← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 161

Sashe 130

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune Mamie take a falo tareda Gwaggo da bata dade da tashi ba, da Ammi, da Mama, da Ya Aya, da Ya Aysha kowa yayi zuruuu, Mamie gabanta sai faduwa yake tun fitarsu, wayan Mamie dake kan kujeran ne yafara ringing firgita tayi da faduwan gaba har saida Ammi tace “Ya isa Mamie! Bari na baki wayar”Mika mata wayar Ammi tayi Mamie ta karba ganin Abba ne yasa dasauri tamike tsaye tace “Alhamdulillah Alhamdulilah Babansu Dr ne Allah sa an ganota” kowa yamike tsaye barin Aya da Aya da jikinsu harya fara rawa kafa wayan Mamie tayi a kunne kafin Abba yayi magana tace “anga Asmeey Alhaji?”
Shiru Abba yayi yadan sauke ijiyan zuciya cikin muryansa data dushashe yace “eh an ganta!” Wani hamdala Mamie tayi tace “kai Alhamdulillah anga Asm…..” saita kasa karasa maganan tuna yanda taji muryan Abba tace “meya sameta? Mesa muryanka yayi wani iri”Ijiyan zuciya Abba yasauke yace “Hamidah inaso ki dubi duka mutanen dake gidan nan farawa da tundaka kan mahaifiyata, kece jagora agaresu da karfin su idan kikai breaking down suma haka dan haka ki Dakar da zuciyanki ki saurareni da kyau” Abba yafadi ahankali ahankali
Gaban Mamie na dukan uku uku tabi duka yan dakin ke tsaye ana kallonta harda Gwaggo, wani irin ijiyan zuciya kakkarfa Mamie tasauke tace “ina jinka” gabanta nawani irin faduwa anatse Abba yace “Asma’u tarasu!” Dummmmmm! Haka Mamie taji saukan zancen kaman aradu tai baya zata fadi dasauri Ammi ta tareta Aya ta karbi wayan dasauri tace “Abba nine…..ni…..nine Abba, meya sami kanwata? Abba tell me? What happened to my little sister? Abba wat happened to Asmeey!”Shiru Abba yayi kafin ahankali yace “Asma’u tarasu Aya!” Faduwa wayan yayi daga hannun Aya wayan Mamie ta tarwatse akasa Aysha ta kankame Aya dudda she’s expecting abinda ranta dayaga mata but she’s not believing it tafashe dawani irin kuka tace “wat happened to my sister”? Gwaggo kaman ta haukace tashiga soshe soshe hannayenta na rawa tace “miya sami Asama na? Ku sanar dani” kankame Aysha Aya tayi tace “our little Sister is no more Asmeey tarasu!” “Innalillahi wa innailaihi raji’un!” Haka Mama da Ammi dake rike da Mamie suka fadi at d same time Gwaggo ta sulale tafadi kujera a sume Mama tai kanta tana kuka, Aya kuka Aysha kuka babu mai lallashin wani Mamie in shock ta rirrike hannun Ammi tace “na zalunci yarinyar nan Ammi”
Mamie tawani kalan fashe da kuka tace “shekaran jiya duk kunya kalan na Asma’u saida ta kauda baki dana gayamusu Hamadi yaje chan gidansu ya kwana nan an cika tacemini Mamie dakina bakowa amman dudda haka ban saurareta ba haka na rabasu wallahi harda kukanta rannan, ashe taji ajikinta tafiya zatayi? Mesa nama Asma’u haka? Mesa na zalunceta haka nahanata kebancewa da mijinta? Innalillahi wa innailaihi raji’un how can Asmeey just die? Kodai wasa Abba kenin?”Ahankali Ammi tace “ba’a wasa da mutuwa! Karki kara fadin kin zalunci Asmeey baki mata komi ba banda alkhairi” Mamie takama zuciyanta tace “this is my biggest regret da bazan taba mancewa ba harnima na koma ga Allah! Is this true? Ko mafarki nake? Tayaya Asmeey zata rasu? Innalillahi Wa Innailaihi Raji’un! Yarinyana da kullum nake cikin gidan nan da ita? Banda mai tayani hira sai ita? Idan bamu kitchen tare muna dinning bamu dinning nuna falo muna kallo, I’ve never meet any girl danake so har cikin tsokan zuciyata kaman Asma’u! Yarinya ce mai shiga rai! Mai tausayi! Ga hakuri! Ga kunya! Ga rashin riko! Ga girmama na gaba da ita! Jiya saida ta rungumeni tace Mamie wlh ina sonki Mamie…..”Mamie tafashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya, mai daci mara dadi mai sosa rai dakin nan babu wani mai lallashin wani suna ahaka sukaji karan ana bude gate Aya tafara tashi dagudu tabude kofa tafice sauran suka biyota abaya banda Gwaggo dake a sume ambulance dasuka gani yaşa kawai Aya ta duke ta zuba guiwa biyu akasa Aysha ma haka Mamie tadafa bango tana kara kallon motan.
EPISODE 1️⃣0️⃣2️⃣

Fiffitowa su Abba sukayi ma’aikatan asibitin suka fito suka bude bayan ambulance din yayyin sukai wajen while Abba yawuce gate wajen aminin nasa daya basa yadin likafanin da ganyen magarya yace “sannu Allah ubangiji ya kara hakuri, bari mubada sanarwa ko masallaci in yaso amata salla bayan anyi la’asar tunda yanzu biyu da yan kai” gyadamai kai Abba yayi ahankali yawuce, su Mamie babu wanda ya iya motsawa saukowa Ya Mustapa yayi yana kallon Hamadi dake zaune just like before yana kallon Asmeey bayako kyafta idanu yasauke kanshi saiya dauki Asmeey ahankali yakalli kanninsa yamusu alamu dasu fito da Hamadi, kama Hamad sukayi suka fito dashi kafafun Hamad kaman sun kamu da shan inna as if they were paralyzed bayama iya motsasu kawai kallon Asmeey da Ya Mustapa yadauka yayi suna tafiya su Mamie da sauran matan na kallonsu is like sun kasa yarda that is Asmeey.

Har saida Ya Abdullahi yazo yana rikeda ita kawai saiya wuce falo yayyin suka shigo yakalli Munir yace kuyi clearing kujerun nan waje daya dasauri Yayyin suka shiga aiki aka kawo tabarma aka shimdida kan carpet din Ya Mustapa yasauke Asmeey ahankali dan fuskanta yafito Aya ta duke awajen Aysha ma haka Munir yawani kalan fuzar da iska, Abba yashigo dakin yakalli matan yace “dan girman Allah kudena kukan nan, Mamie ke zaki shirya yarinyar nan ga matan liman nan zuwa ta taimaka kuma is not time for cry kuma Asma’u addu’a” daidai Matan Liman na sallama tana shigowa aka matsa mata Abba yace “me ake bukata Malama Khadija”? Anatse tace “ruwan dumi, bucket, gloves, turare, shi ganyan magaryan da likafani, auduga, sai ku maza zaku fita dan Allah mata kuje kusa lullubi mala’iku na zuwa irin wajen nan” ahankali Abba yasa hannu yadago Ya Aya yace “Aya haka zakiyi? Kece babba fa, wazai lallashi Aysha kalli Munir fa haba Aya! Ina imanin ki” cikin wani irin murya tace “Abba Abba kasan menake ji Innalillahi Abbaaa” tama kasa magana, Mamie ta goge fuska ahankali tace “bari na dauko” tawuce sama anatse tafito musu da hijabai mazan sukakai Gwaggo dakinta Ya Mustapa yamata allura cus she’s sick, Mazan duk suka fice Hamad yakasa motsi hakan yasa aka barsa, wani kalan zama yayi gefen kofan falon kaman mahaukaci, su Mamie kowa yasaka hijabi suka matsa gefe Mamie tadauko komi Ya Musty yayi knocking tazo ta karbi glove a hannunsa takoma tana kallon Asmeey ruwan dumi aka samata ajiki sannan gently Malama Khadija takarbi hannun Asmeey luckily suka sauko Mamie ta dauke tsumman gyalen dake kirjinta sai Mamie taga gudan jini dukansu sukai shiru suna kallo hawaye yacika idanun Mamie, kafin ahankali tasa hannu ta dauka ta ijiye kan tsumman a gefe wani kalan cirema yarinyar kaya suke da ko su basa ganin jikinta balle yan falon, pads dunma aka ciro that are completely soaked da bloody yadawo so bloody ma not like a pad kowa kawai na kuka……

Anatse Hameed yaciro wayarsa ganin yayyinsa kowa yakira matansa ya sanar dasu Ayuba yakira Ayuba ya dauka, muryan Hameed duk ba dadi ahankali yace “can you bring Zee to gidanmu Yubs?” Jin muryansa yasa Ayuba yace “okay but why is ur voice like this?” Dan gyaran murya yayi yace “my brother just lost his wife” Ayuba yace “twin dinka Hamad?” Gyadamai kai yayi yace “yes” Ayuba yace “ohh my god! So sorry Allah jikanta bari naje” ok ya katse wayan, Hameed yayi dialing number Zee harya katse bata dauka ba ana biyu tadaga tace “Hello” dan lumshe idanu yayi murya chan kasa yace “how is your body?” Ahankali tace “Alhamdulillah!” Anatse yace “Asmeey tarasu Zee!” “Innalillahi wa innailaihi raji’un! Baby mene kace!” Zee tafadi hankali tashe, ijiyan zuciya yasauke yace “Ayuba will come pick you up, kibar mutanen dake gidan, kisa hijab har kasa” gyadamai kai tayi tana fashewa da kuka tace “okay” dan tana son Asmeey sosai, Asmeey itace wacce taci burin zama da ita agidan nan cus sauran matan yayin sun girmesu itada Asmeey sune yara….

Almost 30mins aka dauke matan yayyin duk sukazo, saiga Zee itama motansu yayi parking awaje da mutane ke nan karasawa Hameed yayi yabude mata kofan baya ahankali tafito idanunta sunyi jajir suka hada idanu fitowa tayi shima Ayuba yafito gida Hameed yanuna mata da idanu hakan yasa ta shiga ahankali yabita abaya har wajen kofa suka bude an gama yima Asmeey komi fuskanta akadan bari awajen tayi kyau tai haske mai kyau ga auduga a nose nata da kunne, Malama tadan kalli Hamad dake inda yake tun dazu kaman mahaukaci tace “Mijinta Hamadi Mahifinta yan uwanta mahaifiyarta kuzo kumata addu’a kafin arufeta duka” babu wanda ya iya motsi, dayake duk sun shigo, anatse Munir yatako yazo saiya duka yakalli Asmeey yayi wani huci ya dunkule hannuwansa yasake fuzar da iska murya chan kasa yace “I never knew dead could be this painful, Ya Asmeey you are the best Sister I’ve ever had! I’m sorry I couldn’t protect you as much as I should! Allah ya gafarta miki, Allah yabaki aljanna Firdaus, Na yafemiki kome kikamin even though babu abinda kikamin sai alkhairi, Allah yahadamu a Aljannatul Firdaus!” Yan dakin sukace Ameen, yawuce yatafi yana jan rigan jikinsa yadaura kan fuska yana hawaye daya kasa daurewa.
EPISODE 1️⃣0️⃣3️⃣
Chapter 130 · 0% Book details