← Book details Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 105

Sashe 21

Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajen sau goma sannan ya mi e tsaye yafara yayyafa musu akansu, kowa saida yayi masa sau uku sannan ya kwashe da dariya yana zare idanun sa kamar na she an jajawur dasu sunka a kamar jan wai, Komawa yayi inda ya tashi ya zauna ya auko wani jan yalle ya rufa akan wutar atake ta mutu sai kuma gurin ya au haske gaba aya har wajen bukkan saida yayi haske, Cikin wata irin murya mai kama da ta ibliss yace "an gama komai ya kusan zuwa arshe zasu mutu indai kunyi abun da yadace kada ku ara raba kanku, sannan kutabbatar atare zaku watsa wannan abun acikin fadar adaidai kan kujera kowa zai yayyafa da hannun sa, sannan kuje akin ta ku aga gadon ta, ku cusa, wannan adaidai makwan cinta wannan basai kunyi ku duka ba zaku iya tura mutum aya duk yanda zakuyi kuma kar kubari wani yaganku idan kujayi ido hu u da aya daga cikin su to zai warware kuma babu abun da zai hana tonuwar asirin ku amma indai kunyi komai daidai aranar za a ara nemansu arasa kusa da asar ma baza su zauna ba zasuyi nesa daku nesan da bazasu ara dawowa ba har abada, Tsugunnawa sukayi agabansa sukayi masa sujjada sannan suka ago tare da ha a baki sukayi masa godiya, sannan aya daga cikin su yace "to boka Gundur maiyi tu wicinka, idan ka abu yayi kyau, Wata dariyar yasaki sannan yace mungama magana da aya daga cikinku yayi min al awarin ko abu yayi kyau ko baiyi ba, kafin ma kufara agobe nake bu atar ganin ta anan zaku auko min, aljanu suna bu atar jinin ta, dole ma da jinin ta ragowar aikin ku zai kammala yanda yakamata, bai gaya muku ba, Kallon juna suka shiga yi a tsakanin su da sauri waziri ya sunkuyar da kai tare da an gyaran murya yace "agafar ce ni ban sanar daku ba, alo acin da akace yarannan sun dauki komai shiyasa raina ya aci tun kan na sanar daku nazo nafara yi masa magana shine yace zai magana ce mana matsalar mu saboda ina tunanin boka BunGu yace indai asirin nan ya karye shikenan bazai yiyu a arayin wani ba shine hankalina ya tashi na lalubo boka Gundur na sanar dashi abun dake faruwa shine yace zai yimana aikin da muke so amma saidai da shara i sai mun bashi yarinyar jikar Sabreena (Ameesha kenan) saboda jinin ta zai aikin inba hakaba duk asirin da za ayi mata bazai kamata ba saboda tana tare da wani tsari ajikin kuma ankasa gano meye tsarin nata bare ayi maganin sa dole sai ankawota gurinsa komai zai tafi daidai inbahaka zata iya wargaza mana komai, ta hanyar tsarin dake jikin ta, amma idan aka kawota aka fara kawar da ita shikenan komai zai tafi yanda akeso, nikuma na amince masa da hakan kunji yanda mukayi dashi kafin mu ha u anan, Sauke ajiyar zuciya sukayi gaba ayan su saboda atunanin su wani daga cikin su za subayar shiyasa hankalin su ya an tashi, amma jin ba aya daga jinin su bane yasa suka sauke ajiyar zuciya akusan tare, Amma aya daga cikin su sai yace "amma kuna ganin kuma tsarin jikin nata zai bari a auko ta ta cikin sau i babu abun da zai faru? Yafa a yana kallon boka Gundur, e rai bokan yayi yace "bama son tsoro ko wasiwasi a aikin mu babu abun da zai faru kawai kusan yanda zakuyi ku kawota nan, Jinjina kai suka shiga yi tare da cewa shikenan boka godiya muke Allah dai yabamu sa'a kaima zaka ga sakamako mai kyau ko ya kuka ce, Duk suka amsa da kwarai kuwa, Waziri yace "ai ni idan komai yatafi yanda nake so asirina bai tonu ba babu abun da Bazan iya bayar wa ba mutu ar wannan abun da suka auka bai fallasu ba zakayi mamakin irin kyautar da zanyi maka, nandai kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa gun nuna jin da in su ga sabon bokan da suka ha u dashi yau yau innan, Saida bokan ya dakatar dasu sannan suka yi shiru tare da yi masa godiya aya bayan, sannan suka mimmi e tsaye boka yabasu umarnin su fita aya bayan aya, shima idan aya ya fita sai bayan minti biyu wani zai ara fita, ahaka suka fara fita daga gurin, Tunda Meer yaji haka suna shirin fara fitowa yayi saurin barin wajen ya koma bayan wata bishiya dake gurin da haske daga inda yake zuwa inda zasu fito zai iya ganin fuskar kowa, Yana gurin kuwa matar waziri tafara fitowa, aga ciki wayar dake hannun sa ya saita tana fitowa ya danna mata hoto, jin ance sai nan da minti biyu wani zai ara fitowa yasa yayi saurin bin bayan ta, tana cikin tafiyar ya sha eta ta baya zatayi ihu yayi saurin rufe mata baki da hanki ya sha a mata shi a hanci tana sha a ta zube awajen ya auke ta ya koma inda ya uya ya ajiye ta a gefe, yaci gaba da tsayawa agun yana jiran next fitowa, Daga ita sai Waziri shima yayi masa haka suka ringa fitowa, daga ciki aya bayan aya kamar yanda boka yagaya musu sai aya ya da e da tafiya wani yake ara fitowa, Haka Meer ya ringa aukan su a hoto wasu yasan fuskokin su wasu kuma baisan su ba kuma ganin wasu kuma abun ba aramin mamaki yashaba da ganin fuskokin wasun su da yasan su sosai, haka ya dake yaci gaba da aukar su, har saida suka are mutum bakwai ne, cif yana irgasu har suka bar wajen, kowannen su ya nufi inda yabaro, cikin san a, suka koma makwancin su, Saida ya tabbatar da sunyi masa nisa sannan ya nufo hanyar komawa shima mamaki fal ransa, matar Waziri na sa ale akafa ar sa ahaka yataho da ita har ya araso part in ya shige ya koma akin sa, yana shiga ya sauketa a asa yasamu yasamu slatip ya manne mata baki dashi sannan ya aure mata hannuwanta tare da afafun ta, sannan ya auketa ya bu e drower ya danna ta aciki sannan ya rufe harda saka mu ulli ajiki......, Kayan jikin sa ya hau cire wa, sannan ya samu na bacci yasaka, ya koma bakin gadon sa ya zauna tare da jawo system in sa ya kunna ta ya jona wayar sa ajiki ya fara aiki, bashi ya tashi daga gurin ba saida akafara kiraye kirayen sallahr asuba sannan ya tashi ya shiga bathroom yayo wanka ya auro alwala, sannan ya fito ya shinfi a salaya yayi raka'atul fijr saida yajira akayi assalatu sannan ya tashi ya tafi masallaci, Bayan an idar da sallar ya dawo saida ya ara an dube duben a laptop in har gari yafara haske sannan ya samu ya kwanta......, _____papa da Maama ne zaune a aki suna tattaunawa akan batun fulani, Maama ta kalli papa tace "to tunda har ta rantse ba ita bace ai ni banga amfanin rufeta ba tana matsayin matar ka, ni aganina kawai afito da ita, idan wani hukuncin za ayi mata kuma na auko salahuddeen sai ayi mata afito da ita inyaso sai a cigaba da binciken ko ya kace, duk dade har yanzu shiru babu wani labari ko alamar cin nasara sai a fito da ita wata il ma ta hanyarta zamu iya gano wani abun, kaga ance mutuwar daga angaren ta aka fara sanar da ita, dole idan aka nutsu aka bi a hankali zata iya tuna wasu abubuwan da suka faru alo acin sanar da mutuwar, Tana yin shiru papa ya ora da cewa "nima abun da yake ban mamaki kenan tun ranar nake zuba ido ko zan gano wani abun amma shiru, munyi maganar ma tace zatasa a binciko gidan su Wasila (jakadiyar ta kenan) saboda tun lo acin mutuwar ba a ara ganin taba acikin masarautar kuma anrasa inda gidan su yake, Jinjina kai Maama tayi sannan tace "wai ni wama ya kawota da ba asan asalin taba aka kawo min ita duk dade zaman lafiya mukayi da ita tunda nake zaune da ita banta a ganin wata alamar rashin gaskiya ba a tattare da ita ba banta a tunanin za a ha a baki da ita a cutar dani dan lo acin da abun yafaru aka shigo min aki dole tasan da zuwan su tunda tunkan dare yayi sosai a a'ida a irin wannan lo acin tana tare dani bata barina har sai tagama komai taga nayi bacci wataran ma a akin take baccin sai na farka nake tashin ta ta koma akin ta kuma bata da nauyin bacci motsi ka an yana iya tashin ta, amma nayi mamaki tun wajen magriba na kwanta amma bata le o inda nake ba har akazo aka fita dani tace bata sani ba kaga kwa dole da sanin ko suwaye sukayi wannan abun, Papa yace "maganar ki gaskiya ce ai ta inda ma takama kanta barin masarautar da tayi shine babban abun da yasa aka zargeta, daman kuma Waziri ne ya kawo ta kuma Saida ya tabbatar min da cewa yasan ko wacece ita har iyayen tama yasani amma bayan faruwar abun sai ya nemi kowa nata ya rasa ashe ba alkhairi bane ya kawota, tun lo acin akaita nemanta amma ba asamesu ba, Tunda yace Waziri amma take binsa da wani irin kallo mai cike da tarin tambayoyi, amma dai bata nunawa papa ba saikawai tace "Allah sarki Waziri nawa, to Allah ya bayyana su duk inda ta shiga zamu sameta da yardar Allah mudai dage da addu'a kawai itace mafita, "Hakane Allah dai ya ara karemu ya toni asirin duk wani me hannu acikin" cewar papa Maama ta amsa masa " da Ameen" suna akin sukaji ana nocking Maama tace "waye shigo saboda tasan dai ba wani baren bane shiaysa tace a shigo kawai, daga can wajen Ameesha tace bani shigowa tsofaffi ku fito kawai abinci yana jiranku in kuma kuka tsaya zakuga wayam muncinye kuyi sauri dan yunwa nake ji nika ai ma zan iya cinyewa, tayi maganar cike da tsokanar su tana fa a musu haka kuma ta juya ta bar wajen tana dariya..., Suma ga ba ayan
Chapter 21 · 0% Book details