← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 161

Sashe 141

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana tsaye a airport yana magana da Ya Mustapa awaya ya hangosu, at first only Abba, Baba, and Ya Mustapa yasan zasuzo daga Nigeria saiyaga Hameed, Faisal da Ya Abdullahi, ga Munir tareda su cus sun hadu, dukansu kallon Hamad suke daya rame sosai ga security sa tareda shi da driver motarsa ma ai bazata iya daukansu ba, yakalli driver sa yamai magana yasamo cab ko yakira uber yajuyo duk kunya yakeji, Hameed na zuwa yace “Ango Ango Ango Amarya ta farfado” yawani rungume Hamad daya tureshi yana dan turo baki kunya yacika sa cus hakanan wani extra special kunyan Baba yake, da gangan Hameed yace “Baba surukinka na kunyan ka fa” Baba yayi dan dariya yace “zan ci gidanku Hameed bazaka kyalemin yaro ba taho nan Hamadi” adan kunyace Hamad ya sunnar dakai yace “ina yini Baba, ina yini Abba” kansa Abba yashafa yace “kanacin abinci kuwa?” Gyadamai kai yayi yajuyo yadan kalli Ya Mustapa akunyace sai yadan duka yasa hannu ya karbi jakan hannunsa murya chan kasa yace “welcome Yaya” murmushi kawai Ya Mustapa yayi anatse batare dawani yajisu ba yace “kuka yakare ko? Wife is awake” murmushi yayi mai bala’in kyau cikeda kunya yawuce wajen Faisal da Ya Abdullahi wani kallon iskanci da Faisal yamai yasa yajuya dasauri zai wuce Faisal yarikesa cikin whispering yace “duk ka rame sabida rashin coitus” zokaga dariya mutane dasuke airport ana kallonsu, Ya Abdullahi yace “yana resuming yanzu jikin zai dawo” zokaga dariya barinma Hameed, Abba yace “a airport zamu kwana wai” wucewa Hamad yayi abinsa yabude motarsa Abba da Baba suka shiga, sai wata bus mai kyau ta uber da security sa yasamo su suka shiga harda Ya Mustapa Hamad ma yashigo bayan an gama sa kayan a booth zama kusada Ya Mustapa yayi kansa akasa driver yaja motan sai wasa yake da hannunsa su Ya Abdullahi na surutu abinsu. Ahankali yace “ina Gwaggo”? Ya Mustapa yace “tana sabon gidan da Baba ya saya anan kano tareda Ammi da yara” gyadamai kai yayi yace “Kawu fa ya maida Mama?” Girgizamai kai yayi yace “not yet” shiru Hamad yayi Ya Mustapa yace “wat are the doctors saying about Asmeey?” Ahankali yace “everything is fine kawai physiotherapy ne sabida tafiya and body movement in general” gyadamai kai Ya Mustapa yayi mota na tafiya chan yace “zaka iya daurewa har agama mata physio?” Dawani irin sauri Hamad yakalli Ya Mustapa hada ido sukayi shima kallonsa yake dasauri yamaida kansa kasa Ya Mustapa ya tsaresa kur da idanu, gabaki daya Hamad ya rame ya lalace kana ganinsa kasan harda sha’awa ke neman hallaka sa yakasa magana sai wasa yake da yatsu, anatse Ya Mustapa yace “after tayi physio na today ask them to discharge her and hire wayanda zasu dinga zuwa gida everyday suna mata, ana home service sosai, sannan every week saika dinga kaita hospital din for checkup, take your wife home tayi full recovery adakinta” dan murmushi kadan Hamad yayi wlh yanason Ya Mustapa, Ya Mustapa yakallesa sosai ganin murmushi yake yasa yadauke kai yace “and be gentle na sanka” kifa kansa Hamad yayi a cinyansa dasauri Faisal dake kallonsu tuntuni yace “Ya Doctor wai me kake gayama yaron nan ne yaketa blushing haka yana wani kifa kai a legs” dasauri Hamad yadago kansa, shikuma Ya Mustapa yama Faisal mugun kallo dayasa yace “okay tai tsami zamuji ai” har gidansa sukaje akai parking Ya Mustapa yace “a hotel zamu zauna munyi reservation namu” ahankali Hamad yace “Mamie tamuku girki da daddare sai kuje hotel din” sama suka wuce sai kallon gidan da Hamad yake suke skyscraper apartment suka shiga Hameed yayi wajen Mamie da gudu yace “Mamie na” hakama sauran yaran su Faisal, Faisal yace “Mamie wlh nayi kewanki nazo gidan nan har kunci nakeji banga Mamana ba, tunda na sanki baki taba tafiya kin barmu ba kin dade haka ba” dariya sosai Mamie tayi tace “bagashi ka biyoni ba ga nama” yabude baki tasamai ciki Hameed ma haka Ya Abdullahi ma haka duk girma Ya Mustapa shima yabude baki tasamai takalli Hamad dake falon tace “zonan” tahowa yayi tasamai shima Abba yace “wai yaran nan kunsan ni mijin mahaifiyar ku na nan”

Baba yace “wlh Yaya kagansu fa manyan yara dasu harda likiti duk sun zagaye mahaifiyarsu a kitchen kaman sunyi shekara basu ganta ba” murmushi Mamie tayi tace “ina zuwa barkanku da zuwa” duka yaran tayata daukan kuloli sukayi da plates duk aka kawo falo Mamie ta zauna kusada Abba aka gaisa akaci abinci akai nak sannan akai salla aka fara shirin zuwa asibiti, akwai bathroom a falo akaia ana dakin su Mamie duk wanda Hamad yacema yashiga na dakinsa saiyaki sundai duba dakin an shiga ko’ina an kalla cus yayi kyau but basuyi using bathroom na dakinsa suka shirya tsaf da Hameed da Faisal suka gyara ko’ina harda wanke wanke basu bar any aiki ba sannan suka tafi hospital din.
EPISODE 1️⃣2️⃣0️⃣

Koda suka shigo asibitin Asmeey na wajen physiotherapy har wajen Hamad yakaisu suna kallonta daganan waje yanda take struggling, she can’t walk aka barta ta gwada saitai yunkurin faduwa kaman yara dake koyan tafiya but hannayenta da jaws na fuskanta akwai improvement she’s able to talk yanzu shima bada sauri ba ahankali da natsuwa same with hannunta tana iya moving nasu da sauransu badai sosai ba sai, kafafu shine sai ahankali Munir sai kallonta yake hawaye yacikamai idanu, sannan suka wuce dakin kafin daga baya nurses su kawo Asmeey a wheelchair shiru tayi tana kallon kowa na dakin suma kowa kallonta yake ana murmushi, hawaye taji sunzo mata idanu sosai takalli Munir dashima ke kallonta hawaye sun cikamai idanu, ahankali tashiga daga hannunta dake rawa tamikamai alamun yazo tahowa Munir yayi da sauri sai kawai ya duka agabanta cikeda so yace “Ya Asmeey ya jiki”?Dan dukowa Asmeey tayi awani irin hankali ta rungume Munir tsantsan wani iri Hamad yaji yauma he couldn’t hold it shifa bawai yana kishin Munir bane he knows kaninta ne but shi kawai he wants to be the only person da Asmeey kema hug, Ya Aya tai shiru tana kallon Asmeey, Asmeey na son Munir sosai, da Asmeey ta tashi she didn’t hug her like this but jibi yanda ta rungume Munir, sunkai kusan 2mins ahaka Munir ne ya karbi kansa he’s not a child anymore he’s 20 Asmeey tai aure shima baiso tana hugging nasa haka especially idan mijinta na wurin, share mata fuska yayi yace “stop crying” gyadamai kai tayi Baba yazo wajen yayi cupping face nata yace “Asma’u!” Hawaye en suka sauko daga idanunta Baba yace “ashe zan sake ganinki, stop crying kinji body is going to hurt u again kinji, gyadamai kai tayi Baba yarike hannunta gam yama rasa mezaiyi sai kawai yayi hugging nata yasaketa Abba yace “ya jikin Asmeey kin sami lpy?” Gyadama Baba kai tayi yace “meke miki ciwo yanzu”? Kafafunta ta nunamai Abba yace “zasu dena sannu ko Allah kara sauki” Ya Mustapa yazo wajen zaiyi magana saikuma yaja dan tip na nose dinta yace “how are you Asma’u? Ya jikin?” Akunyace ta gyadamai kai tana mugunjin nauyin Ya Mustapa, Faisal da Ya Abdullahi da Hameed sukazo Hameed yace “saida kika gama samin twin yaci kuka ya gode Allah sannan kika farfado ko”? Dan satan kallon, Hamad tayi dake kallonta shima asace Faisal yace “laaaa shine kike wani satan kallonsa” akunyace ta sunnar da kanta cikeda kunya, Ya Abdullahi yace “ku barta ai ita duk batasan abinda yafaru ba saita warke tass zamu bata labari one by one” ahankali Hameed yace “I’m so glad you’re okay Asmeey” dan kallon Hameed tayi ya gyadamata kai, Ya Faisal yace “welcome back I will take care of you better than before” Ya Abdullahi yace “and we all love you Asmeey” hakanan taji hawaye yazo mata, Mamie tace “kunga zaku sata kuka ko taho kihau gado” ta gungura kujeran takamata suka sata agado ta kwanta tadan saci kallon Hamad shima daidai yana satan kallonta hada ido sukayi, kwata kwata basu samu sunyi magana ba she just wants to hug him raurau tamai da idanu ahankali yadan matso wajen gadon yadan dago kansa karaf suka hada ido da Faisal dasauri yawuce ya zauna itama Asmeey ta lumshe idanu bata wani jimaba sai bacci
Ya Mustapa yakalli Hamad yace “tashi muje muga Doctor” tashi yayi suka fice office na Dr, Ya Mustapa was the one talking nan da man Dr ya yarda yabasu discharge letter but yace subari tayi gobe da safe saisu tafi sannan aka basu contact na care organization dazasuyi contacting su biyasu sabida su dinga zuwa yima Asmeey agida aka rubuta mata magunguna sukaje suka sayo suka dawo dakin.
Chapter 141 · 0% Book details