Sashe 68
Sarki Sameer Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wanda yagansa ya fice daga gidan ma gaba aya, sakamakon kiran da a Khalid ya kirasa, ......., [15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: SARKI SAMEER (DA ZAFI ZAFI) By Yaya Azeema *BOOK* 3 *Ga mai bu atar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da ku inku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number in 08124226526* *_Typing........ 41_* ...........Tun adaren jiya su Dadyn Bossay suka dira a garin kano inda direct suka wuce da Ayuba asibitin su Sam, cikin mawuyacin hali, Nan danan lokitoci suka rafar masa aka fara basa taimakon gaggawa, dan halin da yake ciki yana daf da rasa ransa, Koda gari ya waye ma bai farfa o ba, sun rasa gane kansa, Saida Meer ya shiga gurin da aka kwamtar da shi ya shiga yi masa nasa duban, amma har gari yafara haske bai Ayuba, bai farfa o ba, amma dai ansamo kan matsalar walwar sa ce ta bugu inda ake sa ran koda ya farfa o ba lalle bane ya farfa o cikin hankalin sa zai iya samun wata matsalar daban......, Cikin masarauta kam da wajen ta, maganar bayyanar Abban Ameesha ta gama bazuwa wasu na ta zuwa suna ganin sa, an cikin masarautar kam kowa sai kulawa ta musamman ake basa, Ameesha ma, zuwa yanzu ta an saki jikin ta, tana gurin su Amra ma, suna hira tare da Azeema da tunda taji labari ta iso gidan tundan domin taya awar ta murnar bayyanar mahaifin ta, suna zaune harda sumy da har yanzu bata koma gida ba, itama saboda momma ta hanata tafiya, Fulani kam saboda farin cikin ganin Abban Ameesha, kunsan ta zauna da shi tana matu ar sonsa, saboda shima, take son Sam har ta dawo dashi part in ta yake zama, saboda ta rasa, Abban Ameesha, dan a lo acin ma kusan kullum yana gurin ta saboda soyayyar da take nuna masa, To har yanzu soyayyar tana nan dan haka ta ro i Allah Annabi ya dawo part in ta, da zama zata basa kulawa marar misaltuwa dan bataso ya ara nesa da ita, yanda take jin aunar sa aranta, ji take kamar ita ta haife sa, Ba jayayya kuwa Maama ta kuma aminta da ita akaro na biyu, shima kuma Abban Ameesha, ya yarda saboda yanda yaga tana nuna yanda take son sa sai yaji shima matar ta kwanta masa ya amince zai koma, daman akuna biyu ne aciki, daga na Sam sai extra bayan nata da take dashi a can ciki, Nan ta au al awarin zata sa a canza masa komai na akin ya fa i kalar da yake so, Su Dadda da Maama suna cike da farin cikin tarkon da suka ha awa musu, kuma nan suka sake yanke shawarar nan da sati aya zasu tattara su a ware musu part in su daban, koda gina musu ne, sai ayi, sai kuma Papa ma yace kawai za'a kwashe kayan part in Ammah dai su kuma can, tunda yanzu babu kowa aciki, Su Maama kam sunji da in hakan, tun aranar suka fara shirye shiryen yanda za a fara gyaran part in, a ranar wunin dai wuni sukayi suna hira, amma ba Meer dan har yanzu bai dawo ba, ita kuma Ameesha tana can part in su Amra, Amma sauran duk suna tare, Fulani, Dadda, Papa, Maama, ummy, Abuu, sai Abban Ameesha da suka saka a tsakiya, kowa yana kallon sa cike da so da auna...... labarin Ayuba baizo musu ba sai can da yamma Sam ya dawo cikin masarautar yake sanar dasu duk abun dake faruwa da accident in da Ayuba yasamu, dan duk atunanin su accident yayi ba bugesa akayi ba, anan shima yake jin labarin bayyanar Abban Ameesha, ya nuna farin cikin sa sosai, Bayan anyi sallar magriba suka tattara gaba aya suka je suka duba sa, har zuwa lo acin bai farfa o ba, .........Wuni guda da Meer ya fita suna tare da Khalid amma hakan nan sai ya tsinci kansa da kasa basa labarin abun da yafaru tsakanin sa da Ameesha amma lo aci zuwa lo aci takan fa o masa arai da tuna moment in su na daren jiya, A gidan da suka ajiye mutanen da suka kamo lo acin da ya tura su Ameesha nan, yaje ya ara lugudar su tare da sawa aka tura su can police station in su Khalid, Tare da Khalid suka tafi shikuma ya tsaya a gidan bai bisu ba, Mutane biyun kuma da ya kamo daga gidan su Rasheeda yaran Dady, su kuma yaja su wani aki suka tattauna game da abun da suka sani akan sa, amma ga mamakin sa sai suka ce masa kawaidai idan arsa tana son wani abun ko kuma wani abun yasamu arsa, ko kuma idan yana son akawo masa wani, to sai suje su auko masa, shikenan aikin da suke masa, amma dai suma kansu sunsan da abun da yake yi marar kyau kuma yana da wasu yaran bayan su, wanda su kuma basu san aikin da suke masa ba, Nan Meer yace zai basu aiki su koma gidan nasa sannan su saka masa ido akan duk wani shige da ficen sa, sannan duk yanda za suyi yanaso su kawo masa wayar sa, zaiyi bincike a ciki, musamman awa an nan an kwanakin yafiso su kula dashi sosai, suga inda zaije da inda yake zuwa, Nan suma sukayi masa al awarin in Allah ya yarda zasu kawo masa, wannan abune mai sau i agurin su, sudai burin su kar ya cutar dasu yasa kuma a ulle su, Daga nan Meer ya fito daga tare da su suka wuce can gidan su Rasheeda in shi kuma ya nufi gida, yana kan hanya, Abuu ya kira sa yana tambayar sa ina yake yace yana kan hanyar dawowa gida, Yace to yayi sauri ya dawo Uncle in sa yana kiran sa, sai tambayar sa, yake nan yace gashi nan yanzu zai araso, Yana cikin tafiya yashigo cikin wata unguwa bayan yasha kwana yana hawa kan titi sai kawai yaga gifatawar wannan tsohon da ya ta a gani akan mashin shi kuma ya shiga wani lungu, Da sauri ya taka birki tare da karya kwana yabi inda yaga tsohon yayi, amma abun mamaki sai yaga baigan saba, tafiya yaci gaba da yi amma sai yaga hanyar ta rabe biyu tunanin hanyar da zaibi ya tsaya yi, sai kawai ya yanke shawara yabi wata, sai yaga layin bama ya fita, dawowa yayi yabi ayan layin, baiyi nisa ba yaci karo da wani mashin in a fake a gaban wani shago, daga inda yake yayi parking in motar ya fito, ya nufi wajen, Yana zuwa yayi sallama cikin shagon a tunanin sa ko zaigan sa acikin amma sai yaga wayam, Mutumin cikin shagon ne yace malam lafiya me za'a baka, kallon sa Meer yayi kasa e kamar bazaiyi magana ba, sai kuma yace wani tsoho nake nema wanda yayi parking in wannan mashin an le owa mutumin yayi yana le en mashin in tare da fitowa daga falon yana cike da rashin fahimta, yace wannan mashin in ai nawane babu wanda yayi parking in sa yanzu, Wata uwar harara Meer ya jefe masa batare da yace koma ba, Tuni kuwa cikin bawan Allah nan ya uri ruwa dan ya tsorata da irin kallon da yaga Meer yana binsa dashi, Cike da tsoro mutumin ya ha iyi yawu a boye, yana muzurai ido yace "gaskiya na gaya maka wanann mashin in nawa ne ba nawani bane, idan kuma baka yarda ba bari inkira maka wani anan shagon ka tambaye sa kaji yana fa a yana shirin juyawa ya zaije shagon dake gefan sa, Hannu Meer yasa ya dawo dashi baya, yana dawo dashi ya aga hannu ya kira masa mari, tare da nuna sa da yatsa yace "kar ka nemi ka ata min lo aci ranka zaiyi mummunan aci, ka gaya min gaskiya ina mutumin nan yake, Kuka bawan Allahn nan ya fashe dashi yana dafe gurin da aka mare sa, yace "nifa bansan wanda kake magana akai ba na gaya maka wannan mashin ina ne,yana maganar yana goge hawayen fuskar sa, yana fa ar haka ya aga murya yace "Sulaiman! Sulaiman!! yakira sunan sa cike da rauni da muryar kuka, Daga can cikin shagon na ciki ga amsa da "Na'am Bello, ya amsa tare da fitowa da sauri jin muryar ma ocin nasa ba kamar yanda yasaba jin ta, Yana fitowa yaga abun dake faruwa ya tako da sauri yazo gurin yana kallon yace "Bello me yake faruwa naganka kana kuka, bawan Allah me yake faruwa, yafa a yana maida kallon sa kan Meer, Cike da tsananin damuwa wanda aka kira da Bello yace "Sulaiman dan Allah wannan mashin in waye, Da mamakin tambayar da game masa yake kallon sa sannan yace "kamar ya wannan wace irin tambaya ce naka ne mana, ko haka akace na wanine, "Eh gashin nan kagaya masa yazo ya sameni kawai yace wai sai na fito masa da wanda yayi parking in mashin in yake, nace masa ni babu wanda yazo shago na, mashin kuma nawa ne amma ya i yarda shine harda su marina, ya ara sa maganar cike da ta aicin marin da akayi masa, "Allah sarki, bawan Allah wannan mashin in sane nima kuma ina cikin shagon nan banji arar wani mashin ba, da sai ince maka, ko wani mashin in kake tunanin ya biyo ta nan, amma wannan muna tare babu wanda yazo, in kuma baka yarda ba, mushi ga ciki ka duba cikin shagon ka gani, "Muje, Meer yafa a yanayin gaba, Kallon kallon suka shiga yi a tsakanin su, cike da fargaba, da tashin hankalin abun da zai faru, cikin su duk ya uri ruwa basu ta a tunanin zai iya cewa suje ya duba ba, sun auka idan suka gaya masa haka zai ha ura ya juya, Saboda tsoro duk sun kasa aga afa su bishi, har saida Meer ya juyo yace "me kuka tsaya yi to, har suna gware wajen juyawa suka shiga tafiya da sauri wanda aka kira da Sulaiman yana cewa "a'a