Sashe 11
Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
juyawa ta kallesa, sai kawai ya an sakar mata murmushi ka an yace "yanzu zan dawo, ji yake kamar kar yatafi, kai ta ara aga masa tare da rufe idon ta ta ara komawa yanda take, yar dai ya iya rufe motar ya tafi wani babban shagon sayar da kaya ya shiga, yana shiga ba ata lo aci ya shiga kwaso mata kayan saka dogayen riguna riga da sket harda riga da wando da hijabai, da underwears su panties da bra, duk dai wani abu da yasan zata bu ata saida ya auko mata sannan ya koma kan kayan ciye ciye da su choculate da sauran su abubuwa dai yasiya masu yawa sannan yaje wajen biya ya mi a ATM insa aka ciri ku in aka basa abunsa sannan aka saka masa kayan a leda wasu suka aukar masa sannan suka fita daga gurin har wajen motar aka kaimasa, Hamza na ganin su tunkan su araso ma ya bu e musu booth suka saka masa aciki aka rufe, e motar yayi ya shiga yanda ya barta haka yazo ya same ta ko motsawa batayi ba, Tayar da motar Hamza yayi suka cigaba da tafiya, Sosai ya tsaya yana arewa fuskarta kallo ganin haryanzu bata ce komai ba kuma bata bu e idon ta ba duk da yasan taji shigowar sa, amma bata kulasaba, aramar ledar da ya auko a hannun sa yashigo da ita cikin motar ita ya bu e ya zaro hijabi aciki, ahaka bata motsaba shima kuma baice mata komai ba ya ware hijab in yafara arin saka mata sai alo acin tayi saurin bu e idon ta tana kallon hijab in, kallon ta tamayar kansa sannan ta ara kallon hijab in sai kawai tasa hannu ta kar a ta arasa sakawa, as yayi mata daman kalar da tafi so ya siyo mata maroon colour shikuma baisan shi tafiso ba kawaidai ya aukar mata shi saboda irin shi yafara ganin ta ranar da suka fara ha uwa, shiyasa ya aukar mata kalar, Wani Choculate Biscuit ya auko mata tare da are mata shi ya mi a mata da farko in kar a tayi saida ya watsa mata wani kallo sannan tayi saurin saka hannu ta kar murya can asa asa ta an kallesa tace thanks...., Wani ayatacen murmushi ya ara sakar mata, duk da bata gani ba hakannan yake jin da in godiyar da tayi masa, gashi abun da yake basa mamaki shine yanda ya zuba mata ido yake kallon ta ko iftawa bayayi, angaren ta kuma kallon da yake mata yafara isar ta, sai take jin duk ta takura dashi, gefe tayi da kanta tana kallon waje, ganin inda suke shirin shiga yasa tayi saurin juyowa tana kallon sa, daman shima ita yake kallo dan haka tana juyowa suka ha a ido sai tayi saurin janye nata tare da cewa "naga munzo nan ba gida ba? "Eh nan gidan mune, zan kaiki amma ba yauba, Zata ara magana kenan yace "shiru karkice komai, yafa a yana auke kansa daga gare ta, Itama bata ce inba kamar yanda ya bu ata, amma a asan zuciyar ta tunanin ta shine karfa ya ara kaita inda za a kuma cinzalinta irin gidan da yakaita dan ba aramar wuya suka bata ba duk azabar da umman su Waleed take mata baikai irin wannan ba, ita iyakacin ta duka amma nasu yayi yawa ga aiki ga duka ga zagin cin mutunci, sai taji muguntar gidan su nafilace akan ta gidan da yakaita shiyasa take tsoron kar ya ara kaita inda za' azabtar da ita, duk da taji yace gidan sune amma hakan baisa taji zuciyar ta kwanta ba, so take kawai ta ganta agaban mahaifin ta hakan sai yafiye mata fiye da duk inda zaikaita, Hamza na shiga cikin masarautar Sam yace "yakaisu daidai ofar part in fulani ta yanda suna fito zasu shiga ciki batare da kowa yaga shigar suba, haka kwa yayi ya kaisu daidai ofar shiga sannan yayi parking yana parking in kuma ya bu e motar ya fita yabasu waje, Sam ne ya kalli Sumayya da gaba aya hankalin ta baya jikin ta ya lura bama taga shigowar su ba ta tafi tunani, Hannu yasa ya ri o hancin ta, hakan yasata saurin dawowa daga duniyar tunanin da ta fa "Tunanin me kike ya jefa mata tambaya, kai ta girgiza masa tana kallon cikin gidan ashe har sun tsaya bata saniba, gaban motar ta kalla taga, mejan su ma har ya fita daga motar duk bataji ba tana tunani, ofar yayi ya fita sannan yace itama tafito, da yar ta jawo jikin ta ta matso kusa da murfin sannan ya matsa mata ta fito, Suna fitowa ya riko hannun ta ya bu e kofar da ayan hannun sannan suka shiga ciki, ya mayar da ofar ya rufe, Hamza dake bayansu ya bu e yafara fito da kayan da Sam ya siyo mata sannan ya bisu dashi ciki, Yana shiga ya wuce angaren Sam, abakin ofar ta tsaya ya kwan wasa jin shiru yasa ya tura kofar ya shiga kaitsaye, Basa cikin falon sai kawai ya ajiye kayayyakin afalo sannan yajuya yabar falon, Saida Sam ya shiga da ita akin sannan ya sakar mata hannu kan gado ya nuna mata yace ta zauna, shikuma ya wuce bathroom, shiga yayi ya ha a mata ruwan wanka me zafi sannan ya fito yace "taje tayi wanka, "To tace masa saboda daman a bu ace take da son yin wankan saboda yau kwanan kwanan ta wajen hu u batayi ba tunda taje gidan batayi wanka ba, sun hanata yi, Ahaka yanda take ta tashi ta nufi ban akin, da kallo kawai yabita baice mata komai ba, saboda bayaso ya takura mata, fita yayi daga akin, yana fita ya tadda kayan afalon sai kawai ya auka ya shigar dasu akin, ware su ya shiga yi sannan ya auko mata wasu riga da sket da wata hula harda pant da bra, ya ajiye mata su akan gado, sauran kuma ya ha e su ahaka ya bu e wardrobe in sa yasaka su ya rufe, sannan ya ara fita kitchen insa ya shiga ya auko plate sannan ya bu e frigh ya auko holandiya me sanyi sosai tare cup sannan ya koma akin har lo acin bata fitoba, Mamakine yakamasa ganin irin da ewar da tayi, tunani yashiga yi kodai ba lafiya ba, akin ya nufa yana zuwa yakara kunnen sa yanaso yaji da motsi ko ba motsi, saidai kuma yana kara kunnen nasa, ita kuma tana bu ofar, da sauri tayi baya cike da tsoro tare da sakin aramin ihu, shima saida saida ya an tsoratan yanda tayi masane yasa ya tsorata, Ajiyar zuciya ta sauke tana tace "wlh ka tsoratani, "Sorry naji shirun yayi yawane shiyasa nabiyo inji ko lafiya, yana gama fa ar haka kuma yayi baya dan yabata damar fitowa, Fitowa tayi tana faman sunnar dakai duk da hijabi ne ajikin ta amma sai kunya ta kamata, bakin gado ya zauna yana jiran arasowar ta, tana arasowa ya auki kayan ya nuna mata kayan yace gashi sai kisaka aukar su tayi sannan ta juya zata bar wajen "yace ina zaki? Tace "shiryawa zanje inyi, ewa tsaye yayi yace "kiyi sauri kishirya, sannan ya fita waje, Yana fita tacire hijab in sannan ta auki bra in tunkan tasaka take mamakin yanda akai ya auko size in tana sakawa kuwa tayi mata cas kamar ya gwada ko tagaya masa size in da take sakawa, pant inma daidan ta, haka kayan ma komai daidai ita, saida tagama sakawa sannan ta auki towel in data cire ta aure gashin ta da tawanke shiyasa ma ta da e saida ta ware kalbar kanta ta wanke kan, Tana cikin tsane kannata ya shigo ciki, bakinsa auke da sallama amsa masa tayi tana cigaba da goge ruwan kannata, arasowa yayi gaban ta yana ganin abun da take yasa hannu ya kar i towel in, ya ajiye sa gefe yace "akwai draya gata can, yafa a yana nuna mata inda take, tare sukaje gurin, zatayi da kanta ma yayi saurin karba ya busar mata dashi ya gyara mata kan kamar mace harda yi mata oiling sannan ya aure mata shi da wani zare saboda babu reboon akanta shima kuma basiyo mata ba, Dawo da ita bakin gadon abubuwan da ya shigo dasu ya dawo dasu gabanta ya ware ledar snaks in ciki ya zuba a plate in ya zuba mata holandiyan aciki, sannan yace ta sauko asa, Ba musu ta sauko ta zauna duk abun da yace mata yi take takasa yi masa musu, Hannu tasa zata ci ya dakatar da ita ya auko zai bata ta girgiza masa kai tare da cewa "nagode amma kabarni zanci da kaina, rabuwa yayi da ita, Yana gurin zaune a gabanta har tagama ci tace masa ta oshi, said a ya tabbatar ta oshin sannan ya ha e kayan, ya fita dasu ya dawo, kan kujerar akin ya koma ya zauna yace itama ta dawo ta zauna ba musu ta tashi ta dawo ta zauna gefen sa, tare da sunkuyar da kanta asa, tana kallon yatsun hannun ta ranta cike da tambayoyi, Gyara zaman sa yayi yana facing inta da kyau yace "kibani hankalin nan, itama juyowa tayi tana kallon nasa, cike da ha o duk wata nutsuwar ta gare sa, an gyaran murya yayi sannan yace "ko bantambaya ba nasan abun da yafaru dake agidan da nakaiki ina mai baki ha uri nima bansan haka zai faru ba banta a tunanin halinta haka yake ba anwar kaka tace, yanda na auki Ammah haka na auke ta bansan muguwa bace banyi haka dan na cutar da rayuwar kiba na auko kine dan na taimaka miki kiyi ha uri da duk abun da sukayi miki kuma nayi miki al awari zan ramamiki duk abun da sukayi miki babu wanda zan yale daga cikin su, kigaya min duk abubuwan da sukayi miki, Amma kafin inji abun da sukayi miki inason kifara bani labarin ki kuma ina mahaifiyar ki take nasan matar da naganki da ita ba itace ta haife kiba, kuma shi mahaifinki baya aukan mataki akan abun da take ne ko kuma shima bashi ya haife kiba, shiru tayi na an wasu lo