← Book details Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 161

Sashe 128

Uwa Ko Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tundaga kan Abba, Kawu, Mustapa, Abdullahi, Faisal, Hameed da Hamad dukansu harsu yan sandan juyawa duk sukayi ganin babban mace kan dan yaro dabai wuce su Hamadi ba tsirara while Baba da Munir nawani irin kallon Mom yayi wani baya zai fadi Munir yataresa da sauri hakan yasa Mom ta tashi da sauri gindin Fawaz na fita daga gabanta tawuce dasauri tadauki dogon riga tana sawa shima Fawaz yatashi abala’in rude Mom tashiga juye juye sai kawai tayi wani kofa data gani da gudu Munir yace “zata gudu” yan sandan duka sukayo ciki suka damke Mom da Fawaz dayake Tsirara Hamad yawani shigo azuciye ture yan sandan yayi yawani kama wuyan Mom yana mata wani kallo yace “ina matana?” Wani kallo Mom tamai babu wani alamun tsoro saidai kunya kawai tace “kai har Kanada mata mahaukaci” sakin wuyanta yayi yawani fizge gun na Inspector yasa akan Mom Abba da kowa sukace Hamad! Inspector yace “Hamad calm down let’s handle this properly!” Cikin wata bakan zuciya yana kallon Mom eye cikin eye yace “for the last time Salima! Where is Asma’u?” Sosai Mom ke kallon Hamad gabanta na faduwa sosai ayanda taga idanun yaron wlh he can shoot her and she’s not ready to die now hakan yasa kirjinta na bugawa dar dar tace “she’s in that flat!” Tanuna flat opposite wanda suke ciki Hamad ya jefar da bindigan yajuya da sauri akabi bayansa harda inspector akabar dan sanda data tare da Mom da Asmeey akai flat din, ahankali Hamad yabude kofan flat din wlh wlh abinda yagani yasa kafafunsa suka kasa motsi suka shiga rawa suna karyewa, Asmeey na kwance kan tiles akasa gawani gadon asibiti gawasu karafuna akasa, ga lab coat duk jini, ga hand glove duk jini, ga kaya harda pant apapparke, ga Asmeey kwance cikin jini daya bushi saidai kyalli kyallin danko da jinin yake, Asmeey looks dead, tayi wani irin fari kaman an samata farin hoda dawani dark kalan kore kore, fuskanta wajajen eye balls nata sunyi baki, exactly yanda gawa ke looking, yanda Hamad yayi kasa haka shima Munir da Baba, Kawu ma yakasa motsi, su Hameed ma haka, da kyar Ya Mustapa nawani irin layi yataka yashiga dakin da namijin kokari.
Wajen Asmeey yayi ahankali yaduka yayi kneeling cikin jinin yana kallon yarinyar da babu any breathing sign ajikinta, hannunsa yawani shiga rawa yakaisu yadaura kan hannuwan Asmeey dake kirjinta ta kankame wani tsumma haka daya koma kalan jini yadaura akai, hannunta sanyi kaman kankara, kokarin zare hannun yayi amman hannunwan sun sankare yarinyar ta dade da rasuwa! Awani irin hankali yace “Innalillahi wa innailaihi Raji’un!” Duhu duhu Hamad yafara gani kansa na bubbuga yasoma jin magana sama sama, Abba yayi jarumtar shigowa dakin yazo wajen yace “a’a ina ganin doguwan suma ne Doctor ko”? Yakai hannayensa zai kama na Asmeey dake kirji but hannun yarinyar sun sankare kaman kankara kaman ya fizgo da karfi zasu karye, jikinsa yayi wani kalan mugun sanyi sai yabar hannun, yakai yatsansa wajen hancinta yakara yayi shiru hoping yaji sign na numfashi, babu ko digin numfashi daka fita daga nostril dinta, gabansa nawani irin fadi Abba yadago kanta cus he’s not believing this, ahaka kan yataso asankare in that same position wallahi babu rai jikin Asmeey! Ahankali cikin sanyin muryan dake breaking Abba yace “Innalillahi…….wa Innailaihi…….Ra…..Ra…..Raji’un! Kullu Nafsin Za’ikatul Maut!” Flat! Hamad yazube awajen.

INNALILLAHI WA INNAILAIHI RAJI’UN ASMEEY TA RASU!???

ASMEEY TARASU??

HOW IS HAMAD GOING TO LEAVE WITHOUT ASMEEY? HOW????

TA INA YARON ZAI FARA?!

ALLAHU AKBAR MOM SHIKENAN KINCI BURIN KASHE YARINYAR NAN YAU BURINKI YA CIKA!

GA KI GA FAWAZ MOM!!

I AM REALLY CRYING GUYS😭😭😭
Chapter 128 · 0% Book details