← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 161

Sashe 136

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
BAUCHI
Har karfe hudun rana Mom na zaune agidan ita kadai ko kukan kaza bataji balle motsin mutum in that big huge house, ga yunwa ya isheta, ga zazzabi tanaji, wayanta ta dauka tai dialing number Gambo yar aiki amman baya shiga takira yafi sau goma sai chan ga Gambo na kiranta cikin muryanta na yan kauye tace “Hello Hajiya kina jina kauyenmu ba network naga kinmin fulashi, nazo kauyen mu mahaifiyata ba lafiya saita warke zan dawo, ina saman dutse yanzu hak……” katse wayan Mom tayi taja dogon tsaki batasan zata sanar da ita kafin tai tafiya ba kodan taga bata gari, tashi tayi saikuma tai dialing number Fawaz but busy yake nuna mata kaman yayi blocking nata da wayan na shiga daukane bayayi but this time he blocked her, tashi tayi ahankali tafada bayi wanka tayi tafito taciro abaya tasaka tadauki handbag da key motarta tafito compound wani irin ba dadi gidan ke mata yanda babu kowa ciki, tawuce wajen motarta tayi tayi tayi ta kunna yaki kaman battery yamutu makaniken ta takira yace “gashinan zuwa” takoma ta zauna anan compound within 20min sai gasa yazo ya duba motan yace “Hajiya sai taje office mun mata gyara fa dole saina tafi dashi” ijiyan zuciya Mom ta sauke taso tai amfani dashi tace “to zan maka transfer” bonnet yabude yayi tabe tabe motar ta tashi yabude gate yafice yasauko yarufe gate, Mom na zaune a compound din zuciyanta baya mata dadi ko kadan kusan 20min wayanta yahau ringing dasauri takalli screen din makaniken ne dauka tayi tace “Idris yaya”? Hayaniya taji wani yace “gani nayi an rubuta Hajiya motar ta kama da wuta fa anan junction na layin zuma!” Faduwa gaban Mom yayi junction na anguwansu kenan fa dasauri tamike tayi gate tace “me mene?” Bude gate tayi tafito yace “gashinan an cirosa kafansa ya kone amman yana lafiya motar ce dai naci da wuta kan titi” daganan kofar gida Mom ta hango motarta na kamawa da wuta akan titinsu ga jama’a faduwa wayan yayi daga hannunta kirjinta na bugawa bamatasan mezatayiba, da kyar ta duka tadauki wayan tashiga tafiya har zuwa junction kawai ta tsaya turus tana kallon ikon Allah, sosai motanta keci da wuta gabanta sai bugawa yake ita kadai Fawaz yarabu da ita, kare ya cijeta, an barmata gidan ita kadai, yanzu motarta yakama da wuta fushi Allah yake da ita? Amman ai ba ita ta kashe Asmeey ba kuma Allah yasani, tasan yes tai wishing yarinyar ta rasu but da ranta sukabar dakin ai, natural death tayi ai, alhaki ne yafara kamata? Kurmus tana tsaye tana kallo motanta ya cinye ana kashewa baya kasuwa saida ya rage langalangan mota kadai sannan ta mutu Mom kawai ta juya tana tafiya da kyar takoma gida ta shiga ta zauna she needs a car but tanadama kudin siya account nata tabude tanada 2.5 a current bank nata, tanada 1m a savings account nata, sai pension nata na stanbic ibtc bank tanada about 9M.

Ta kashe kudi zuwa kanon nan hotel da car rent da sauransu, she needs a car ga promotion za’a mata yanzu how is she going to get to work tommorow batajin bolt ko uber na aiki a Bauchi ba tashi tayi takoma daki tadebi ruwan zafi a water dispenser ta jefa Lipton tasha tashi tayi takoma watsa maganinta a baki tai salla ta zauna ahaka har 10 nadare, daga baya ta daure taje baya ta watso ruwa ta sa kayan bacci tazo ta kwanta akan gado for the first time in her life takasa kashe wuta tai shiru, mesa yaranta babu wanda yakirata and she know by now kowa yasan meya faru metayi? Aya bata kirata ba, Aysha haka, Munir haka, Yayanta Alhaji Mahmoud haka, koda su yaran suna tsoro da shakkan confronting nata Yaya fa? Mesa bai mata magana ba ai baya tsoronta shi duk ta damu yanda babu wanda ya kulata.
Ahaka bacci yayi awon gaba da ita……

Inyaaaaaaa! Inyaaaaa! Inyaaaaaa! Taji kukan jariri da muryansa da keda bala’in zaki kaman zai yaga mata kunne akanta, gently tashiga bude idanu, duhu tagani ko’ina yayi baki kirin chan saiga wata yar jaririya cikin farin kyalle asama hanging jaririyan tadago kanta idanunta jajir kaman jini takalleta tace “Inyaaaaaa……inyaaaaaaaa” tana kallonta sai taga jaririyan tabude baki harshenta yakoma kaman maciji yayi tsawo daga saman yazo wajenta zai kama wuyanta wani wawan ihu Mom tayi ta tashi zaune daga bacci ahaukace. “Innalillahi wayyo Allah na! Na shiga uku” tashiga tari sosai tana shafa wuyanta da fuskanta tana kallon dakin da ko’ina amman bakomi taji kafanta na zugi, dasauri takalli kafan saitaga bandage din ya futa wajen yazama ciwo sosai ga jini kaman an sosa hannunta ta kalla saitaga jini alamun ita ta sosa maybe cikin bacci dasauri tashiga sauka daga gado tawuce bayi ta kunna tap gaban wash hand basin ta wanke hannunta tadago kanta takalli madubi kawai saitaga Asmeey tsaye abayanta da fararen kaya tana kallonta ihuuuu Mom tayi ta runtse idanu. “Wayyoooo Allah na nashiga uku Innalillahi! Auzubillahi! Bismillahi Rahmani Raheem” tabude idanun ahankali a tsorace ta kalli madubin babu kowa dasauri tajuyo takalli bayanta babu kowa jikinta wani irin rawa yake mata tsoro har cikin zuciyanta, bude kofan tayi tafito tawuce saman kujera tadauki charbinta na wajen tadawo gado ta zauna tana jan charbin tana. “Astagfurullahi lazi! Astagfurullah wa’atubuilaika!” Sai juye juye take tana kallon dakin, baccin dabai kara daukanta kenan ba ahaka gari yawaye bayinma tsoron shiga taji abude tabar kofan tayi wanka tafito ta shirya tabude drawer tacire duka gold nata tanaso ta sayar ta hada kudi tasai mota.

EPISODE 1️⃣1️⃣2️⃣

Batason karamin mota akwai raini batasan yazatayi without a car ba cus is a necessity! Zuba gwalagwalan da akalla ta saida zasu iyakai 50M ajaka ta shirya tsaf tafito ga anguwansu ba’a samu keke ko machine tashiga takawa akasa sai kallonta ake she looks so posh to be walking akafanta kunya kaman zata nutse kasa Tawuce junction bamata ga body motarta ba kawai ta tare keke tashiga tace kotu. Court taje yau take especting official appointment letter na komawanta chief judge hartaga yan cases nata around 2 shiru babu wani letter karshe dai takasa daurewa tawuce office na wani superior haka datake mutunci dashi yace “Hajiya Mrs Turaki” murmushi tayi ta zauna tace “yanaji shiru har yanzu banga letter ba” kofansa ya kalla saikuma yatashi yawuce Mom yadan fita sannan yadawo yazo dab da ita yaduko wajen kunnenta cikin whispering yace “maybe because u are out of town saisa bakiji news ba Muntari Surbajo yabi ta karkshi fa” dasauri Mom ta kallesa ranta na mugun baci, ya gyadamata kai yace “the guy get people on top he work am shi za’a bawa I heard it from a trusted source zakiga email yau, tun rannan namiki kiran duniya sabida kema u should come do your thing but wayanki baya shiga na village u go wat happen to your line ne?” Kasa magana Mom tayi sabida bacinrai tace “ta ina yayi passing requirement na zama chief judge wannan ai yaudara ne da karya” mutumin yace “ahhh u know our work well forget that thing see an riga an basa saidai kiyakuri kawai check ur email sef”dasauri Mom tabude wayanta tashiga email aiko ga message an mata waita yakuri akwai wani basic requirement da sukeso da batada shi so sabida haka an bama a more befitting candidate than her the position of chief judge, Mom saida ta jefar da wayanta akasa tana wani huci kaman macijiya mutumin yace “ahhh calm down Mrs Saraki! Calm down I know it’s painful sunga mace ne ke” yadauki wayan yabata karba tayi kawai tamike tace “sai anjima” tafita bata tabaji ranta yabaci kaman haka ba kuma da an sameta waya datayi yan dabarunta da kyar ta tare keke ta shiga tafada inda zai kaita kasuwa zuwa tayi ta saida zinaren tafito tasake shiga wani keke ga ledan kudi a hannunta sai taka tsantsan take dashi, suna ahaka a keken wasu maza suka tare keken Mai keken na kokarin tsayawa Mom tace “drop na daukeka f……” tsayawa taga yayi batasan meya faruba tadaiga daya daga cikin passenger dasuka tare keken ya hura mata hoda a fuska taji daya yana cewa Oga yace “tasaka jan leshi da abaya wlh itac…..” daganan bata sake jin komiba.

Bude idanu tashigayi kwance taganta akaman police station bayan counter akasa da sauri ta zabura ta tashi macen dake wajen tace “ahh Mrs Saraki kin tashi” dasauri Mom tace “Meya sameni Matter?” Kallonta Matter tayi dan sunsan Mom tace “wasu yan Fulani suka kawoki wai an ganki wasu yan keke napep sun wurgoki a sume”? Arude Mom tace “ina wani bakin leda haka da handbag dina?” Dasauri matter tace “ke kadai ce har agogon da dankunne sun cire miki ke harda takalmi ma just ke kadai aka kawo but we are investigating it” faduwa gaban Mom yashiga yi tace “Innalillahi my gold money! Wayyyooo I need to go to the bank nai blocking account dina please matter bani takalmi da aron 1k”
Mom nabasu cin hanci so matter batai musu ba tabata wani slippers da 1k Mom ta karba tafito aguje mata na binta da kallon tausayi Mom tawuce tahau machine ta tafi gt kafin tai blocking account tace aduba mata wlh an cire duka kudin account dinta tass da atm card nata balance dinta 0 kuma tanada 2m, suma Mom takusan yi aka taru akanta da kyar ta ita bayani akace ta POs suka cire kudin menene menene da kyar Mom na layi ta tafi UBA shima an kwashe yar 1m dinta biyar bata magani yanzu, ba waya bakomi yan zobunan hannunta da agogo da takalmjnta mai tsada an kwashe ina zata fara samun wani kudi da zamatasai waya? “Innalillahi wa innailaihi raji’un!”

Daga jiya zuwa yau Allah is just stripper her off all her privileges one after another! Jama’a muji tsoron Allah! Billahillazi kome kikeda shi bazai hana Allah ya karbe komiba in a second dan shine yabaki! Leave life carefully and avoid cutar dawani, Allah na yafe laifin dakamai but baya yafe laifin dakama wani har sai wanin ya yafemaka.

Wait did u all see how Mom lost everything in matter of hours??? Muje zuwa!
EPISODE 1️⃣1️⃣3️⃣
Chapter 136 · 0% Book details