Sashe 87
Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka ringa tafiya shikan sa baisan inda zasu ba, a wata kasuwa suka tsaya, wanda shi kansa baisan wane gari bane, saidaga baya yake jin sunan garin Kano abun da zasu ci yafara tunani dan haka yana ganin ana dako shima yaje yace a taimaka masa, abashi aikin yi zasu siyi abinci, Wani mutumine yaji yabasa tausayi, hakannan ya auko dubu biyar yabasa, yace yaje basai yayi masa dakon ba, Tun daga nan, Baba yake zama a cikin kasuwar, tare da ar sa, kuma har yanzu batadawo daidai ba, kawai dai ta dena sambatun da buge buge, Wajen Satin su uku a haka suna kwana a asan wata rumfar me tebur sai ya nemi yallaye yake rufe musu ciki idan dare yayi zasu kwanta, daga baya kuma sai aka fara ankare wa dasu, wani mutum ya nemi yayi masa lalata a, sai kawai ya tattara ina sa inasa suka bar kasuwar haka sukai ta garari daga can suyi can daga na su koma can, daga arshedai da Baba yaga abun hakane sai kawai ya auke ta suka koma daji da zama, ya ha a musu bukka da komai da zasu ringa amfani dashi, sannan ya ringa shiga daji yana nemo wasu magungunan sai yanzu yake ganin amfanin sanin su, ada sana'ar mahaifin sace amma shi baita a maida hankali akan suba, sai yanzu inda ma Allah ya taimake sa duk ya ri e su, kwaso su yafarayi yana kaiwa cikin gari yana siyar wa, ku in kuma da yake samu sai yaringa siyo musu abinci da abun da yasan zasu bu ata daga baya kuma yama ha a nurhu da kansa yake yi musu abin da zasu ci, A wajen siyar da maganin ne, ya ha u da wa annan yaran su biyu da suka taimake su suka fito dasu, suna ha uwa suka gaisa cikin mutunta juna, sannan suke basa labari sun shiryu sundena wannan harkar, suma duk kusan marayu ne basu san iyayen su, shiyasa suka fa a irin harkar, daga baya kuma suka shiryu, nan suka tambaye sa ina ya koma yagaya musu harkar da yake, nan suka ro ashi shine suka ha a kai gaba ayan su suka koma rayuwar da jin idan zai fito sai su fito tare kowa ya nemi nakan sa, a haka har suka tara ku i suka bu e shago da taimakon wani Alhaji da yabasu jari, Alahamdulillah komai yana tafar musu yanda yakamata, a lo acin ne Bello da Sulaiman suka bu aci Baba da su koma cikin gari subar dajin tunda suna da ku i sai su kama gida..., Amma baba yace a'a sude suje su kama inyaso kullum idan ya fito da ringa ha uwa, babu yanda suka iya dan sunfi son zaman cikin garin akan dajin, badan suna so ba suka bar Baba ar sa suka koma cikin garin inda Baba yabasu shawarar su nemi shaguna biyu me daki a ciki sai sun ringa kwana a ciki sun samu kwanciyar hankali, ganin hakan yasa Baba yace su taya shi bincike akan matar agano masa inda take, Nan suka shiga bincike akan Dadda shi yanayi suma sunayi masa har aka gano inda take da kuma komawar su gidan sarautar duk wani motsin su da labarin gidan babu wanda baya zuwa kunnen Baba, shima kuma yana nemo wani abun da kansa, abun da yasa ya i tona mata asiri kawai saboda yana so sai ya fara gano dalilin da yasa ta za i yi musu haka, kuma ya bari sai ranar da asirin ta ya tonu yasan dole asirin ta ya tono ko bada e ko bajima, shi kuma agun tonuwar asirin zai bayyana kansa yazo ya ara da tashi shai ar, daga nan ya ora musu har zuwa inda ta samu lafiya gaba aya, tun buge tan da Meer yayi da mota tun lo acin yakaita asibiti daga nan kuma akayi mata aikin matsalar ta gaba aya ta dawo normal, Yana gama bada labarin, duk sun fahimce sa, kuma basuga laifin sa ba, saboda daman duk wanda yaga haka indai ba bayani akayi maka ba baza ka ta a yarda ba, uri yabawa Dadda abisa zargin ta dayayi akan rashin sani, daga nan suka cigaba da tattaunawa, sai wajen arfe sha aya na dare sannan kowa ya fara shirin kwanciya, Dadda da Ameesha da maman ta, akace su tafi aki, shikuma Baba su tafi da Abban Ameesha, da farko Abban Ameesha in yarda yayi wai saidai su tafi tare da Norry in sa, akace masa ai bazai yiyu ba, dole sai an ara aura musu aure saidai yayi ha uri nan da sati aya sai a ware musu part insu daban bayan an mayar da auren su, Ba haka suka so ba, dande anfi arfin sune kawai suka yarda daga nan sukayi sallama, kowa ya tafi makwancin sa, asuba ta gari.........., Washe gari tunda wuri duk suka ha u a cikin falon gurin breakfast daga nan kuma aka ha a taro a cikin fada na gabatar da bayyanar matar Abban Ameesha, da kuma mutumin da ya tsinci Sameer tun yana yaro, Kowa ya taya su farin ciki anayi, gwaggwo ma ba abarta a baya ba ta nuna farin cikin ta tsantsa, ga bayyanar ahalin ta gaba aya wansu da kwarkwatar su babu wanda aka rasa, sannan anyi maganin duk wani makiri da mugu dake kusa dasu saidai kuma ayi fatan Allah ya kiyaye gaba, Har aramar walima aka ha a akayi saukar Alqur'ani, aka ci aka sha, sannan akayi sada ka ga mabu atan wajen masu yawa, A cikin sati ayan kamar yanda akace aka mayar da auren Abban Ameesha da Maman Ameesha, inda aka ware musu part in su domin suje suci gaba da soyayyar su daga inda suka tsaya, part biyu akayi su da su Dadda da Baba, ofa ce kawai ta rabasu su da su, Ameesha tana ta murna wai zata koma part in su Maman ta akace mata ai ga nata part in can, suma can zasu koma ita da Meer tunda akayi maganar tayi shiru bata sake magana ba, A ranar da zata koma can akayi rashin sa'a Bossay yakawo ziyara gurin ta, yasamu mummunan labari, bawan Allah harda su suma, koda ya farfa o kam sunbatun ya shigayi akan me yasa za'ayi masa haka bayan ansan shi yake sonta amma shine za'a aura mata, shikenan ancuce sa ankashe shi bazai ta a aure ba, yasan arshen sa yazo mutuwa zaiyi idan bai rayu da ita ba, kuka kam kamar aramin yaro haka yaringa yi, itama kuma anta o mata inda yake mata ayi nan ta shiga daru itama akan sai ansa Meer ya sake ta dan baza ta zauna da shi ba, da suna rufawa juna asiri akan sun sa santa junan su, yau sai asiri ya tonu, kowa saida ya shaida rashin son da basuyi, Dadda da batasan da auren ba daman tace meyasa za'ayiwa jikar ta auren dole to kuwa sai an sake ta tunda bataso, rikici yaso ya alle Dadda itama ta dage sai an sakar mata jika, Sude su Maama Abban Ameesha basu iya cewa komai ba kowa jan bakin sa yayi yai shiru, Papa da yaga yarinyar bata so kuka take kamar ranta zai fita, kuma shi yafi son kwanciyar hankali baya son tashin hankali dan shi tun farko ma yaso yace asoke auren sai kuma yaji ance sun sa santa junan su shiyasa ma kawai tabar maganar sai kuma yanzu yaji aka sun haka, da haka sai yace..... To shikenan indai basa so za'a warware auren dan haka Meer ya sake ta, kowa ta amin ce, Meer yana kan kujera ya ora afa aya kan aya yana danna wayar sa inka kalle sa sai ka rantse baya cikin falon duk wannan abun dake faruwa, ko a jikin sa, Papa ne ya kalle sa yace "babana kaji meke faruwa ko ka sake ta dan Allah ko hankalin ta zai kwanta, kaga yanda take kuka, Ai baba kamar yayi magana da gini, har saida ya kuma yi masa magana, Maama tayi masa, dan itama yanzu ta saduda ta ha ura da auren, baki tasa itama tace "Babana magana ake ma kasa e tan kawai tunda nasan kaima bakaso, kar mushiga ha in ku, Abuu ne yace "Haba Maama wannan wacce irin magana ce kuke yi, ai ba ayi haka ba, ni ina ganin kawai abarsu, idan akace su rabu su suke gaba damu ma kenan, bamu isa muyi musu abu ba suyi mana biyayya ba, "A'a fa Abu kaman ta a yanda ka auro ni ko kamanta nima iyayena basa so na biyo ka, kaga kwa tunda banyuwa nawa biyayya ba, kar kaga laifin wani in ya i yi, daman abun haka yake kama tudeeni tudaan, duk abun da kayi sai anyi maka, duk dani da dalilin su na hanani auren ka, amma duk da haka banyi musu biyayyar ba, tunda akan gaskiya suka hanani dan haka, nima na goyi baya ina ganin kawai kabar kowa ya auri wanda yake so.... Harar ta Abuu yayi hakan yasa tayi shiru tana juyar da kanta gefe, Sai yanzu Meer ya kashe wayar sa tare da mayar da wayar sa, aljihu yana mi ewa tsaye, Cikin isa da ta ama yace "Ni zan wuce, wannan maganar taku ce, lo acin da kuka aura auren jin sa nayi kawai a masallaci, dan haka idan kun yanke shawara, idan anje sallar asuba gobe sai ku sanar da cewa an warware auren da kuka ulla kun aura kuma zaku saki matar, shikenan a wuce wajen, kowa sai ya huta, sai da safen ku yafa a yana ficewa daga cikin falon, dan tafiya sabon part in sa, dan baiga dalilin da zai hanasa komawa ba tunda yagama kai komai nasa can, Kamar ruwa ya shanye su haka suka koma harya fice babu wanda tasamu warin gwiwar dakatar dashi, Abban Ameesha ne yace "shikenan ta faru ta are sai kowa yayi ha uri wanda bazai ha ura ba yakashe kansa, tunda de miji bashi da niyar sakin matar sa, in kuma zaku iya sakin ta kamar yanda yace batare da yawun bakin sa ya furta hakan ba, to bismillah nima de bacci nake ji, Norry muje ko yaja hannun matar sa suka bar galon zuwa nasu