← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 161

Sashe 73

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Tashi Gwaggo tayi tawuce dinning tadauki indomie ta tawuce dakin dashi tabude kofa tashiga ciki tana kallon Asmeey datahau gadon takifa kanta agadon tana kuka, Gwaggo tace “kiyakuri mana haka lamarin rijalu suke, amman karkija laifinsa haka mata ke binsa kaman zasu cinye, shi ba ruwansa dasu, tashi kici abincin” cikeda masifa Asmeey da Gwaggo takara kılar da ita tace “bazanci ba” Gwaggo takama baki tace “tohhh babban magana ai shikenan daga nazo lallashinki zakihau mini masifa shikenan nayi nan ku karata ke da shi” ta tashi tabude kofan tayi fitowanta tadawo wajensu Faisal ta zauna tana masifa. Faisal yace “dan Allah kona tafi Hameed call me kabani update yanda za’a shirya daga fadan nan” suka wani kashe shida Hameed, Ya Mustapa yamai wani kallo yace “tashi kabar gidan nan lokacin tafiya yayi infact kutashi all of us mutafi hardakai Hameed tashi kabini gidana I need you to do something, Gwaggo kema tashi muje” dasauri Gwaggo ta tashi tana warware mayafi dake kugunta, Hameed na kumburo baki yace “kai Yaya dan Allah nidai ka barni nan, to wazaiga reconciliation din wannan da harda Gwaggo zaka dauka” kunnensa Ya Mustapa yaja yace “kumuje” dukansu ya tattarasu badan sunso ba suka fice, Hamad na tsaye wajen window he’s so nervous yaga Ya Mustapa yadauki Gwaggo da Hameed a motarsa, sukuma su Ya Faisal kowa ya shiga tasa motar sunbar gidan dasauri yawuce kofa yashiga saukowa kasa direct dakin Gwaggo yayi kai tsaye yabude kofa Asmeey na zaune kan gado takifa kanta a kafa tana kuka jin an bude kofa yasa tadago kanta ganin Ya Hamad ne dauke kanta tayi ta tashi azuciye tasauka daga gadon zata wuce bayi taku daya yarike mata hannu wani irin fashewa tayi da kuka zata kwace hannunta tace “ka saken mini hannu ka koma wajen bakuwar ka” tashiga kokawa dashi yaki barinta, Asmeey tace “nace kasaken ka koma wajen bakuwarka data saba zuwa wajenka a kofar gida kuna hira, I don’t want to talk to you ,leave me alone” kin sakin hannunta Hamad yayi yana kallon idanunta yana shafamata hannu kirjinsa na bugawa sosai, yana kallon yanda take kuka idanunta sunyi jazur she’s seems very very hurt, ahankali yace “are you jealous?” Dakatar da kukan datakeyi Asmeey tayi dasauri takallesa da jajayen rinannun idanunta lips nata na rawa tace “jealous?” Itama ta tambayesa cus she’s genuinely confuse, batasan mesa she’s really hurt kirjinta namata zafi sosai ba, to mesa takejin haka? Kasa magana tayi sai kawai ta sauke kanta kasa tashiga kokarin fizge hannunta tace “ni kasaken ka koma, yau baku dade a hiran bane” dayan hannun yakama yarike yana murzawa, ahankali calmly yace “I don’t know her!” Sake fashemai da kuka Asmeey tayi tanason ta kwace hannunta zuciyanta na tafarfasa tace “amman ai tana zuwa maka hira ko”? “the other day nadawo daga masallaci naganta a kofar gidanmu” Hamad yafada trying ya wanke kansa, Asmeey da kishi ya rufe mata idanu tace “metace maka?” Asmeey ta tambayesa cikeda karfin hali dajin zafi, murya chan kasa mai taushi kuma Hamad yace “I can’t remember but I told her I’m married karta kara zuwa” kaman fa wacce she owns him Asmeey tace “toh metazo maka yau”? Lumshe idanu yayi awani irin hankali yace “wallahi ban saniba!” Yanda yamata rantsuwa saitaji zuciyanta yawani yi melting ya karaya it’s shows bayason tai fushi and he cares about her anger, he’s not saying sorry but he seems scared da yanda take fushi, dan rage tone din kukan tayi tace “to mesa kawuce ni kabita bayan nine matarka?” Dan wannan ne yafi cimata zuciya akomi, sosai Hamad ke kallonta, she’s really angry fa, she’s questioning him sosai, no wonder yayinsa sukace he’s done for, is she jealous of him? Ya tambayi kansa, ahankali cikeda muryan lallashi yace “ban bita ba, naje narufe door ne sainaga kin shigo nan” kallonshi takeyi tana making crying face saikuma cikin masifa sosai tace “duk randa wata yarinya tazo gidan nan wajenka duk abinda namata ita taja wlh, saina jijjima mutum ciwo, kuma takara zuwa tagani zata gayamin idan mijina nata ne mayya kawai mai biyo maza gida, classless girl kawai Husband snatcher!” Baitaba ganin Asmeey na masifa ba sai yau, and she looks damn cute, funny as well and lovely ganin akansa take fada haka, dan murmushi yayi karaf akan idanunta fashewa da kuka Asmeey tayi kaman yarinyar dake borin masifa, ashe Asmeey ta iya daru tace “okay I am funny ko? I look funny, murmushi kakeyi” dasauri Hamad ya girgiza kai yace “no nothing is funny My Baby” masifa da kishi yasa bamataji my baby ba, cikin kuka tace “toh why are you smiling? Kadauka da dadi wato tazo gidanmu tana neman mijina? Why are you smiling”? Ahankali yana kallonta sosai yace “you look cute when you’re jealous ne” yayi maganan yakai hannu yadan sosa goshinsa, Asmeey tawani kara kulewa cikin fushi ta fizge hannunta tace “to go and meet that girl tunda I am funny and I am jealous ne” tawani juya fuuuu zatayi kofa da sauri kawai Hamad yarungumota tabaya ya kulle hannuwansa acikinta kaman dan baby murya chan kasa yace “Hussyn Hamad! Don’t punish meeeee!”Shima yayi magana kaman dan baby so sweet, makemai kafada Asmeey tayi zatai magana kawai yawani juyoda ita yafizgota zuwa jikinsa kawai yahada bakinsu, kankarewa taji tayi da gudu ta runtse idanunta, tafiya Hamad yashigayi da ita, kawai suka fada gadon Gwaggo he’s kissing her totally lost kaman wanda wani abu ya shigesa just now, Asmeey na kokarin kwace kanta ahaukace Hamad yakai hannunsa kirjinta zai taba boobs nata dawani iron sauri takulle hannayenta akirjinta ta fizge bakinta tana tashi zaune tajuyamai baya da sauri ta daure hannayenta akirji tana wani irin nishi kaman zuciyanta zai fito, yakai kusan one minute ahaka sannan yataso zaune yazo ta bayanta gently yadaura fuskanta abayanta yana maida ijiyan zuciya just like her yana shakan kamshinta, ahankali yace “wash your face I will bring dankwalinki and shoe let’s go out zaki fita?” Dasauri ta gyadamai kai kirjinta na bugawa, mikewa yayi yasauka daga gadon yawuce kofan Gwaggo saikuma ya kifa kansa jikin kofan yana dan huci so yake gabansa ya kwanta he’s wanting Asmeey sosai! Kusan 2mins yayi sannan yabude kofan yafice ahaka yana addu’a Allah karya fito dako Abba ko Mamie, daki ya shiga yafada bayi sai chan yafito wallet dinsa yadauka da key yawuce yadauki dankwalin kayan data saka dawani black flat shoe da handbag yadauki wayanta yasa aciki ya kashe wutan dakin yasauko kasa yadawo dakin Gwaggo, ta wanke fuskanta tana zaune yana shigowa tasauke kanta kasa, zuwa wajen yayi ya warware dankwalinta yashiga dauramata yau yadanyi kokari simple daura saiya dauki veil dake gadon ya rufa mata yabata handbag karba tayi yamika mata hannu, kin karba tayi ta tashi tana zura takalmin ya kalleta tayi kyau wlh shima haka yana sanye da native farin yard, hannunta yakama suka fito taki yarda su hada idanu, fitowa waje zuwa wajen machine dinsa yana gogewa yana kallonta bata taba hawa machine ba, wayansa yaciro yama Mamie text sun fita sannan yahau kan bike din ya karkato matashi sosai yace “hau” dan kallonsa tayi kafin ahankali takai hannu ta dafasa tahau machine din, kunna machine din yayi yay horn mai gadi yabude musu yaja machine din ahankali yafice mai gadi yabisu da kallo sunyi bala’in kyau!
Wani irin murmushi Asmeey tayi feeling very safe tana bayansa babu wasu mutane anguwansu dayake na masu kudi ne, suka fito suka shiga titi baya wani gudu sosai da ita, wani restaurant mai bala’in kyau yakaita cosmo parking yayi ta sauka ahankali tana dafasa yasauko ga few men awajen kawai saiya rike mata hannu yace let’s go.
Shiga sukayi dakansa yaja mata table tazauna aka kawo musu menu ya karba yabata yace “order” kasa kallonsa tayi ta karba ahankali tana kallo tai jimm kafin ahankali tashiga fadin abinda takeso, tasan baya aiki baida kudin kaman su Ya Hameed, duka abinda tai order was 11,500 Hamad ya karba sai kawai taga yashiga bada order da yawa, jiya he design website for wani an biyasa 150k just last night, even though his plan is yabama Mamie 100k afara sayama Asmeey kayan akwati but he don’t mind spending everything on her now he will work hard again yasami kudin yamata akwati saiti like every other girl.
Wucewa waiter yayi bayan yagama musu placing order, ahankali yasa hannu ya dauki hannunta dasauri ta kallesa saikuma tadan kauda kai murya chan kasa yace “stop being Angry nadinga saka nikaf”? Gyadamai kai tayi yayi murmushi kadan kaman irin masoyan nan sunzo outing, daidai nan aka kawo musu order su, mamaki tayi ganin abubuwan daya musu order harda drinks masu hayaki zuciyanta yayi wani iri dan tasan baida kudi and taga Menu su da tsada abinda tai order was the cheapest one, wucewa waiter yayi, ganin abubuwan daya musu order sai taji zuciyanta yayi wani iri dan tasan baida kudi, he doesn’t have, taji wani tausayi da ya taso ya tsayamata azuciya saitaji kuka yazo mata cus tasan sabida fushin datayi yasa zai kashe kudi haka yakawota nan just to make her happy haka, hawaye ne yasauka daga idanunta dasauri takai bayan hannunta ta share, kallonta Hamad yayi saikuma yataso dasauri yazo dab da ita looking seriously worried ganin she’s still not happy, awani irin hankali yace “Asmeeey” dago idanunta tayi takallesa hawaye sun ciko sosai ga mamakinsa kawai rungumeshi tayi tafashe da kuka ajikinshi mara kara sosai sai jikinta dake rawa wlh ya mugun bata tausayi, murya chan kasa tace “I’m sorry Ya Hamad!! I am making you spend plenty money! Bazan kara fushi ba kayakuri wlh it’s not your fault nasani, I’m sorry” dawani irin sauri yadagota sai kawai yashiga patting back dinta batare daya damu da mutanen wajen ba, issue yadauka nakan table din yakai fuskanta yashiga sharemata yayi murmushi murya kasa kasa yace “waya cemiki u are making me spend? You are my wife I am not even doing enough! You deserve much more than this sabida you are My Queen okay” ahankali yace “I want to be a husband to you just like Annabi Muhammad SAW is to matayensa! Loving! Kind! Helpful! Romantic! Playful and sweet! Don’t think of tommorow! Kudi da arziki na Allah ne! Allah daya bani yau nakawoki nan shizai bani gobe! Have faith in Allah Husnah, I am sure he will give me enough to give matana duk abinda takeso, it’s okay!” Gyadamai kai tayi feeling calm, kalaman shi were so soothing ma zuciyanta, bata tabaji yayi dogon magana hakaba sai yau, sake kallonta Hamad yayi still looking worried yace “don’t cry again, everything here is for u! Idan bai isheki ba akaro, now eat” gyadamai kai tayi tadauki spoon tafaraci just sabida to make him, sai kallonta yake, dan kallonsa tayi tai murmushi kadan ahankali tace “kaima kaci” ijiyan zuciya ya sauke ganin she finally smile, gyadamata kai yayi yadauki spoon yafara ci sunayi suna kallon junansu bini bini just like lovers da basu riga sunyi aure ba.
Chapter 73 · 0% Book details