← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 106

Sashe 96

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Malam Kalla!."Ta na faɗa ta juya da rarrafe hannunta da takalmanta ta ci gaba da rarrafawa tana fatan Allah sa dai muyane gidan sun falka daga suman dolen da ta saka su wanda ga shi ita kanta ba ta samu biyan buƙata ba. Sai da ta ɗan yi tafiya sannan ta je kusa da wani bangon jikin wani gida ta dafa ta miƙe tsaye har lokacin gabanta yana dukan lugude tsabar faɗuwar da yake. Haka ta samu ta lallaɓa gida tana jin jikinta kamar an cire mata ƙarfi kwata -kwata, dakyar ta shiga ta yi wanka shi ma ruwa kawai ta kwara babu nutsuwar yi da sabulu kasancewar tana tsoron Abba ya dawo ya ganta da kaya a jiƙe ga shi har da ƴat guntuwar gudawarta da ta saki a cikin kayan. Alwala ta yi ta koma ta zauna hat lokacin gananta yana faɗuwa. Tana jin yadda wayarta take ta ruri amma ta kwanta lifet a kan tabarta tana jin yadda har lokacin ƙirjinta yake fat-fat. Ta san kuma ba kowa ne mai wannan kiran ba sai Aliya za ta dame ta ita kuma yanzu ita kanta ba ta da nutsuwar yawan surutu, don gabaɗaya a firgice take fatan ta Allah sa ta iya yaƙi da zuciyarta kar Abba ya gano a halin da take cjki.

Ta jima a kwance tana ta jan lahaula wala quwwata illah billahi aliyal azim. Don daga ta rufe idanunta sai ta ga Malam Kalla ta rasa yadda za a yi ta daina jin bugun zuciyarta yana tsananta tana tsoron kar wani ciwon ya kama ta sanadin yawan firgicin nan..

A can gidan Malam Kalla kuwa Umma tana ambaton sunansa sai kowa ya tashi daga gajeran suman da ya yi, haka aka ci gaba da koke-koke tamkar babu wanda ya suma to kowa ma ya manta abin da ya faru, su Abba ma haka suka jajanta wa iyalan nasa tare da masa addu,a suka fito suka nufi masallacin don yin sallar isha,i.

Umma tana nan yashe a kan tabarma, jin wayarta ba za ta bari ta huta ba ta tashi tsaye za ta ɗakko wayar ta amsa, wani bugar jikin ƙofar gidan da aka yi hankali tashe Umma ta yi cikin ɗakin zaninta da ya suɓuce ya faɗo ko ta kansa ba ta bi ba haka ta yi cikin ɗaki daga ita sai ƙaramin siket da ake sakawa a ciki. Ko da ta shige ɗakin a guje ta banko ta saka sakata ta jimgina bayanta da jikin ƙofar tana numfarfashi. Tunanin ta ko Malam Kallan ne ya sake biyo ra har gida idan haka ne har ta fara tunanin yau sai dai bango ya tsage ta shige!.

Barar da almajirin ya fara rafkawa a tsakar gidan, shi ya ankarar da Umma almajiri ne ya bugi ƙofar. Wani wawan tsaki Umma ta ja tana mai tashi tsaye ta buɗe ƙofar ta fito tsakar gidan tana luƙawa almajirin zagi wai duk ya kasa bara a bakin ƙofa sai ya zo yana bugar ƙoga kamar za a yi yaƙi.

Susum almajirin ya fice daga gidan, ita kuma ta hau masifa tare da sunkuyawa ta É—auki zaninta a fili tana cewa

"Wannan ai shashanci ne ka zo ka ruɗawa mutane ciki, dama ni da nake a ruɗe ka zo ka ƙara ruɗani nake tsere ni kaɗai a tsakar gida, har ina yada zani wallahi ka ɗauki alhakina" Ta faɗa tana ɗaukan zanin ta ɗaura, daidai na kiran ya sake shigowa a fusace ta ɗauki wayar don haushin Aliya take ji ba ta san irin rijiyar da ta tsallake ba, rijiya mai gaba miilyan ma ba gaba dubu ba. Ɗagawa ta yi sai kuwa ta ji Aliya tana faɗin

"Umma aka ce Malam Kalla na unguwar nan ya rasu, ina ta kiran ki in ce ki shirya rangaɗaɗau ki je ki ɗura masa aganin nan a hanci ko kakarmu ta yanke saƙ... Ba ta ƙarasa ba Umma ta ce

"Aliya na je gidan Malam kalla"

Aliya ba ta gama.jin ba,asi ba ta carara uwar guÉ—a don tunaninta aiki ya kammala. Umma kuma tsabar takaici sai ta kasa magana sai da ta gama guÉ—a da ife-ife ta ce
"Allah ne kaɗai ya aan karatun kurma Umma, a yau ba sai gobe ba zan nemi takardar saki a wajen Kasim, ni ba don mutane ƴan sanya ido ba da wallahi babu wata idda da zan zauna yi kawai sai in auri Ibrahim ɗin, don na ƙosa fara gasawa Jidda baƙar aya mai tsakuwa a tafin hannunta yanzu ne za mu nuna mata dama mu asalin maƙiyanta ne ƴar daular da ta afka ciki ce ta aanya mu ka sassauta tuƙin gangancin ƙiyayyar da muke yi wa rayuwarta...

Umma jin batutuwan da Aliya take ba su da alamar ƙarewa ita kuma ta san ba a zo wajen wannan maganar ba domin an samu saɓanin abin da ita Aliyar take zato, cike da muryar mai ɗankaren sanyi ta ce

"Aliya aiki fa bai kammalu ba, don na je har ɗakin gawar Malam Kalla amma wallahi magani dai bai samu shiga hancinsa ba... Tun Aliya ba ta gama jin komai ba hawaye suka yi wa fuskarta tsinke ba komai ne ma ya ɓata mata rai ba sai yadda Umma ta samu damar da ta yi wasa da damarta don ta ce har ɗakin gawar ta je kuma dai ta san bokanya ta bata maganin da za ta barbaɗawa mutanen gidan su sume kenan idan har kowa ya suma sannan ta shiga ɗaki mai ta tsaya yi ba ta aiwatar da aikin ba?. Cike da muryar kuka mai nuna tsantsar takaici da baƙinciki ta ce

"Haba Umma da kin san ba za ki iya ba wallahi da ni na yi, ni fa É—azu Amatullahi ta kirani take ce min Malam Kalla ya mutu tsabar farincikin an samu sabuwar gawa ta namiji kuma a unguwar sai da na nuna jin daÉ—ina da har Amatullahin ta kusa harbo jirgina domin ban faÉ—a mata aikin da za ki yi a kan gawa ba kin san ba komai ne kake kwashewa ka faÉ—awa mutum ba duk da ta san komai"

Umma maganganun Aliya sun sosa ƙoƙon ranta haka ta fara magana cike da masifa ta ce

"Aliya ni za ki cewa ba zan iya ba, ai da kin zo ke kin je kin zuba, da kin san irin rijiya da bayan da na tsallake wallahi da baki yi wannan furucin ba, ni da gawa ta riƙe min hannu da ƙafa muka ringa rigima da gawa" Ƙirjin Aliya ta dafe da hannu ɗaya tana zare ido a take ta ji tsoro ya baibaye ta ta ce

"Umma dama bai mutu ba ne? Mun shiga uku Umma kar dai asirinki ya tonu?"

Umma ta ce

"Ai shi ya sa ake aso mutum ya fara jin ba,asi kafin ya yanke hukunci, to da asirina ya tonu ai da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, wallahi ban san mai ya sa wannan gawar ta mini haka fa ke ƙarshe da na matsa sai na gudu haka na janyo gawar nan ƙiiii wallahi har bakin ƙofar gidan Aliya, amma yadda kika san ana saka mini maganaɗisu ko kuma a saman iska haka aka ɗagamu daga ni har gawar aka mayar da mu" Umma ta faɗa tana kwashe komai ta faɗa mata.

Tsoro duk ya mamaye Aliya ga shi Kasim bai dawo daga masallaci da ta fita ba sai ta ji gidan gabaɗaya ya mata girma, amma saboda zuciya marar kyau da kuma mugun ƙuduri wannan abin da Umma ta faɗa bai zame musu aya ba sai ta ce

"Amma ai da sauran maganin ko Umma?" ,

Umma ta ja tsaki ta ce

"Sai ki yi kuma Aliya, an ce miki muna ta fafatawa da gawa guntun na ledar ya kife iska ta ɗaga ledar ma ni ba zan ce ga inda ledar take ba to ana ta kai wa yake ta kaya? Wallahi da a ce ke ce kika ganki riƙe a hannun gawa kuma gida babu kowa ta riƙe ki gamgam har da su shaƙe wuyan hijabi da tuni kin suma" Aliya ta yi shiru tana jin ɓacin rai tare da tunanin shin mai ya sa ba ta da sa,a a rayuwa mai ta sa duk aikin da aka bada a yi a kan abubuwan da za su saisaita rayuwar ta sai an samu akasin lissafi sai komai ya rushe, kenan ita haka za ta dawwama a talauci Jidda a daula, Umma ba ta ankara ba ta ji Aliya da ƙarfi ta ce

"Ba zai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuwa ba, akwai wanda yake saka mana hannu a aikin nan ina zargin Jidda ce in ba ita ba ya za a yi a ce duk abin da za a shirya a kanta ko kan mijinta abu ba ya yiwuwa in har ba saka hannunta ba ya za a yi a ce gawa ta yi motsi har ana kokawa wananna abin da sake kuma wallahi duk ranar da nufina ya cika sai ta wulaƙanta iya wulaƙanta a wajena" Ta faɗa tana rushewa da kukan baƙinciki.

Suna cikin wayar Abba da ya dawo saga masallaci ya yi sallama, da sauri ta ce

"To madalla Aliya ka gaishe da Kasim ɗin, to zai ji Abban naki ai ga shi nan ma ya shigo" Ta faɗa don ta ankarar da Aliya Abba ya dawo haka ta datse kiran tana ɗan wayincewa ta tattaro nutsuwarta amma gabanta yana faɗuwa game da Abba tana jiran ta ji kanun labarai shin Abban ya gano ta je gidan mutuwar ko kuwa kowa ma ya sani tun da ba ta san yadda aka ƙarƙe ba.

Ganin jikinsa sanyi ƙalau tun kafin ya ƙarasa zama ta ce

"Kai Allah sarki Malam Kalla lokaci ya yi!" Ta faÉ—a cike da jimantawa, ya gama zama ya ce
Chapter 96 · 0% Book details