uwarta na fushi she stays here dudda babu wanda ya riketa mijin yama bata kudin mota but she couldn’t go, Let them be, auren nan Allah kadai zai iya rabasa” ijiyan zuciya Abba ya sauke yace “bari naje wajen Mamie je wajen kanninka” Gyadamai Kai yayi Ya Mustapa yawuce dakin Hameed.

WAYE KEDA LAIFI A FADAN NAN?

HAMAD WENT TOO FAR RIGHT?

SHI YA NUNA TASA UWAR NADA DARAJA YANUNAMA ASMEEY TATA UWAR BATADA DARAJA??

SHIN HAMAD YA KYAUTA?

ASMEEY TA KYAUTA DATAI BLAMING MAMIE?

COMPETITION ASMEEY KEYI DA MAMIE??

SO TAKE HAMAD YAFI SONTA KAN MAMIE??

WAT EXACTLY ASMEEY KESO??

Let’s discuss 💃
EPISODE 4️⃣6️⃣

Hamad yagani zaune kan gadonsa yajingina da bango yana kallon window gasu Faisal da alamu sunmai magana sun gaji yaki kulasu, karasawa yayi yazauna gefen Hamad din yakallesa sai kawai yayi patting hannunsa yace “Hameed nasan kaine sarkin update, is this the second lovers fight ko first?” Atare Faisal da Hameed har suna hada baki sukace “second ne Ya Doctor” dan murmushi yayi yakai hannu yashafa kan Hamad yace “ba’a handling mata da zuciya haka Hamad! Kacika zuciya, aka ganka sai adauka bawan Allah ne kai ba’asan kaine fitinannen yaron gidan nan ba mai dan banzan zuciya, why will you give matarka kudi and tell her to go”? Baimason maganan yunkurawa yayi zai tashi daga gadon zai wuce Ya Mustapa yarikeshi kawai saiga hawaye shaar! Yasauke kansa kasa hawayen na diddiga, Yayinsa duk suka taso, murya chan kasa Hamad yace “leave me alone Yaya” Ya Mustapa yace “anki dawo ka zauna anan” yakamasa badan yaso ba ya zaunar dashi, ahankali Ya Mustapa yace “ba inda zata, Asmeey is not going anywhere” murya chan kasa yace “ina ruwana” yawani juyar da kanshi su Faisal sukace. “awwwwnnnnnn” cus He looks so cute wlh dayace ina ruwanshi, Ya Mustapa yace “kadauka you can live without Asmeey ta tafi? Haka zaka dinga mana kuka kullum” bayan hannunsa yasa dasauri ya goge fuskansa yace “ni I am not crying because of her ta tafi mana! I am just sad ne because of Mamie” Faisal yace “wlh karyane munafuki! Ta tafi wazaka dinga matsawa agado”? Dawani kalan sauri Hamad yamike Ya Mustapa yakamosa yana ma Faisal dakuwa yace “wat is wrong with u?”Ya Abdallah yace “Ya Doctor gaskiya ne fa mace wasa ce? Idan ta tafi baida wajen biyan bukat…..” tashi Hamad yayi yace “niku saken” ya fizge hannunshi yawuce yafita daga dakin Ya Mustapa bai damu ba he will talk to him later dan yan iskan yaran nan will not let him speak to him, sai suma yahau magana dasu kan Asmeey yana musu bayanin situation na yarinyar.
Chapter 80 · 0% Book details