← Book details Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 105

Sashe 36

Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baza ta sake dawowa ba ta tafi har abada dan haka shikuma jinin Muhammad (papa) bazai ta a ci gaba da mulki ba, Shima sai ya yarda da hakan, da tsarin shekarun murabu sa in sarki Salahudeen nayi idan suka sauke sa zasu ora Sameer akai(Sam) tare da matar sa ar gidan Hajjaju,(ina fatan kun fahimci inda zancen ya dosa, dalilin da yasa ake so aha a Sam da ar hajjaju aure, saboda shine Sarkin gaba kuma ta hakan aka ara samun ha in kan sauran duk suka Amince daga baban Sam in har ita hajjajun) Sai gashi abu yana daf da cika burin kowa zai cika sai kuma muka tashi da karyewar asirin da duk mukayi acikin gidan nan lo acin hankalin mu yatashi ganin faruwar hakan, saboda boka yabamu tabbacin duk ranar da jinin gimbiya yataka cikin gidan da afar sa to ranar komai zai karye, saidai kuma nisan yanda zamuyi, to shine ranar da abun yafaru muka fara bincike acikin gidan dan gano wanda ya shigo cikin gidan anan mukayi tozali da wata yarinya mai kama da gimbiya sak, nan muka tabbatar da itace jinin ta, dan haka sai muka saka Abdallah ya ringa ganin duk wani takunta har muka ci sa'a suka fita shopping shine nida Abdallah muka bi bayan su har lo acin da suka arasa inda zasu, sai muka ara kiran wasu yaran mu masu yi mana aiki suka auko ta, suka kawo ta cikin masarauta, Mukuma muka shiga gurin muka gana da manajan gurin muka bashi ku i mai yawa ya goge duk wata auka sannan muka hanasa fa awa kowa idan anzo yin bincike, Daga nan bamu ara ganin yarinyar ba, da muka tambaye ta sai tace taje taga yarinyar kuma tasa a fita da ita daga cikin gidan aje akashe ta, wata il ma ankashe tan, tunda ga nan muka ara kwantar da hankalin mu sannan muka fara tunanin samo wata mafitar bamu samu ba kuma ashirin Fulani ya tonu Hajiya Sarah ta tona mana asiri dan mu ta tonawa ba Fulani ba tunda ita bata san komai ba kawai muna amfani da itane ta yanda koda wani abun zargi yafaru ita za akama, ba wanda zai zargi Ammah, nan akarasa musu labarin har zuwa ranar yau da suke zaune agaban su......., [15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: SARKI SAMEER (DA ZAFI ZAFI) By Yaya Azeema *BOOK* 3 *Ga mai bu atar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da ku inku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number in 08124226526* *_Typing........ 'shiru fadar ta auka kowa da mamaki yake kallon Ammah da ta dur ufar dakai, Babu wanda yasamu damar yin magana saboda al'ajabi yagama kashe su, Meer da ya nuna ayar baiwar yace "saura ke ke kuma nawa akace za abaki, wane aiki kike mata, batare da ta ago ta kalli kowa ba ta jawo mayafin ta ta rufe fuskar ta sannan tace "nima ku ......., Meer ne ya dakatar da ita tare da daka mata tsawa yace ta bu e fuskar ta sannan ta ago ta kalli kowa, kowa ya kalle ta, Cike da jin kunya ta ago da kanta, tana ifta ido tana kallon wani wajen daban, sannan taci gaba da cewa, ni matar anin tace kuma wallahi duk abun da nake bada son raina bane tirsasani akeyi tunda mijina na ya mutu suka koreni daga tasu masarautar tare da yarana saboda suna tunanin wai ni na kasheshi hakabnuke zaune cikin wani hali ni da yara na saboda ni marainiyace auren ma da yar suka bari akayi dande yanaso shiyasa suka bari akayi da yar shima kuma tunda mukayi nake fuskantar abubuwa har Allah ya auki ransa amma sai akace nice shiyasa suka koreni, Ina cikin wannan halin watarana tazo har gidan da nake ta kawo min tayin aiki acikin gidan nan nayi mamaki jin tayin aikin da ta kawo min awata Masarautar da bata su ba kuma itama ba acikin ta take ba, da na tambaye ta dalili sai tace zata gaya min amma ba yanzu ba, yanzu tana so inshiga gidan in fara aiki zata nema min hanya kuma idan nashiga aiki zanyi mata, zata biyani ku i masu yawan gaske nikuma ganin babu abun da nake bana sana'a kuma bansamu wani mijin ba ga kuma halin da nake cikin na uncin rayuwa sai kawai na amince mata duk da banji wane irin aiki zanyi mata ba na yarda da haka, Ko sati aya ba ayi ba na shirya komai a na kuma daman duk maza ne susu biyu sai tace zata sa a kula dasu, ahaka muka rabu dasu ta turo ni gidan tare da wani namiji tace angama komai aiki kawai zan fara duk inda aka bani inkar a zamuyi magana daga baya nace mata to, daga nan nazo nafara aiki a sashen Fulani nake da zuciya aya nake zaune da ita tsakanina da Allah, to saidaga baya kuma lo acin da gimbiya tana da ciki wanda ita kanta gimbiyar batasan tana dashi ba saboda a lo acin gaskiya banji ana cewa tana da ciki ba amma bansan ya akai ita tasan dashi ba, nayi mamaki sosai amma ban nuna mata hakan ba, sai SA'ADATU ta kira ni awaya ta neme ni tace ince zanje gida mahaifiya ta batada lafiya, haka kuwa mukayi na shirya naje na sameta a gida, Da naje sai take ce min aikin da zan mata shine zata bani magani inzubawa gimbiya Sabreenan acikin abun shanta shine kawai aikin da take bu ata idan nayi haka zata baki kyauta mai tsoka sai abun da naza a nake so shi zata ban, nace mata shika ai aikin da zanyi tace, sai kuma nayi wani tunani sai nace mata ai kuma ba a sashen gimbiyar nake aiki ba a sashen Fulani nake, sai tace min eh kar na damu da wannan zata san yanda zatayi za'a mayar da ita sashen, nan dai na ara jefa mata tambaya ta nace badai na mutuwa bane ko dan bazanyi kisan kai ba, sai tace min eh "bana mutuwa bane na tambaya ta meye tace kawai inje inyi abun da tace min, na amsa mata da to saboda a lo acin kwata kwata ban kawo wai na zubar da ciki bane saboda banyi karatun boko ba, ni tunani nama bai kawo ciki ba, Daga nan mukayi sallama da ita tasa aka dawo dani cikin masarautar, bayan kuma na dawo ko sati aya ba ayi ba na fara aiki a angaren gimbiya Sabreenan kamar yanda mukayi da ita haka akai na zuba mata shi a shayi a washe garin ranar ranar kuma da na zuba mata ranar akace bata da lafiya aka tafi da ita asibiti bandai san mai yafaru da ita ba saboda zuwa dare suka dawo kuma lafiyar ta alau shiyasa banyi tunanin ko maganin da nasaka mata bane, Ana haka bayan wasu watannin sai SA'ADATU ta ara kirana taban na ara saka mata, saboda wanccan yautar ku en da tayi min har yaro na ta auki nayin karatun sa sai haka yamin da i dan haka tana ara nema hakan a karo na biyu nayi saurin amincewa nan ma naje na zuba mata, Saida mukayi haka wajen sau uku da ita sannan na an fara fahimtar wani abun da taban maganin sai naje na tambayi wani likita sai yake gaya min na zubar da ciki ne kuma indai aka saba shan sha koda yaushe zai zamana ko ansamu cikin ma zai iya zubewa da kansa saboda abun zai zamewa mutum jiki, Tunda naji haka na dawo gida ina ta tunanin kuma ni abun dake mugun daure min kai har lo acin ban ta a ji ance gimbiya tana da ciki ba to amma kuma mai yasa take bani maganin zubar da ciki inbata, sai nace bari ingwada ta idan ta ani bazan ara saka mata ba, Kamar yanda tasaba kuwa ta ara bani tace insaka mata a abinci wannan karon sai kawai a lo acin na nuna mata rashin yarda ta sai tace idan ban amince ba ko kuma na tona mata asiri sai nayi da nasanin sanin ta sai tasaka gaba aya dangin na cikin tashin hankali, hakan yasa na tsorata na amince mata badan ina so,ta bani maganin kamar yanda muka saba, ni kuma gaskiya tunda naji na meye nayi al awarin bazan ara bata ba, Ko da na koma gida sai na i sakawa idan ta tambaye ni kuma sai ince mata nasaka ni kuma sai inje in zubar dashi, duk sanda taban haka nakeyi, Abun da ya ara bani mamaki ana aukan lo aci bansaka ba, sai naji maganar gimbiya na da ciki hakan yasa na ara tabbatar da na zubewar ciki ne take ban ina saka mata bansan sani ba, Da SA'ADATU taga haka cike da tashin hankali ta kirani nan ta ara bani wani tace wata il wancan ya daina aiki za'a canza da wannan in tabbatar da nasaka mata shi ayau sai na nuna mata zanyi hakan, ina fitowa kuwa na zubar dashi nayi tafiya ta, Da tagadai da gaske cikin ya i zubewa yana ta fitowa kuma ta tabbatar da zubawa ne banyi ba, sai yasa tafara yi min barazana in bansaka ba, nima sai nayi mata, nace wallahi idan bata rabu dani ba sai na tona mata asiri kuma sai nagayawa mahaifiyar ta dan batasan tanayi ba, saidai duk abun da zatayi min tayi min, sai lo acin ta rabu dani da taga haka, shine har aka samu gimbiya ta haifi Sameer na farko shima kuma bayan haihuwar sa da an kwanaki........ Kuka ta fashe dashi taka sa arasawa, duk ido suka zuba mata da mamakin abun da yasata kuka haka, Saida tayi kuka sosai sannan ta tsagaita ta goge hawayen ta tace "kuyi ha uri a kullum na tuna abunnan sai na zubar da hawaye, SA'ADATU bata da imani muguwa ce acikin mugayen azzaluma ce, tsakanina da ita saidai Allah yasaka min, Bayan haihuwar sa tasa aka kamani aka kaini wani waje aka daure ni ga kuma yarana suma tasa aka kawo su agabana
Chapter 36 · 0% Book details