Sashe 55
Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koya miki sallama sai ki dawo, Ga mamakin sa sai yaga bata tanka masa ba ta ara tsugunnawa ta auka batare da tace wani abunba, saida ta fita sannan tayi sallamar kamar yanda yake bu ata shikuma bai amsa ba, haka ta ara maimaita wa sannan ya amsa ciki ciki, tashigo ta ajiye masa a inda ta ajiye azu, ta ara juyawa zata tafi, Still sai ya ara cewa "na sallame ki ne, Kai kawai ta girgiza sannan ta koma sai ta tsugunna tafara bu e abincin zata zuba masa saiji tayi yace nasakaki ko nace miki ina son ci, Kai ta girgiza masa sannan ta koma gefe ta tsugunna, Wayar sa ya auka yafara daddanawa amma kuma asan zuciyar sa tunani da mamakin canzawar yarinyar yake, kamar ba itace ba kwanaki tazo ta cikawa da surutu amma yanzu tayi wani sanyi gaba aya ta canza duk abun da yace mata yi take ba wannan taurin kan nata da take nuna masa yanzu batayi, so yake ta kulasa yanda zaiji da in cin mutuncin ta amma ta i kula sa, yana wannan tunanin ya ago ya saci kallon ta, sai yaga tana tsugunne ta zubawa waje aya ido tana ta kallo amma bisa ga dukkan alamu hankalin tama ba agun yake ba idon tane kawai agun, hakan kuma sai ya ara basa mamaki fiye da wanda yake a farko, an gyaran murya ya gwada yi yana kallon ta, ko motsawa batayi ba alamun bataji sa ba, da arfi yace " ke! an furgit tayi ta dawo daga tunanin da takeyi kuma duk da haka bata yarda ta kalle sa ba, e rai yayi yace "watakon na lura dake daga jiya zuwa yau kamar raini ya shiga tsakanina dake ko har inayi miki magana ban isa ki bu i baki kiyi min magana saboda raini kodan kina duba da auren da aka aura shiyasa kike tunanin bari kiyi min abun da kika ga dama, Yanzu ma da sauri ta girgiza masa kai hawaye na shirin fara saukowa daga idon ta, Kawar da kansa yayi yace "kika sake kika min kuka anan sai nasaki me dalili kitashi kishaga ki wanke min toilet sannan kizo ki gyara akin nan daga yau yazama aikin ki tunda kina tunanin ke matar aure ce, to ba da i zakiji ba wahala zaki sha uban da yace kibari a aura auren.., Da sauri ta augo batasan lo acin da tace "nima fa baso nake ba kuma bansan an aura ba me yasa zakayi min wannan fahimtar nuna baso nake ba kuma ai nagaya maka tun jiya kasake ka huta nima in huta dan wallahi naci gaba da zama ahaka zan iya rasa raina saboda bazan ta a iya rayuwa da kai ba, kafi arfina kalar ka daban kalata daban halin mu ba iri aya bane daga jiya zuwa yau ni ka ai nasan halin da na tsinci kaina da zaka taimaka min da ka sauwwa e min tun ba aje ko ina ba na ro eka kasake ni, kuma kama daina wannan tunanin kamar yanda kace wai na rainaka saboda ina tunanin auren dake tsakanin mu, to ko aya bazan ta aukan hakan ba, shigowa ta ma gurin ka bawai dan da son raina bane dole ce tasa nashigo na ajiye maka batare da na tanka maka duk maganganun da kake kawai ina yi maka biyayya ne saboda gudun magana banason abun da zaisa kaci mutunci na ko kamin muguntar da kasaba, amma idan ban kulaka ba sai mu zauna hakan to naga kai kuma duk yanda akayi ma ba'aburgeka sai kayiwa mutum masifa da bala'i, shiru tayi tana goge hawayen da yagama wanke mata fuska, Tana giogewa kuma ta mi e daga gurin cikin sauri ta shige ban akin nasa, tana shiga ta rufo ofar, Yana zaune agun yana jiyo shashshe ar kukan ta a bathroom in domin da ta shiga ban akin guri tasamu kawai ta kama kuka saboda tsabar wani atoton ba in ciki da yake taso mata daga asan zuciyar ta, da ita kanta mamakin hakan take, kawai dan an aura mata aure sai gaba aya rayuwar ta ta nemi canzawa alhalin wanda ka aura mata an uwanta ne, idan kuma tunanin auren Bossay ai shi Meer in yace zai sauke ta taje ta auri duk wanda take so, kuma ko a yanzu bai hanata kula kowa ba, to amma batasan me yasa take jin irin wannan yanayin ba gaba aya batajin ta daidai, ta wani fannin kuma so take ta ha u da tsohon nan hakan kawai taji tana bu atar ganin sa, angaren Meer kam maganganun da Yahaya masa ba aramin tsaya masa arai sukayi ba, karon farko da maganar wata mace macen ma yarinya kamar wannan tagaya masa magana yatsaya yana tunanin maganar ta, gashi daman tun ba yauba ya tsani yaji tace masa mugu, hakan yaji tabasa tausayi, da ace akaran kansane da tuni ya saketa kodan yaga ta dena wannan tunanin akan sa gashi tace tana son wani, da ace yana da yanda zaiyi da sakin nata zaiyi, amma ta zauna yayi tunani kwata kwata bazai ta a sakin taba indai ba su abune suka ha u suka ce yasake taba shine zai sake ta a yanzu dai saidai kuma idan tayi ha uri zai saketa ne daga zaran lo acin da ya ibarwa kansa zai zauna da ita lo aci na cika zai saketan ko da yardar su ko ba yardar su, amma kuma bayaso ya ganta cikin irin wannan yanayin da yaganta yau a kwana aya har ta canza, kuma tabbas zata shiga wani hali kamar yanda ta fa a idan suka cigaba da zama a haka, Sosai ya shiga tunani samowa kansa mafita akan wannan sabon al'amarin da yake neman hanasa sukuni, baita a tunani yarasa mafita irin na yau in, yanke shawarar kiran Khalid yayi dan yazo su tattauna akan yaji ta bakinsa, dan yana bu atar neman shawara dole ya kirasa, Ya mi a hannu zai auki wayar kenan ita kuma ta fito daga bathroom in bayan tagama kukan nata ta wanke ban akin shine ta fito, Fitowar tace tasa yafasa aukan wayar yana kallon ta, ta fara tattare akin, sai kawai yace "zo kifice min daga aki, anjima ki dawo ki gyara idan na fita, Ko uffan bata ce ba kuma bata ara aukan komai ba ta dakata da tattarar da take duk da daman ba wata tattarar arzi i bane dan ba wani datti a akin kawai dai ledojin abarsa da yasaba shane sai wata jaka da ya ajiye ta kan kujera, zata fita yakuma cewa "wazai auke miki wannan tarkacen ko ance miki mayunwaci ne ni, "hmmmm tace aranta kawai ta dawo ta auka ta fice abun ta bata kuma tanka masan ba, Binta yayi da ido har tagama ficewa daga akin sannan ya an jinjina kai tare da dafe kansa, shi kansa yasan bazai ta a canzawa ba kafin fa ta fito yabarwa ransa bazai kuma tanka mata ba har ta fice amma sai gashi daga fitowar ta ya koreta, wayar ya auka ya kira Khalid yana agawa yace "ko me kake kabari kazo yanzu ina son muyi wata magana Please,yana jiyo sa zai fara tsokanar sa kawai ta kashe wayar daman yasan halin sa inbaiyi ba ai ba shi bane, yana ajiye wayar ya ara lulu awa wani dogon tunanin game da sabon lamarin da yake shirin tunkaro sa......, ************************ ____Su Hamza sun araso gidan su Bossay inda suka samu tarba me kyau daga angaren su Ammi, a babban falo suka sauka inda aka baje musu kayayyaki masu yawa itadai Ammi taji da in zuwansu musamman ma Ayuba da akace shi an uwansu ne, Bayan sun gama ciye ciyen su a kwashe kwanukan akan kira duka sauran yaran gaba ayan su suka hallara acikin falon inda Dadyn su Bossay ya ara gabatar da su Ayuba da Hamza agaban sauran yaran sannan aka an basu ta aitaccen bayani game da abun da yafaru, sannan Ayuba ya ora musu da nasa bayanin da kuma bu atar da yazo musu da ita akan zasu koma can gaba ayan su domin su gabatar da kansu acan kowa yasan su yasan dasu, Gaba ayan su sunyi matu farin ciki dajin asalin su, Dadyn su Bossay yace ta amince zasuje in amma za abari a aga masa afa saboda shirye shiryen bikin Bossay da ya riga ya gabato saura kwana shida baikama ta ace sun tafi ba gwara idan akayi ko sati aya ne sai su tarkata har ita amaryar tashi su tafi amma yanzu idan sukaje hankalin su ma duk ba'a guri aya ba kuma bazasu da e ba zasu ara dawowa saboda auren, Sai Ayuba yake cemasa yayi ha uri dai ko susu biyune su fara zuwa ko inyaso sai adawo ayi bikin ko kuma su aga bikin idan komai ya daidai ta sai ayi bikin ma acan, Nan shima Dady yace gaskiya aure ta matso bazaiyiyu ace an aga saba, yanzu dai abun da za'ayi shine kawai su kwana anan inyaso gobe da sassafe sai su shirya dashi Ayuban da Hamza su fara yin gaba inyaso shi ya biyo su daga baya, Duk dai yanda Ayuba yaso yaja ra'ayin Dady ya amince amma ya i yarda dole suka tsaya akan goben zasu tafi su ka Nandai zama ya tashi inda Bossay yaja Hamza ya sauka a akin sa shikuma Ayuba tunda ba sa'ansu bane dady ya ajiye sa a akin sa na angaren ba i, da suka shiga kuma nan suka ara zama Ayuba yana ta basa labarin abubuwan da yasani nagame da masarautar da labarin mahaifin su......, Su Hamza kuma suna aki suma Hamza yana tambayar Bossay wai dama aure za ayi masa, nan Bossay shima yake basa labarin baya son auren yabasa labarin yarinyar gaba aya tun farkon ha uwar su har zuwa yanzu yabasa har labarin yanda yarinyar ta kirasa tagaya masa bata sonsa amma shi baisan meyasa Dadyn sa yana ce sai anyi auren ba, duk da yaji komai, yagama basa labarin cike da inbun damuwa afuskar sa, Hamza yayi mamaki sosai sai yacewa Bossay ya kwantar da hankalin sa zaisa afasa auren indai bayaso amma da shara i sai yafara samun wacce za'a auara masa auren