← Book details Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 105

Sashe 43

Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ara cewa, "Lfy qalau " shima ya amsa mata dashi tare da ara yin shiru, Itama kuma sai tayi shirun ta rasa kuma me zatace masa, Jin tayi shiru har tsawon wajen minti 2, sai kawai ya daure yace "baki da abun cewa ne inkashe kin kirani kuma, kinyi min shiru, Azeema ma ana ta angaren ma daurewar kawai take dan ko kiran ma ta gwada kiran sa yafi sau ashirin tana fasawa tun ba yauba sai dai yanzu ta rufe idon ta ta daure ta kirasa, Tana kwance akan gadon ta jin abun da yace yasa ta runtse idon ta, kuma bata san maiyasa takasa katse kiran ba tunda ya riga ya aga, da yar ta bu i baki, tace "uhmm daman akan maganar nanne daka turo min message kace in sameka a mota ni kuma da na fito bangan kaba shine yanzu na kira inji ko maiyasa kace haka, idan da wata maganar sai muyi ta nan, jijjiga kansa yayi jin rainin hankalin da tayi masa maiyasa zatace wai bata gansa ba bayan kuma arya take yana kallon ta ko inda yake ma bata kalla ba tana fitowa ta tafi gurin motar da zasu tafi amma shine yanzu zata raina masa hankali, wani haushin tane ya ara zuwan masa wuya, "Shikenan ai tunda baki zoba a lo acin ai ya wuce sai kije kuci gaba daga inda kuma tsaya, ai bani yakamata ki kiraba kije ki ta kiransa arewa duk inda zaki ku tafi tare har bacci ma kuringa yi tare kar ku rabu da juna arewa daukan ki a mota, sannan dan Allah kar ki ara kirana banaso tunda bani da matsayin da zan miki magana kiji to kije na barki dashi in kirabu dani da abun da yake damuna basai kin ara min da taki ba banaso, Allah yaba ku zaman..., yana kaiwa nan ta bu i baki zatayi masa magana kenan yayi saurin kashe wayar tare da jefar da ita a asa yana jin zuciyar sa na wani irin una, Kwantar da kansa yayi ajikin kujerar yana rufe idon sa, kamar daga sama yajiyo muryar hajiyar sa tana cewa "daman nasan wannan damuwar ba iya ta rasa Sam bace akwai wani abun a asa, ashe sirika tace ta saka min yaro gaba, tana maganar tana arasowa wajen sa sannan ta tsugunna ta auko wayar tare da zama a kusa dashi, e idanun sa yayi tare da gyara zaman sa yana mamakin ya akai tajisa shi yama manta a inda yake da yasani ya koma akin sa, "Haba babana, muryar ta, ta katse masa tunanin sa, tace "haba haba sai kace bana miji ba kai waya gaya maka ana soyayya a haka, ba 'a saurin yanke hukunci cikin fushi, gaya min maiye tsakanin ku kuma mai ya ha aku? shiru yayi na wasu an sakanni sannan ya numfasa da farko yaso oye mata amma daga baya da ya tuna ta riga tasan komai, kuma daman tsakanin sa da ita ba wata oye oye baya iya oye mata komai, tunda aduniyar nan ita ka ai ta rage masa idan da wanda zai iya gayawa damuwarsa bayan ita to saidai Sam su su biyun nan su ka ai yake gayawa damuwarsa to yanzu Sam baya nan dole ita ce wacce zai gayawa abu dake damunsa dashi akaran kansa abun mamaki yake basa baisan ya akai sonta yakamasa haka ba lo aci aya, kuma bai ara tabbatar wa ba sai ranar da yagan su da Hamza, Nan ya gyara zama yafara bata labarin duk wani abu da ya faru tsakanin sa da Azeema amma yana rage wasu abubuwan kamar lo acin da yafara ganin ta a office in sa Salim baya nan har ya alle mata bra, da kuma gurin da ya ri eta a aki har ta fito ta shiga kitchen ya ara binta, har Fulani taso ta kamasu Allah ya taimake su, komai Saida yagaya mata, har lo acin da wannan na arshen yafaru yagan su da Hamza alamun dai suna soyayya tare..., Hajiya yana gama bata labari tasaka masa dariya sannan tace "masa ai ba haka ake soyayya ba wannan ai duk laifin sane tunda batasan yanayi ba kuma bai ta a gaya mata ba to taya zata san yana sonta, idan sonta yake yi ai gaya mata zaiyi sannan tasan dashi amma bai gaya mata ba taya zai ringajin haushinta, nan dai Hajiya ta tsaya da kanta ta nusar dashi kuskuren sa da ora sa a hanya har ta fahimta sannan tace yaje har gidan su ya shawo kanta kuma yabata ha uri in kuma ba hakaba to komai ma zai iya faruwa, yana zaune wani zai aure ta, Ai a lo acin ma yagama fahimtar ta kuma yagano laifin sa, dan haka ko aki bai koma ba yace yanzu zai tafi gidan su, tunda de yasani, gwanda yaje da wuri tun lo aci bai ure masa ba, kar yaje yaji labarin aure bai shirya mutuwa ba, dan idan yarasata ji yake sai ya rasa ransa, Sallama yayi Hajiyar sa sannan ya tafi tana ta tsokanar sa tanayi masa dariya, haka ya fice daga gidan tabi shi da addu'ar samun nasara......., 'yana kan hanyar sa yana tasakin murmushi sai yanzu yagama ashe kansa ya ulle duk baiga abun shiga damuwa ba, akan an wannan abun da bai taka kara ya karya ba, duk laifin sane ma amma yana tafaman jin haushin ta ashe shine ma abun haushin gashi har ta daure ta kirasa amma yayi mata rashin mutunci yanzu kuwa dole yaje ya bata ha uri akan abun da bata sani ba ya hauta da fa a da jin haushin ta, yana daf da arasawa unguwar tasu dan kwana zaiyi kawai sai yaga wata mota tayi kwana, motar kuma kamar dai yasanta, Da sauri yayi rivers ya juya yabi motar, dan yana da tabbacin motar asibitin suce kuma babu wanda yake shiga inba Sam ba, dan haka ya ware yajata da gudu yabita saboda waccen in ma gudu ake, Haka sukaci gaba da tafiya suna tafiya yana bin bayan motar har suka araso kusa da wata unguwa sai yaga motar tafara slow tare da samun guri akayi parking in motar, Tsayawa yayi shima daga an nesa dasu yana hango motar yana jiran mai fitowa, Yana gurin kuwa saiga Sam yafito daga ciki fuskar sa auke da face mask sai p cap Dan badan yayi masa farin sani bana bazai ta a gane saba, yana ganin fitowar sa shima ya fito da sauri ya nufo inda yake, Sam yana fitowa ya zagayo ya bu ewa sumy tare da mi a mata hannu ta ora nata akai tana kallon fuskar sa ta sakar masa murmushi wanda hakan kana gani kasan tsatstsan murmushin auna ne, Shima da murmushin ya mayar mata, yana arasa fito da ita daga ciki, Fuskar sa auke da murmushi idon sa akan ta, yace "yarinyar nan kin raina ni wallahi an kwali yaja riga ko kinsaka ni agaba saida burinki ya cika gashi munzo to kuma wallahi afata afarki tare zamu shiga kuma a haka dan ko sakin hannun ki bazanyi ba, ba ruwana da idon mutane, aramar dariya ta saki tace "wallahi baka isaba muje dai bakin ofa sai ka dawo ka jirani bafa da ewa zanyi ba yanzu zan fito wallahi, (tun bayan barin su gida washe gari ya auke ta ya kaita wani gida ya auko mata wata tsohuwa su ringa kwana tare saboda tsaro badan tsoro ba a an kwana biyun nan da sukayi ba aramar sha uwa sukayi ba har suka ulla soyayya zuwa lo acin kowa ya fahimci yana son an uwansa, duk sun tattara komai da kowa sun ajiye gefe sun rungumi junan su, ba inda suke zuwa soyayyar su kawai suke yanzun ma dalilin fitowar su, itace ta takura musu wai ya kawota gidan wata awar ta zata kar i wani abu yayi yayi da itama tagaya masa mai zata kar a amma ta i gaya masa, Shi kuma sai yace bazai zoba sai ta fa a ita kuma tace bazata gaya masa ba saboda sirri ne, daga nan suka rigayi yace baza su zoba, sai da yar ta shawo kansa tayi masa wayo ta lalla a sa da kalamai, sannan ya yarda suka shirya suka fito tana yi masa kwatance har suka araso) Sam zai yi mata magana kenan saiga shettima ya araso wajen, tare dayin gyaran murya, Juyowa Sam yayi da mamaki yake kallon Shettima dake tsaye agabansa shima yana masa kallon mamaki yana kallon hannun su dake ri e da juna, kallo aya yayi wa sumy yagano ta, amma ita bata gane saba ganin sa yasa ta fara jan hannun ta daga ri on da yayi mata amma sai ya ara ri ewa am, "Malam kallon fa daga ina haka? Sam ne ke yiwa Shettima tamaya da ya tsatsaresu da ido, "Hmmm daga sama nake an rainin hankali kai watakon kana nan hankalin ka kwance kabar mutane acan cikin tashin hankali,sai neman ka ake ka kashe wa mutane waya anrasa inda kake, Sauya kalar fuskar Sam yayi cike da yanayin rashin da i yace "idan an nemeni mai za ayi min, bayan an kore ni to kuma mai zan tsaya inyiwa mutane kaga malam kaima idan ba gaisawa ce ta kawo kaba ka rabu dani dan Allah ina cikin farin cikina kar ka sanya min damuwa ina zaman zama na, "Haba Sam ni kake gayawa haka, koda yake banga laifin ka ba, amma dai koma meye ya kamata ka ajiye komai agefe abun da ya faru ya riga ya faru saboda gida ba lafiya ya kamata ka dawo gida kodan saboda mahaifiyar ka, duk da ta yanke hukunci cikin fushi amma yakamata kayi mata uzuri, ni bata gaya mana ainahin abun da yafaruba kawai dai tace kun samu matsala, tace ka tafi kar ka ara dawowa inda take, to amma tun ka ayi nisa ta gane kuskuren hakan nemanka take kamar me tayi kuka ba adadi, ga kuma babbar matsalar da ta faru acikin gidan, abun ya matu ar cutar da zuciyar ta abun ka tausaya mata ne yanzu tana cikin wani hali babu wanda take bu ata kamar kai tana bu atar ka akusa da ita yakamata ka koma gida Sam, "Shiru
Chapter 43 · 0% Book details