← Book details Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 105

Sashe 59

Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********************** Dadyn Rasheeda, kusan kwana yayi acikin garin Gombe suna neman mutumin, gaba aya ya tashi hankalin ma'aikatan gidan akan sai sunje duk inda yake acikin garin suje su samosa, harda ikirarin inbasu samo sa ba sai ya kashe su gaba ayan su, yar suka gano wa anda suka fita da shi ta hanyar CCTV camera dake bakin titin kusa da gidan tanan sukaga lo acin da mutane suka shiga gidan suka fito dashi suka sakasa amotar su, number motar suka auka sannan ya ara mutane wajen lalubo inda motar take, dan haka tun wajen magariba suka bazama suna neman ta, sai kuma aka ci sa'a suka ha u dasu lo acin da suka fito daga wajen su Ayuba bayan sunkai Abban Ameesha akan hanyar su ta dawowa sukaci karo a hanya aka kamasu...., Sunyi sunyi su fa a musu inda yake amma sun i fa a sai gana musu azaba ake amma har cikin dare basu fa a ba, sai gaba da asuba da suka ga suna daf da rasa ransu aya daga cikin su ya fa i inda yake, sai lo acin aka rabu dasu, sannan suka fara shirin tare da mutanen da suka kama, Washe gari.... yanda Abban Ameesha yaga rana haka yaga dare bai rintsaba ko ka an yana ibada da ro on Allah da mi a godiyar sa ga mahallici, Ana kiran sallar farko ya tashi ya ara yin wasu nafilfilun sannan, da aka kira sallah kuma ya tashi Bossay da Ayuba sukayi alwala suka tafi masallaci, Bayan an idar saida suka zauna gari yafara haske sannan suka fito suka nufi hanyar gida da zunmmar suna zuwa zasu shirya su auki hanya, tundaga nesa suka ga wata motoci a ofar gidan da an mamaki suka tsaya suna kallon motoci biyu dasuke ofar gidan, arasawa sukayi suna shirin shiga kenan saiga Dadyn Ameesha nan yayi saurin fitowa daga motar da fara'ar sa, yana cewa "ashedai kai inne nagani azu da zan tafi masallaci naga kunfito naga kamar kuna sauri shiyasa banyi maka magana ba, nace bari in aka idar ma ha u da na fito kuma sai na rasaku shiyasa nace bari inzo inda naga kafito..... Shima Bossay da fara'ar sa ya arasa tare da tsugunnawa har asa ya gaida shi su Hamza ma duk suka gaidashi, Sannan Bossay ya ora da cewa "Allah sarki ashe da rabon zamu ha u dan wallahi yanzu muke shirin barin garin muma, wani ya en Dady ya kuma saki sannan yace shikenan ma kaga sai mutafi tare wa annan fa bansan suba, ko daman kuna da an uwane anan garin banta a sani ba, kasan nan garin mune babu inda bansani ba, an murmushi Bossay yayi sannan yace "Eh Dady amma mu an shiga daga ciki ka zauna, duk an uwanane, Suna maganar suna arasa shiga cikin gidan, Sauran mutanen da duk suka uya saboda tunkan su Bossay su gansu shi Dady yagan su dan haka da yaga Bossay acikin su gudun yin abun kunya agaban sirikin sa, kuma yana so yagano meye ala arsa da shi da yagan sa agunsu su suka saka a auko sa kokuwa duk yana bu atar amsoshin sa agun Bossay, sai kawai yacewa yaran suyi sauri uya idan kuma sunshiga ciki su fito su kama gaban su kar yafito yaga wani, idan wani abun ya faru zai kirasu kar suyi nisa, suna shiga cikin falon Abban Ameesha bai zauna ba yace to me kuma zasuyi yakamata su tafi ai, Nan suma suka an kintsa jikin su Hamza ya fara shiga wanka, kafin kuma ya fito Bossay ya bawa Dady labarin a gurguje yanda zai fahimta, Yana gama bashi labarin kuwa Dady harda ara gaisawa da Abban Ameesha, cike da nuna alamun tausayi yace "Allah sarki gaskiya ancuceka Allah yasaka maka duk wa anda sukayi maka haka, wallahi bakaga yanda arka ta zama ba ai agida na take aikatau yarinyar tana da matu ar hankali gata kamar ku aya babu inda ta barka har yanayin maganar ku iri aya, Yana an fakar idon sa ya ara cewa 'ai ni iyalina basu ta a gaya min ainahin tarihin suba sundai ce su ka ai suke rayuwar su bayin Allah, bansani ba wallahi da ban bari tayi aiki ba da na taimake ta, Wani iri Abban Ameesha yaji jin arsa wai aikatau take to duk ina ku in da ya barmusu ko kuma cincinye tunda shekarun da yawa, sosai tausayin su yakamasa jikin sa yayi mugun sanyi, Bossay ne yayi saurin canza maganar gudun kar yaje yayo musu arima Abban Ameesha ya fahimci sauran sun mutu ya aga musu hankali tun anan yafiso idan yaje yaji komai, Inda yaci sa'a ma suna cikin haka Hamza yafito da shirin sa tare da an kayan da sukazo dasu Bossay sai yace "ai bama da sai yayi wankan ba su tafi kawai duk dan gudun kada hirar tasu tayi zurfi ya tono wasu abubuwan, dan haka ba ata lo aci suka gama komai suka fito, sai Dady yace "kawai ma su tafi a motar sa tunda shi ka ai ne dan shima yana so ayi wannan aikin ladan dashi ba'a barshi abaya ba dole yaje har inda zasu, To daman Ayuba ba dashi zasuyi tafiyar ba dan mahaifiyar sa na neman sa da gaggawa saboda baigaya mata zuwan nasu ba, dan haka sai kawai yace dasu suje a motar tasa inyaso shi ya biyo su daga baya yana da wata motar, daman haka suka tsara, to Dady ya nemi hakan sai kawai suka amince da hakan suna ganin hakan sai yafi musu sau i ma, akan su tafar masa da mota, Haka suka shiga motar Dadyn Rasheeda a driver site sai yace Abban Ameesha ya shiga gaba, Bossay da Hamza kuma suka shiga baya, ba ata lo aci suka auki hanyar kano........ tunda suka fara tafiya kowa yayi tsit da abun da yake sa awa aransa, gudu kawai suke shararawa daman akan titi sakamakon safiya ce babu kowa akan titin...... Bayan tafiyar su da an minti na Ayuba baibar gidan ba saida ya koma cikin gidan yayi wanka shima sannan ya shirya ya fita daga gidan, a aladai zaiyi wajen minti ashirin haka sanan ya fito, yana cikin tafiya ya tuna da yaransa da sukayi masa aiki yace zai tura musu ku i dan haka sai kawai ya zaro wayar sa daman yana da account number insu yana tafiya duk ya tura musu, sannan ya kira an Ladi dan yagaya masa ya tura musu sannan ya ara yi musu godiya, yana agawa bayan sungaisa ya gaya masa ya tura musu har zai kashe wayar an ladi yayi saurin dakatar da shi, "Sir akwai matsala fa, kai ka ai ne? Ayuba yace "Eh ni ka ai ne me ya faru? Murya asa asa yace "sir kunyi ba azu ko? "Eh, Ayuba ya ara bashi amsa. "Yauwa to wallahi karku yarda dashi shine mutumin da ya auke wannan mutumin da muka kawo muku, tunjiya yakama mu yanzu haka muna wani waje a ulle shine yasa akayi mana duka har saida muka fa i inda kuke, lo acin ma da kuka dawo daga masallaci muna tare dashi da yagankune yace duk mu uya kada wanda ya fito, Saida kuka shiga mutanen sa suka ara kamomu suka kawo mu wani wajen daban yanzu haka muna nan angar amemu a aki wayarnan ma basu san tana jikina ba, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna lillahi wa'inna ilaihi an ladi, waye wannan mutumin shikenan ai yanzu haka duk ma abun da zai musu ya musu dan suntafi kano tare a motar sama suka tafi, Shima Dan Ladi cike da damuwa yashiga yin sallati, yace yanzu dai yanda za'ayi ka kirasu kagaya musu tunkan suyi nisa, dan wallahi mutumin nan bashida imani ko ka an babu abun da bazai iya yi musu ba bakaga yanda yasa akay......, bamm yaji anturo kofa hakan yasa yayi saurin sauke wayar zai oye amma ina anriga angansa da sauri suka wace wayar suka shiga dukan sa dan sunji wata maganar tasa saboda suna kallon sa ta CCTV camera dake akin, Dan haka tuni suka hau dukansa aya kuma yace "bari insanar da Oga...... yafa a yana zaro wayar sa tare da barin akin...... "Hello, hello an ladi an ladi kana jina yanzu kuna ina? kana jina, yana ta magana baima san ankashe ba, saida yazaro wayar yagan ta akashe, kiran number tasa yakuma yi sai yaji an aga.,. Ana agawa yace "Hello kasan unguwar da kuke yanzu kaga yamin zan turo a fito daku ni yanzu zankira su kafin inbi bayan su nasan zan cinmasu dan basu da e da tafiya ba, maimakon yaji muryar an ladi sai kawai yaji ankwashe da dariya tare da cewa muna wajen gidan uwarka ka, ana fa ar haka kuma yaji it ankashe wayar, Ayuba ji yake kamar yayi hauka gefen titin yasamu yayi parking, tare da saurin lalubo number Dadyn Bossay, saboda bashi da ta su gaba ayan su, saidai kuma sau uku yana kira ba'a aga ba, da yaga ma atawa kansa lo aci kawai ya yanke shawarar gwanda ma yabi bayan nasu tun kan lo aci ya ara urewa yanzu dai yasan duk inda suke yanzu basu fita daga garin Gombe ba idan yayi sauri zai iya kamosu.... A 360 ya kwashi motar shima ya auki hanya yana gudun kuma yana ara gwada kiran layin Dadyn Bossay har yanzu kuma ba'a aga ba, gudu yake sosai kamar zai tashi sama haka yake jan motar nan, yana daf zai fita daga garin wata atuwar mota ta tunkaro sa gashi a arin hannun sa take gurin sa take tunkaro wa gadan gadan kuma ta cike hanya amma duk da haka sai yayi ari ya daina gudun yabi gefen ta zai sauka daga kan titin, amma ina kafin yakai ga sauka motar har ta araso kusa dashi tare da dakar gaban motar sa take yafara juyawa aka ara buga masa ya motar ta wuntsila can gefen titin, masu babar motar kuma sukayi tafiyar su, suka barsa agun........ *********************** Gudu suke shararawa suma kamar akan titi dan ba aramin gudu Dadyn Rasheeda yake yi ba, sai gashi tafiyar da zasuyi wajen awa biyar ko shida amma baifi suyi awa hu u ba, Suna cikin tafiyar
Chapter 59 · 0% Book details